Monday, November 26, 2012

AN GABATAR DA KARATUN IDUL GHADIR NA KWANA UKU A KATSINA

 Kimanin kwana ukku aka kwashe ana gabatar da tarurrukan tunawa da munasabar  Idil Ghadir, domin tuna ma al’ummar musulmi wasiyyar da Manzon rahama ya yi a hajjin bankwana ,a ranar 18 ga watan zulhijja  bayan da ya kammala aikin  hajji  zaya koma Madina, taron da Da’irar ‘yanuwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky(H) ta Katsina ta shirya tare da gabatar da shi tun daga ranar Talata 21 har zuwa Alhamis 23 ga zulhajjin wannan shekara ta 1433.

A wannan taro Malam Yakubu Yahaya ya gabatar da karanto falalolin Iyalan gidan Manzon  Allah Musamman Imam Ali(AS) domin al’umma ta fahimci irin matsayinsa da jarumtakarsa hada da ilimin da Allah ya bashi domin dai ya zamo Halifar Manzon Allah bayan wafatinsa. Haka kuma a wannan biki, malam Yakubu ya karanto doguwar hudubar da Annabin rahama ya karanta a wancan lokaci.
Bayan kammala karance-karancen ne, malam yakubu ya ankarar da al’umma cewa, wannan al’amarin da ya faru na bijire ma wasicin Annabi da wasu suka yi, ba ana karantawa ba ne domin ana kiyayya da wasu kamar yadda wasu suke gani, a’a saidai ana karantawa ne domin al’umma ta san hakikanin sakon da wadanda aka ce abi bayan wafatin Manzon.
A jawabin nasa ya yi nuni da yadda sakamakon bijire ma wasicin aka kirkiro abubuwa na addini wadanda ba Manzon Allah ne ba  ya yi umurni da yinsu , inda ya bada misalin kiran salla biyu da ake yi a ranar Juma’a, abinda ya ce  mai Risala ya bayyana da cewa, banu Umayya ne suka kirkiro shi, haka kuma a kokarin rufe matsayi na Imama Ali(A) sannan ya ce, kimanin kashi saba’in da biyar  cikin dari na addini da ake yi  duk an kirkiro su ne bayan wafatin Manzon Allah duk dai domin ganin an kauce ma wasicin  bin Imam Ali (AS) , ya kara da cewa, akan haka ne ma Mu’awiyya ya tara malamai suka yi ta kirkiro Hadisan falalar wasu Sahabbai don rufe matsayuin Iayalan Annabi, wannan ya sa aka kwashe shekaru ana zagin Imam Ali(AS)  da Iyayensa , matarsa , ‘ya’yansa dama duk wanda ke binsa, Malam Yakubu ya ce, bayan zagin imam din wasu ma sun kara da yin izgili, inda halifa Mutawakkil yake yin shiga irin ta Imam Ali ya  fito fada , yadda da an gan shi sai ayi ta keta dariya waidai domin nuna izgili. Ya ce, Mutanen da Allah ya yi  Umurnin a girmama, sune aka  koma ana zagi da yi masu izgili.
Malam Yakbu ya bayyana cewa,akwai bukatar al’umma ta fahinci abinda muke cewa tunda addini muke yi, kuma shi ne zamu yi sannan mu tsira, kuma gaskiya tana nan sannan dole wannan gaskiya ce zamu yi. Sai ya tabbatar da cewa, tabbas an jaraba Sahabbai akan wannan lamari, wasu sun ci jarabawar wasu kuma  sun fadi kamar yadda aka jaraba wasu al’ummu suka fadi.sannan ya tabbatar da cewa, “ duk fa wanda ya gitta ma Manzon Allah. To fa zamu gitta masa kowanene, iyakar gaskiyar wannan Magana kenan, amma ba muna gaba da wani sahabi bane, basu  yi mana laifin komai ba, kuma basu bamu haushi  kuma Allah ya ba su, sun ga Manzon Allah, sun bi shi Sallah sun kuma yi jihadi  tare da shi ,amma daga baya wasu sun fadi jarabawa, wasu kuma sun ci. saboda haka wadanda suka ci jarabawa muna tare da su dari bisa  dari, wadanda suka fadi kuma al’amarinsu yana wurin Allah, amma dai mu, bada muba” sanna yace Muna fatan za a yi mana adalci kada aje ace mun zagi Sahabbai, domin abinda ke faruwa kenan a wasu masallatai. Ya ce, “ba babatu zaka yi ba, yadda na karanta littattafai  da hujjoji da dalilai , kai ma sai ka yi haka. Idan wani yana jin ba haka bane, shi ma sai ya tara mutane ya karanto masu littatafai da suke nuna ba haka ba ne.”
An dai kammala wannan taro da majalisin mawaka, inda mawakan gwagwarmaya suka hadu suka wake  munasabar Ghadir sannan aka rufe taro da addu’a tare  da  yin fatar Allah ya dawwamar da mu akan wilaya da Imam Ali(AS).

