Friday, April 17, 2015

KAMMALA MAULUDIN DIYAR MANZON ALLAH(S) A KATSINA



 A jiya Alhamis ne aka kawo karshen tarurrukan mauludin Fatima(AS) da 'yan'uwa mata  na Da'irar Katsina da kewaye suka shirya.

Malam Yakubu Yahaya ne ya rufe wannan biki da karanto wani yanki da Hudubar Sayyida da ta yi a gaban Halifar musulmi Abubakar bayan hana ta hakkinta da aka yi  bayan wafatin Manzon Allah(S).
 Ba muna jin dadin karanto abubuwan da suka faru bayan wafatin Manzon ba ne, sai dai muna karantawa don mu san inda gaskiya ta ke , mu yi riko da ita ,mu kuma ji inda karya ta ke, mu bar ma masu karyar  abinsu.Malam Yakubu a wajen karatun Kammala Mauludin Fatima da ‘yan’uwa mata suka shirya a katsina
A karshe Malam Yakubu ya yi fatan Allah ya karba mana ya tabbatar da mu bisa shiriya, ya kuma nuna mana na wsu shekaru masu zuwa. Ya kuma yi fatan Allah ya saka ma kowa da alheri musamman wadanda suka shirya  da kuma wadanda suka taimaka har abin ya yiwu.

No comments:

Post a Comment