Sunday, July 15, 2012

AN GABATAR DA TARON YAUMUTTKLIF A DA'IRAR KATSINA


An bayyana takalifi da cewa shi ne a sa ka yin abinda  baka son yi, a  kuma  hana ka yin abinda kake  son ka yi. Malam Yakubu Yahaya  wakilin ‘yanuwa  almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) na da’irar  Katisna da kewaye  ne  ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da jawabi ga kananan yara  maza da matan  da suka kai shekarun  wajabcin shari’a  a kansu, a bukin “yaumut  taklif” wanda  dandalin matasa na yankin  ya shirya aka gabatar da  shi a ranar Lahadi  19/ 8/1433  a markazin ‘yanuwan dake  garin Katsina.

A farkon jawabin sai da Malam  Yakubu  ya kawo ma yaran wasu abubuwa da yara suka fi fifitawa, inda ya tambaye su abin da yaro ya fi bukata tsakanin ranaikun karatu  da kuma na hutun makaranta, ranar barci  da tashi ayi salla cikin lokaci  dangane  da sallar Asubahi  da dai  sauran misalai  makamantan wadannan. Sai ya  kara bayanin cewa, shi  takalifi baya  nufin Allah ya  dankara ma mutum aiki ne,  sai dai  domin a lahira Allah za ya canja ma mutum din ne da abin da ya hanu  a duniya  da   abinda  yake a lahira.
Malam Yakubu  ya  bayyana  ma yaran cewa, ana fara addini  ne  tun mutum  yana  yaro,  ba sai an girma ba ne ake  fara yinsa, sai  ya ce, idan ka ga tsohon  banza, to babu shakka yaron banza ya  taso, haka ma abin yake  idan  ka ga tsohon kirki, to ya taso ne a yaron kirki, inda ya ba yaran misalin  Shehu  Usman dan Fodiyo muijaddadi (RA)  yadda ya taso da kirki tun yana yaro ya kuma yi  rayuwar  kirki, ga kuma Imam Khomaini(KS) shi ma haka ya taso, kana Sayyid Zakzaky(H) shi ma  haka rayuwarsa  take, sai ya karfafa  cewa, duk inda ka ga yaron kirki  to za ya zama tsohon kirki, haka ma idan kaga sabanin wannan.  Sai ya tambayi  yaran ko akwai wanda ya ke so ya yi irin  tsufan  su Malam Zakzay (H), inda duk cikar su  suka amsa da cewa, E!. Sai ya yi fatan Allah (T)  ya tabbatar da haka.
 Malam  Yakubu, ya jawo hankulan  yaran da cewa, idan aka kai shekaru  irin nasu, to ba a bukatar  yaro ya bata Sallarsa  idan yana yi,  ko kuma ya boye ya ci wani abu idan yana Azumi,  ya ce , wanda duk ya yi haka ,to ana binsa  bashi sai ya rama su, idan ma azumi ne sai ya kara da guda  sittin(kaffara)  sakamakon bata daya da ya yi. Sannan ya kiraye su da cewa, ba a bukatar su zama masu karya , cin amana, su kuma zamo masu biyayya ga iyayensu, su kuima  lizimci yin amfani da  abubuwan  da  suke  koyo a makarantu na addini da aikatawa tun daga wannan rana har zuwa mutuwa. Sannan ya bukaci malamai da iyaye da su kara kulawa da sallar yaran a makarantu  da kuma gidajensu  har ya zamo sun saba. Sannan aka gabatar da salla raka’a  biyu wadda  Malam Yakubun  ya jagoranta  domin  koya ma yaran yadda ake bukatar su rika gabatar da ita a duk  sa’adda lokacin ta ya  gabato.
Shi dai wannan  biki na ‘yaumut taklifi’ an  gabatar da shi ne da zimmar  zaburantar da yaran da shekarunsu  suka  kama  daga tara zuwa sama  ga ‘yan mata, su kuma maza daga goma sha  biyar .
Saidai  a wanna karo an lura da cewa,  wadanda suka halarci wannan taro akwai kananan yaran da shekarun  nasu basu kai wadanda  aka bukata ba, abinda ya jawu yin kira da cewa, wasu sai an sake dawowa da su a wasu shekaru masu zuwa nan gaba, kamar yadda Malam Yakubu ya bukata.  An dai kammala wannan biki karo na  farko cikin nasara.


No comments:

Post a Comment