Sunday, July 15, 2012

AN GABATAR DA TARON YAUMUTTKLIF A DA'IRAR KATSINA

An bayyana takalifi da cewa shi ne a sa ka yin abinda  baka son yi, a  kuma  hana ka yin abinda kake  son ka yi. Malam Yakubu Yahaya  wakilin ‘yanuwa  almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) na da’irar  Katisna da kewaye  ne  ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da jawabi ga kananan yara  maza da matan  da suka kai shekarun  wajabcin shari’a  a kansu, a bukin “yaumut  taklif” wanda  dandalin matasa na yankin  ya shirya aka gabatar da  shi a ranar Lahadi  19/ 8/1433  a markazin ‘yanuwan dake  garin Katsina.

A farkon jawabin sai da Malam  Yakubu  ya kawo ma yaran wasu abubuwa da yara suka fi fifitawa, inda ya tambaye su abin da yaro ya fi bukata tsakanin ranaikun karatu  da kuma na hutun makaranta, ranar barci  da tashi ayi salla cikin lokaci  dangane  da sallar Asubahi  da dai  sauran misalai  makamantan wadannan. Sai ya  kara bayanin cewa, shi  takalifi baya  nufin Allah ya  dankara ma mutum aiki ne,  sai dai  domin a lahira Allah za ya canja ma mutum din ne da abin da ya hanu  a duniya  da   abinda  yake a lahira.
Malam Yakubu  ya  bayyana  ma yaran cewa, ana fara addini  ne  tun mutum  yana  yaro,  ba sai an girma ba ne ake  fara yinsa, sai  ya ce, idan ka ga tsohon  banza, to babu shakka yaron banza ya  taso, haka ma abin yake  idan  ka ga tsohon kirki, to ya taso ne a yaron kirki, inda ya ba yaran misalin  Shehu  Usman dan Fodiyo muijaddadi (RA)  yadda ya taso da kirki tun yana yaro ya kuma yi  rayuwar  kirki, ga kuma Imam Khomaini(KS) shi ma haka ya taso, kana Sayyid Zakzaky(H) shi ma  haka rayuwarsa  take, sai ya karfafa  cewa, duk inda ka ga yaron kirki  to za ya zama tsohon kirki, haka ma idan kaga sabanin wannan.  Sai ya tambayi  yaran ko akwai wanda ya ke so ya yi irin  tsufan  su Malam Zakzay (H), inda duk cikar su  suka amsa da cewa, E!. Sai ya yi fatan Allah (T)  ya tabbatar da haka.
 Malam  Yakubu, ya jawo hankulan  yaran da cewa, idan aka kai shekaru  irin nasu, to ba a bukatar  yaro ya bata Sallarsa  idan yana yi,  ko kuma ya boye ya ci wani abu idan yana Azumi,  ya ce , wanda duk ya yi haka ,to ana binsa  bashi sai ya rama su, idan ma azumi ne sai ya kara da guda  sittin(kaffara)  sakamakon bata daya da ya yi. Sannan ya kiraye su da cewa, ba a bukatar su zama masu karya , cin amana, su kuma zamo masu biyayya ga iyayensu, su kuima  lizimci yin amfani da  abubuwan  da  suke  koyo a makarantu na addini da aikatawa tun daga wannan rana har zuwa mutuwa. Sannan ya bukaci malamai da iyaye da su kara kulawa da sallar yaran a makarantu  da kuma gidajensu  har ya zamo sun saba. Sannan aka gabatar da salla raka’a  biyu wadda  Malam Yakubun  ya jagoranta  domin  koya ma yaran yadda ake bukatar su rika gabatar da ita a duk  sa’adda lokacin ta ya  gabato.
Shi dai wannan  biki na ‘yaumut taklifi’ an  gabatar da shi ne da zimmar  zaburantar da yaran da shekarunsu  suka  kama  daga tara zuwa sama  ga ‘yan mata, su kuma maza daga goma sha  biyar .
Saidai  a wanna karo an lura da cewa,  wadanda suka halarci wannan taro akwai kananan yaran da shekarun  nasu basu kai wadanda  aka bukata ba, abinda ya jawu yin kira da cewa, wasu sai an sake dawowa da su a wasu shekaru masu zuwa nan gaba, kamar yadda Malam Yakubu ya bukata.  An dai kammala wannan biki karo na  farko cikin nasara.

