Sunday, July 15, 2012

AN GUDANAR DA BIKIN YAYE DALIBAN FUDIYA TA KATSINA A KARO NA GOMA


A ranar Assabat 25/8/1433 da ya zo daidai 14/ 7 2012, makarantar Fudiyya Nursery and Primary Katsina ta gabatar da bikin yaye dalibanta karo na goma na wannan shekara wanda aka gabatar a unguwar Filin Sanji Katsina.

A jawabin da ya gabatar babban bako kuma Daraktan makarantar, Malam Yakubu Yahaya ya bayyana cewa, hakuri shi ne maganin dukkan matsala, ya tabo tarihin fara karatu a wannan makaranta inda ya bayyana yadda mkarantar ta somo tun ana karantarwa a zaurukan jama’a da aka ara, kama-kama har zuwa wannan wuri bayan samun damar ginawa, ya kara da cewa, duk da matsalolin da aka fuskanta, an sami nasarar kutsamasu ne saboda hakuri da malamai suka yi,amma bangare iyayen yara sun kasa yinirin  wannan hakuri da wadannan matsaloli saboda kasa tsayuwa da nauyin da ya rataya ga wuyansu ta fuskar sauke nauyin makaranta, daga nan Malam Yakubu ya bukaci iayaen da su samar da wani asusu wanda za su rika amfani da kudin suna juya su domin bayar da tallafi ga malamai dama  makarantar.

A yunkurin samar da makarantar sakandare da hadin gwiwar kwamitin ahl-duthour da Lajnar Fudiyya suka fara, Malam Yakubu ya yi tuni garesu da su yi kokari su samar da koda karamar Sakandare(JSS) ta yadda idan Dairar ta sami dama sai ta samara da babbar sakandare(SSS), sanna ya ce, idan zai yiwu yaran da za su fita shekara mai zuwa su  fara  da ita, musamman idan aka yi la’akari da  tabarbarewar tarbiyya a makarantu. Sannan Malam Yakubu ya bayyana cewa,”muna da babban guri akan yaranmu, tunda a yanzu komai ya ruguje a wannan kasa kuma babu wani abu da yake ginuwa a yanzu sai wannan harka”. Sai ya yi kira ga kungiyar tsofaffin dalibai na fudiyyar(FOSA) da su yi kokari su shige ma yaran makarantar  gaba domin  kawo ma makarantar ci gaba”.

A tun farko da yake gabatar da jawabi, shugaban makarantar Fudiyya, Malam Kabir Sani, godiya ya nuna ga da’irar “yanuwa ta Katsina akan fadada makarantar da ta yi, sannan ya bayyana shirin da ake yi na fara karatu bangaren Islamiyya  wanda za a fara gabatar da shi bayan dawowa hutun sabuwarv shekarar karatun makaranta.

An dai kammala wannan biki da bayar da kyaututtuka ga wasu iyaye da suka yi fice wajen bayar da gudunmuwa ga makaranta a wannan shekara tare da nada sabbin shugabannin dalibai na wannan shekara.  


No comments:

Post a Comment