Aranar Lahadi 10/ 6/ 2012 , dandalin
dalibai na Acadamic Forum yankin Katsina ya gabatar da taron tunawa da makon
Imam khomene (KS) na wannan shekara a dakin taro na ‘women centre’ dake
unguwar filin samji Katsina.
A jawabin da ya gabatar, Shekh
Muhammad Mahmud Turi, wakilin Sayyid Ibrahim Yakubu Zakzaky(H) a birnin
Kano , ya karanto kadan daga tarihin Marigayi Imam Khumene(KS). Malam Turi ya
bayyayana cewa, Imam ya taso ne a gidan Ilimi, amma a yanayi na maraici domin
mahaifansa sun rasu tun yana karami,amma a haka ya yi ta rayuwa irin ta
neman ilimi ya kuma rayu a cikin yanayi karancin abin hannu domin an
tabbatar da cewa, a lokacin bargo daya ne kadai ya mallaka, amma a haka ya ci
gaba da neman ilimin.Malamin ya ce, tun yana da kananaan shekaru ya fara
koyarwa a Hauza saboda hazaka da Allah (T) ya ba shi.Malam Turi ya kara
bayyana cewa, Allah madaukakin Sarki ya haska ma Imam halin da al’ummar
iran ta ke ciki na rashin bin dokokin Allah, bayan da Imam ya fara wayar ma
al’umma da kai sai gwamnatin Sha, ta yi yunkurin kashe shi, abinda ya sa
Malamai suka bayyana Imam khomene a matsayin Ayatul lahi, hakan yasa dole Sarki
Sha ya janye yunkurin kasha shi, sai dai gwamnatin ta kore shi daga Iran ,inda
ya yi hijira zuwa kasar turkiya sannan daga can zuwa kasar iraki, inda a can
din ma dai ya ci gaba da wayar ma al’umma kai musamman abin da ya shafi Fikira
akan ‘Wilayatul fakihi’ watau jagorancin Malami, wannan kira na imam ya jawo
masa kyama daga Malamai.
malam Turi ya kara da cewa, duk
lokacin da Musulmi suka yi watsi da tsarin Allah, to rayuwarsu zata kasance a
cikin kaskanci, kamar abinda yake faruwa a wannan kasa a halin yanzu. Ya ce,
Imam ya ci gaba da kokarin wayar ma mutane kai akan hadarin bin tsarin gwamnatin
da bata musulunci ba domin rashinta gwamnatin musulunci na hana aikatuwar
musuluncin. Malam Turi ya kara da cewa, Imam ya yi gwagwarmaya da malamai fiye
da yadda ya yi da Kafirai, domoin Malaman suna zarginsa da kawo cikas wajen
bayyanar Imam Mahadi(AJ)
Malam Turi ya bayyana wasu darussa
da za a dauka a rayuwar wannan bawan Allah inda malamin ya yi tambayar cewa, Mi
yasa Imam ya sami wannan nasara , amma ga dimbin Malamai basu sami wannan ba?
Sai ya bada amsar cewa, Imam ya na da zuciya daya,sai ya ba Allah(T) wannan
zuciya sai Alah ya hore masa zukatan al’umma.
Malam Turi ya kirayi ‘yanuwa akan
yaki da zukata domin kauce ma abubuwan da za su bata zuciya saboda
shagaltar da ita tare da gurbata ta yadda ba zata iya yunkurin
gwagwarmayar tabbatar da addini ba.
A lokacin da yake kira akan kulawa
da tarbiyyar ‘ya’ya, Malam Turi ya bayyana cewa, gurin makiyanmu shi ne
su bata tarbiyyar musulmi, sai ya bayyana muhimmancin kulawa da
tarbiyyar yara domin su kasance sun sami tarbiyyar addini domin su zamo cikin
rundunar da zata zamo ta Allah. Da zata taimakama addini.
A wani bangaren jawabin nasa, ya
bayyana cewa, duk jama’ar da tadanfaru da Imam Khomenei, za a ga bambanci da
sauran koda kuwa Shi’a mutum ya ke yi.Ya bada misalin wasu kasahe irin su
Pakistan da suke da Shi’a, amma saboda basu damfare da Imam basu sami daukaka
ba, amma ga Hizbullahi nan yadda suka buwaya.
A karshe ya bayyana cewa, a wannan
kasa babu mafita ga al’umma sai ta hannun Mujaddadin wannan al’umma
Sayyid Zakzaky(H) kamar yadda shehu Usman dan Fodiyo ya yi
bushara.’abinda ya kamace mu shi ne riko da wannan gwagwarmaya ta hanyar
kyautata alaka da Allah kamar yadda Sayyid Zakzaky(H) ya ke kira akai’
No comments:
Post a Comment