AN GUDANAR DA BIKIN YAYE DALIBAN FUDIYA TA KATSINA A KARO NA GOMA

A ranar Assabat 25/8/1433 da ya zo daidai 14/ 7 2012, makarantar Fudiyya Nursery and Primary Katsina ta gabatar da bikin yaye dalibanta karo na goma na wannan shekara wanda aka gabatar a unguwar Filin Sanji Katsina.

A jawabin da ya gabatar babban bako kuma Daraktan makarantar, Malam Yakubu Yahaya ya bayyana cewa, hakuri shi ne maganin dukkan matsala, ya tabo tarihin fara karatu a wannan makaranta inda ya bayyana yadda mkarantar ta somo tun ana karantarwa a zaurukan jama’a da aka ara, kama-kama har zuwa wannan wuri bayan samun damar ginawa, ya kara da cewa, duk da matsalolin da aka fuskanta, an sami nasarar kutsamasu ne saboda hakuri da malamai suka yi,amma bangare iyayen yara sun kasa yinirin  wannan hakuri da wadannan matsaloli saboda kasa tsayuwa da nauyin da ya rataya ga wuyansu ta fuskar sauke nauyin makaranta, daga nan Malam Yakubu ya bukaci iayaen da su samar da wani asusu wanda za su rika amfani da kudin suna juya su domin bayar da tallafi ga malamai dama  makarantar.

A yunkurin samar da makarantar sakandare da hadin gwiwar kwamitin ahl-duthour da Lajnar Fudiyya suka fara, Malam Yakubu ya yi tuni garesu da su yi kokari su samar da koda karamar Sakandare(JSS) ta yadda idan Dairar ta sami dama sai ta samara da babbar sakandare(SSS), sanna ya ce, idan zai yiwu yaran da za su fita shekara mai zuwa su  fara  da ita, musamman idan aka yi la’akari da  tabarbarewar tarbiyya a makarantu. Sannan Malam Yakubu ya bayyana cewa,”muna da babban guri akan yaranmu, tunda a yanzu komai ya ruguje a wannan kasa kuma babu wani abu da yake ginuwa a yanzu sai wannan harka”. Sai ya yi kira ga kungiyar tsofaffin dalibai na fudiyyar(FOSA) da su yi kokari su shige ma yaran makarantar  gaba domin  kawo ma makarantar ci gaba”.

A tun farko da yake gabatar da jawabi, shugaban makarantar Fudiyya, Malam Kabir Sani, godiya ya nuna ga da’irar “yanuwa ta Katsina akan fadada makarantar da ta yi, sannan ya bayyana shirin da ake yi na fara karatu bangaren Islamiyya  wanda za a fara gabatar da shi bayan dawowa hutun sabuwarv shekarar karatun makaranta.

An dai kammala wannan biki da bayar da kyaututtuka ga wasu iyaye da suka yi fice wajen bayar da gudunmuwa ga makaranta a wannan shekara tare da nada sabbin shugabannin dalibai na wannan shekara.  

