‘yayanuwa mata almajiran Sayyid Ibarahim Zakzaky(H) dake da’irar Katsina, sun shirya tare da gabatar da muzaharar
mauludin Sayyida Fatima azzhara
diyar Manzon Allah (S) ta wannan shekara a wannan rana ta Talata,24/6/ 1433
.
Muzaharar wadda aka soma da misalin karfe tara da rabi na
safiyar wannan rana , ta sami halartar ‘yanuwa mata
daga yankuna daban-daban na cikin
garin Katsina da kewaye, a bisa rakiyar Harisawa da suke
a goshin wannan muzahara , sannan ‘yan makarantun Islamiyyu na ciki da wajen
garin Katsina da suke dauke da tutoci
iri daban-daban ana tafe mawakan Harkar
musulunci na rero baitocin yabo ga
Sayyida Fatima(AS) dama wakokin mahaifin
ta da sauran “ya’yanta A’immatul
huda(AS).
Muzaharar wadda ta zagaye muhimman titunan garin Katsina, ta kayatar ainun ida
aka kwatanta ta da wadanda suka gabace ta, duk da karacin abubuwa kamar yadda
daya daga cikin masu shirya ta ta shaida
ma manema labarai da suka zanta da ita. Malam Bilkisu
idris ta ce, “akwai shirye-shirye da za a gabatar idan Allah ya nuna mana ta shekara
mai zuwa, wanda ta ce, za su fadada shirin domin gayyato mata daga bangarori da
yawa na cikin garin Katsina.
A jawabin da ta gabatar bayan kammala wannan muzahar, Malama
Safiya Kabir, ta bayyana wasu kadan daga
cikin matsayai na wannan baiwar Allah da cewa, ita ce wadda Allah da kansa ya daura mata aure da
babban bawansa Imam Ali (AS), sannan ta bayyana takaicin irin wahalhalu da
wannan baiwar Allah ta hadu da su tun bayan wafatin mahaifinta Annabi Muhammad (S).Ta ce, a yunkurin rufe matsayi da darajarta ne, ba
za ka taba jin ana karanto wasu Hadisai da za a danganta ruwayarsu daga wajen
ta ba, domin kada jama’a su fahinci wasicin da Annabi ya yi na bain shiriya a hannun jikokinta, sai tayi fatan al’umma musamman ‘yanuwa mata za
su yi bita akan rayuwarta su kuma yi koyi da halaye irin na Fadima(AS).
Kafin wannan muzahar, sai da kwamitin ‘yanuwan mata ya
gabatar da wata ziyara zuwa ga malaman makarantun allo dake yankuna hudu na bangarorin da ake da su a wannan da’ira da
suka hada da yankunan Gabas, Yamma, Kudu
da kuma Arewa wtau (Zones) tare da gabatar ma almajirai da
malamansu kyaututtuka na abinci da
kuma sabulan wanki albarkacin wannan baiwar Allah .
Za dai aci gaba da gabatr da wannan gagarumin biki na tuna
haifuwar diyar Manzon Allah Fatima azzhara (AS)
a rana daya da ta rage inda Malam
Yakubu Yahaya zaya gabatar da jawabin karshe na wannan biki.
No comments:
Post a Comment