Thursday, April 2, 2015

AN FARA GABATAR DA MAULUDIN SAYYIDA ZAHARA (SA) A KATSINA

A jiya Laraba ne kwamitin 'yan'uwa mata na Da'irar Katsina da kewaye ya fara tgabatar da mauludin Sayyida Zahara Diyar Manzon Allah (s)na wannan shekara ta 1436.An fara gabatar da jawabi ne a Unguwar Kofar Bai Kusa da Korau Cinima da ke cikinbirnin Katsina, haka kuma a yau da dare ne za a gabatar da jawabin mauludin a Unguwar Rafin Dadi a bakin Asibitin Malam Barau.wanda Malam Abubakar Nuhu Talata Mafara zai gabatar.

No comments:

Post a Comment