Sunday, July 8, 2012

AN GABATAR DA BIKIN YAUMUT TAKLIF A GARIN KATISANA

An bayyana takalifi da cewa shi ne a sa ka yin abinda baka son yi, a kuma hana ka yin abinda kake son ka yi. Malam Yakubu Yahaya wakilin ‘yanuwa almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) na da’irar Katisna da kewaye ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da jawabi ga kananan yara maza da matan da suka kai shekarun wajabcin shari’a a kansu, a bukin “yaumut taklif” wanda dandalin matasa na yankin ya shirya aka gabatar da shi a ranar Lahadi 19/ 8/1433 a markazin ‘yanuwan dake garin Katsina.
A farkon jawabin sai da Malam Yakubu ya kawo ma yaran wasu abubuwa da yara suka fi fifitawa, inda ya tambaye su abin da yaro ya fi bukata tsakanin ranaikun karatu da kuma na hutun makaranta, ranar barci da tashi ayi salla cikin lokaci dangane da sallar Asubahi da dai sauran misalai makamantan wadannan. Sai ya kara bayanin cewa, shi takalifi baya nufin Allah ya dankara ma mutum aiki ne, sai dai domin a lahira Allah za ya canja ma mutum din ne da abin da ya hanu a duniya da abinda yake a lahira.
Malam Yakubu ya bayyana ma yaran cewa, ana fara addini ne tun mutum yana yaro, ba sai an girma ba ne ake fara yinsa, sai ya ce, idan ka ga tsohon banza, to babu shakka yaron banza ya taso, haka ma abin yake idan ka ga tsohon kirki, to ya taso ne a yaron kirki, inda ya ba yaran misalin Shehu Usman dan Fodiyo muijaddadi (RA) yadda ya taso da kirki tun yana yaro ya kuma yi rayuwar kirki, ga kuma Imam Khomaini(KS) shi ma haka ya taso, kana Sayyid Zakzaky(H) shi ma haka rayuwarsa take, sai ya karfafa cewa, duk inda ka ga yaron kirki to za ya zama tsohon kirki, haka ma idan kaga sabanin wannan. Sai ya tambayi yaran ko akwai wanda ya ke so ya yi irin tsufan su Malam Zakzay (H), inda duk cikar su suka amsa da cewa, E!. Sai ya yi fatan Allah (T) ya tabbatar da haka.
Malam Yakubu, ya jawo hankulan yaran da cewa, idan aka kai shekaru irin nasu, to ba a bukatar yaro ya bata Sallarsa idan yana yi, ko kuma ya boye ya ci wani abu idan yana Azumi, ya ce , wanda duk ya yi haka ,to ana binsa bashi sai ya rama su, idan ma azumi ne sai ya kara da guda sittin(kaffara) sakamakon bata daya da ya yi. Sannan ya kiraye su da cewa, ba a bukatar su zama masu karya , cin amana, su kuma zamo masu biyayya ga iyayensu, su kuima lizimci yin amfani da abubuwan da suke koyo a makarantu na addini da aikatawa tun daga wannan rana har zuwa mutuwa. Sannan ya bukaci malamai da iyaye da su kara kulawa da sallar yaran a makarantu da kuma gidajensu har ya zamo sun saba. Sannan aka gabatar da salla raka’a biyu wadda Malam Yakubun ya jagoranta domin koya ma yaran yadda ake bukatar su rika gabatar da ita a duk sa’adda lokacin ta ya gabato.
Shi dai wannan biki na ‘yaumut taklifi’ an gabatar da shi ne da zimmar zaburantar da yaran da shekarunsu suka kama daga tara zuwa sama ga ‘yan mata, su kuma maza daga goma sha biyar .
Saidai a wanna karo an lura da cewa, wadanda suka halarci wannan taro akwai kananan yaran da shekarun nasu basu kai wadanda aka bukata ba, abinda ya jawu yin kira da cewa, wasu sai an sake dawowa da su a wasu shekaru masu zuwa nan gaba, kamar yadda Malam Yakubu ya bukata. An dai kammala wannan biki karo na farko cikin nasara.

Sunday, June 10, 2012

ACADAMIC FORUM YANKIN KATSINA YA GABATAR DA TARON MAKON IMAM KHUMEINE(KS) NA WANNAN SHEKARA TA 2012

Aranar Lahadi 10/ 6/ 2012 , dandalin dalibai na Acadamic Forum yankin Katsina ya gabatar da taron tunawa da makon Imam khomene (KS) na wannan shekara a dakin taro na ‘women centre’ dake unguwar  filin samji Katsina.

A jawabin da ya gabatar, Shekh Muhammad Mahmud Turi, wakilin Sayyid  Ibrahim Yakubu Zakzaky(H) a birnin Kano , ya karanto kadan daga tarihin Marigayi Imam Khumene(KS). Malam Turi ya bayyayana cewa, Imam ya  taso ne a gidan Ilimi, amma a yanayi na maraici domin mahaifansa sun rasu tun yana karami,amma a haka ya yi  ta rayuwa irin ta neman ilimi ya kuma rayu a cikin yanayi  karancin abin hannu domin an tabbatar da cewa, a lokacin bargo daya ne kadai ya mallaka, amma a haka ya ci gaba da neman ilimin.Malamin ya  ce, tun yana da kananaan shekaru ya fara koyarwa a Hauza saboda hazaka da Allah (T) ya  ba shi.Malam Turi ya kara bayyana cewa, Allah madaukakin Sarki ya haska ma  Imam halin da al’ummar iran ta ke ciki na rashin bin dokokin Allah, bayan da Imam ya fara wayar ma al’umma da kai sai gwamnatin Sha, ta yi yunkurin kashe shi, abinda ya sa Malamai suka bayyana Imam khomene a matsayin Ayatul lahi, hakan yasa dole Sarki Sha ya janye yunkurin kasha shi, sai dai gwamnatin ta kore shi daga Iran ,inda ya yi hijira zuwa kasar turkiya sannan daga can zuwa kasar iraki, inda a can din ma dai ya ci gaba da wayar ma al’umma kai musamman abin da ya shafi Fikira akan ‘Wilayatul fakihi’ watau jagorancin Malami, wannan kira na imam ya jawo masa kyama daga Malamai.
malam Turi ya kara da cewa, duk lokacin da Musulmi suka yi watsi da tsarin Allah, to rayuwarsu zata kasance a cikin kaskanci, kamar abinda yake faruwa a wannan kasa a halin yanzu. Ya ce, Imam ya ci gaba da kokarin wayar ma mutane kai akan  hadarin bin tsarin gwamnatin da bata musulunci ba domin rashinta gwamnatin musulunci na hana aikatuwar musuluncin. Malam Turi ya kara da cewa, Imam ya yi gwagwarmaya da malamai fiye da yadda ya yi da Kafirai, domoin Malaman suna zarginsa da kawo cikas wajen bayyanar Imam Mahadi(AJ)
Malam Turi ya bayyana wasu darussa da za a dauka a rayuwar wannan bawan Allah inda malamin ya yi tambayar cewa, Mi yasa Imam ya sami wannan nasara , amma ga dimbin Malamai basu sami wannan ba? Sai ya bada amsar cewa, Imam ya na da zuciya daya,sai ya ba Allah(T) wannan zuciya sai Alah ya hore masa zukatan al’umma.  

Malam Turi ya kirayi ‘yanuwa akan yaki da zukata  domin kauce ma abubuwan da za su bata zuciya saboda shagaltar da ita tare da  gurbata ta yadda ba zata iya yunkurin gwagwarmayar  tabbatar da addini ba.
A lokacin da yake kira akan kulawa da tarbiyyar ‘ya’ya, Malam Turi ya bayyana cewa, gurin makiyanmu shi ne  su bata tarbiyyar  musulmi, sai ya bayyana muhimmancin kulawa da  tarbiyyar yara domin su kasance sun sami tarbiyyar addini domin su zamo cikin rundunar da zata zamo ta Allah. Da zata taimakama addini.
A wani bangaren jawabin nasa, ya bayyana cewa, duk jama’ar da tadanfaru da Imam Khomenei, za a ga bambanci da sauran  koda kuwa Shi’a mutum ya ke yi.Ya bada misalin wasu kasahe irin su Pakistan da suke da Shi’a, amma saboda basu damfare da Imam basu sami daukaka ba, amma ga Hizbullahi nan yadda suka buwaya.
A karshe ya bayyana cewa, a wannan kasa babu mafita ga al’umma sai ta hannun Mujaddadin wannan al’umma  Sayyid Zakzaky(H) kamar yadda shehu Usman dan Fodiyo ya  yi bushara.’abinda ya kamace mu shi ne riko da wannan gwagwarmaya ta hanyar kyautata alaka da Allah kamar yadda Sayyid Zakzaky(H) ya ke kira akai’

Saturday, June 2, 2012

DANDALIN MATASA NA HARKAR MUSULUNCI A NIJERIYA YANKIN KATSINA YA GABATAR DA MAULUDIN FATIMA(AS) A GARIN KANKIA, JIHAR KATSINA

Zama matashi mai addini babban matsayi  ne, kuma falala ce daga Allah(T). Malam Yakubu Yahaya ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da jawabin mauludin Syyida Azzahara(AS) da dandalin matasan harkar musulunci karkashin jagorancin Sayyid  Zakzaky(H) na yankin da’irar Katsina da kewaye ya shirya ya kuma  gabatar a dakin taro  na ‘Shema youth empowerment  Centre’ dake garin Kankia, jihar Katsina, a ranar Lahadi  7 /7/1433.

Malam Yakubu  ya ci gaba da cewa, duniya gaba dayanta, a wannan lokaci matasa ne suke tafiyar da ita, ina ya bada misali da manyan kasashen  duniya  dama wannan kasa da cewa,shugabanninsu duk matasa ne, haka idan aka dubi rundunonin soji  da sauran jami’an  tsaro na duniya, duk za a ga dai matasa ne  suke jagorantar su, ya ce, duk wasu bangarorin tafiyar da al’amurran al’umma dai zaka ga cewa,matasane ke rike da su. Ya ce, hakama  lamarin Lahira ta matasance,inda  ya bayyana Imam Hasan da Husaini (AS) a matsayin shugabannin aljanna. ya kuma karanto kissar Annabawan Allah da suka hada da Annabi Ibrahim da sauransu da irin gwagwarmayarsu da zalunci duk suna matsayin matsa ne suka aiwsatar da haka. Sannan  idan aka dubi ashabul  Kahfi  suma matasanne,ya ce, wadanda suka rufa ma Manzo baya a lokacin kiransa irinsu Imam Ali ,Sayyida Zahara(AS)  da sauran su  ,za a ga cewa dai matasan ne.ya kara da cewa, haka ma Mujaddadai  irinsu Shehu dan Fodiyu Da Imam Khomenei (KS) duk matasa ne suka dafa masu sai ya ce duk wannan yana nuna maka cewa,matasa sune  jari na duniya da Lahira, kuma akan yarinta ake gina duniya da Lahira,ya kara bayyana cewa, “ba girman jiki bane , zuciya ce mai kyau da ta  siffantu da ibada.” sai  ya ankarar da matasa akan yunkurin da makiya suke yi na  rosa tarbiyyarsusannan ya   nuna wajabcin lura tare  da kauce ma afkawa cikin hadartin wannan tarko. Sai ya bayyana mafita daga wannan tarko da cewa, itace addini ,”a dasa ma matashi tsoron Allah, ibada da son  Lahira tare da tsaron azabarta ,”kuma wannan shi ne manufar kiran Sayyid  Zakzaky(H) ,  ba  al’amarin neman mukamin duniya ba ne”,
Ta bangaren Sayyida Zahara(AS) kuwa, Malam Yakubu ya tabo wasu kadan daga matsayai  da falalolin da Allah ya bata Musamman Tsayuwarta dadagewarta akan bin Allah da taimaka ma sakon da aka aiko Manzo  Da shi,sannan ya bayyana  cewa, al’amarin ahlul Bayt abu ne  mai hatsari domin kuwa abu ne wanda ya shafi Imani.Ya kara da cewa,zaka ga mutum ya yi imani da sakon Manzo a dunkule , amma  da an ce ayi dalla-dalla sai ka ga yana shafa keya bai yarda ba. Ya tabo abubuwa da dama  da suka shafi  hakkkin ahlul Bayt da suka hada da Khumusi,Wila’a  da jagorancin su  kamar maganar  ‘ Halifofi bayana Sha biyu ne” kamar  yadda yake a littafan Buhari da MUsulimu, amma dai mutane  ba su yarda ba, inda zaka ga babban Malami idan aka yi masa wannan bayani baya yarda, haka kuma yake ga sauran musulmin duniya. Sai ya yi mamakin yadda kiriri aka maida Halifofin Annabi  guda Hudu, bayan shi Annabin ya ce Sha biyu ne kamar yadda ya zo a Buhari da Muslim,  ya ce “lallai akwai hadari akan wannan” ya kammala da cewa, ” Ba so bane kawai, a‘a  bi ne ga wadannan  bayin Allah” 

Tuesday, May 15, 2012

MUZAHARAR MAULUDIN SAYYIDA FATIMA AZZAHARA (AS) A KATSINA

‘yayanuwa mata almajiran Sayyid Ibarahim Zakzaky(H) dake  da’irar  Katsina, sun shirya  tare da gabatar da  muzaharar  mauludin Sayyida  Fatima azzhara diyar Manzon Allah (S) ta wannan shekara a wannan rana ta Talata,24/6/  1433 
.
Muzaharar  wadda  aka soma da misalin karfe tara da rabi na safiyar  wannan  rana , ta sami halartar ‘yanuwa  mata  daga yankuna  daban-daban na cikin garin Katsina  da kewaye, a  bisa      rakiyar Harisawa  da  suke a goshin wannan muzahara , sannan ‘yan makarantun Islamiyyu na ciki da wajen garin  Katsina da suke dauke da tutoci iri daban-daban  ana tafe mawakan Harkar musulunci na rero baitocin  yabo ga Sayyida Fatima(AS)  dama wakokin mahaifin ta da sauran “ya’yanta  A’immatul huda(AS).
Muzaharar  wadda  ta zagaye  muhimman  titunan garin Katsina, ta kayatar ainun ida aka kwatanta ta da wadanda suka gabace ta, duk da karacin abubuwa kamar yadda daya daga cikin masu shirya ta  ta shaida ma  manema  labarai da suka zanta da ita. Malam Bilkisu idris  ta ce, “akwai shirye-shirye da  za a gabatar idan Allah ya nuna mana ta shekara mai zuwa, wanda ta ce, za su fadada shirin domin gayyato mata daga bangarori da yawa na cikin garin Katsina.
A jawabin da ta gabatar bayan kammala wannan muzahar, Malama Safiya Kabir, ta bayyana  wasu kadan daga cikin matsayai  na wannan  baiwar Allah da cewa, ita  ce wadda Allah da kansa ya daura mata aure da babban bawansa Imam Ali (AS), sannan ta bayyana takaicin irin wahalhalu da wannan baiwar Allah ta hadu da su tun bayan wafatin mahaifinta  Annabi  Muhammad (S).Ta ce, a yunkurin rufe matsayi  da darajarta  ne,  ba za ka taba jin ana karanto wasu Hadisai da za a danganta ruwayarsu daga wajen ta ba, domin  kada jama’a  su fahinci wasicin da Annabi ya yi  na bain  shiriya a hannun jikokinta, sai tayi  fatan al’umma  musamman ‘yanuwa  mata  za su yi bita akan rayuwarta su kuma yi koyi da halaye irin na Fadima(AS).
Kafin wannan muzahar, sai da kwamitin ‘yanuwan mata ya gabatar da wata ziyara zuwa ga malaman makarantun  allo dake yankuna  hudu na bangarorin da ake da su  a wannan  da’ira  da suka hada da yankunan  Gabas, Yamma, Kudu da kuma Arewa  wtau  (Zones) tare da gabatar ma almajirai da malamansu  kyaututtuka  na  abinci  da kuma sabulan wanki albarkacin wannan baiwar Allah .
Za dai aci gaba da gabatr da wannan gagarumin biki na tuna haifuwar diyar Manzon Allah Fatima azzhara (AS)  a rana daya da ta rage  inda Malam Yakubu Yahaya zaya gabatar da jawabin karshe na wannan biki.