Saturday, October 6, 2012

AN KADDAMAR DA MAKARANTAR HARDAR AL'QUR'ANI MAI GIRMA A YANKIN KATSINA

Gatancin da zaka yi ma danka shi ne ka ba shi ilimi, musamman ma na addini.Malam Yakubu Yahaya ya bayyana haka a yayin kaddamar da  makarantar hardar alkur’ani mai girma da Da’irar ‘yanuwa Musulmi almajiran Sayyid Ibrahim ZakzakY(H) yankin Katsina ta gabatar a ranar 20 / 11/ 1433 a  matsugunnin  makarantar na gajeren lokaci da ke tsohuwar Markaz dake Unguwar vyari a cikin birnin Katsina.
A farkon jawabin nasa, Malam Yakubu ya tabo kadan daga cikin tarihin yadda aka fara gabatar da karatun harder al’Qur’ani tun daga lokacin Sahabban Manzon Allah, a lokacin da suka fahinci cewa, mahardatan al’Qur’ani suna karanta sakamakon Shahada da wasunsu suka yi a fagen fama.
Malam Yakubu ya ci gaba da bayyana cewa, al’Qur’ani shi ne jogon tafiya a wnnan harka ta Musulunci, shi ne kuma zaya gyara al’umma kamar yadda ya gyara al’ummomin baya.Ya tabo yadda turawa suka sami ci gaba sakamakon shiga kaashen musulmi da suka yi suka karanto ilmomi da malaman musulunci suka rubuta sakamakon karantar al’Qur’ani, sai ya nuni da cdewa da Bature bai zo ya yi mana barna ba, da yanzu mun kai wani matsayi na ci gaba.sai ya bayyana cewa, za a karantar da al’Qur’ani da manufar samar da ilimomi da fannoni daban-daban domin samar dam asana da suka san duniya kuma suka san Lahira.Ya ce,” za a koyar da duk wani fanni na ilimi, wannan shi ne gurinmu”
A wani sashen jawabin nasa,Malam Yakubu ya ankrar da dukkan ‘yanuwa cewa, kasancewar wannan makaranta ta fara ne a mazauni na gajeren lokaci kafin samar da mazaunin tan a dindindin, akwai bukatar ‘yanuwa su san da cewa, akwai aikin samar da wannan mazauni sannan kuma ga shirin samar da makarantar Sakandare ta Fudiyya da shi ma ake yunkurin yi domin samar da ingantaccen ilimi ga ‘ya’yanmu.Saai ya gode ma wadanda aka dora ma nauyin ganin an fara wannan karatu sannan ya bukaci iyaye das u koma makaranta domin gyara ma yaransu duk wani nkuskure da zasu yi a lokacin da suke bita a gida, domin wanda baida abu ba zaya iya bayar da shi ba.
A karshe, Malam Yakubu ya nasihanci malaman wannan makaranta da yin hakuri da matsalolin da zasu iya fuskanta a yayin tafiyar da harkokin wannan makaranta.
A zantawar da almizan ta yi das hi, shugaban Lajnar makarantar ta Tahfizul Qur’ni, malam Shehu karkarku, ya bayyana cewa samar da wannan makaranta aiwatar da irshadin da sayyid Ibrahim Zakzaky(H) ne ya yi a shekaru biyu da suka gabata a kano yayin saukar karatu da aka gabatar, inda ya bukaci kowane yanki ya samar da irin wannan makaranta.
An kammalam wannan taro na kaddamarwa ta hanyar yanke zare da Malam Yakubu ya yi ,sannan ya fara karantar da yaran a matsayin fara karatu a wannan sashe na harder littafin Allah mai girma. 

MUZAHARAR NUNA KIN JININ FIM DIN BATANCI GA ANNABIN RAHAMA A BIRNIN MARADI, JAMHURIYAR NIJAR

Kamar sauran takwarorinsu na duniya, ‘yanuwa musulmi almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) na yankin jihar Maradi dakewaye dake Jamhuriyar Nijar, sun gabatar da gagarumin jerin gwano na nuna kyama da kiyayya ga fim din batanci ga Annabin rahama Muhammad (S) a ranar Assabat 13/ 11/ 1433.
Malam Sulaiman Gidan Runji ne ya gabatr da jawabin rufe wannan jerin gwano,inda ya bayyana godiya ga allah (T) da ya yi mu musulmi a karkashin jagorancin Manzon allah(S),sannan ya bayyana ma al’umma manufar wannan jerin gwano da cewa, manufar it ace nuna goyon baya ga Mnazon alla, tare da nuna kin yarda ga abinda wannan la’ananne ya yin a cin mutunci annabi Muhammad(S).
Malam Sulaiman Gidan runji ya bayyana cewa, masu wannan yunkuri na bata martabar Manzon Allah . sun riga sun makara,domin tuni alla madaukakin Sarki ya riga ya daukaka bawansa.ya kara da cewa, wannan yunkuri, sun yi shi ne domin su tsokani musulmi, su kuma gwada su ga ko su musulmin  barci suke.to sai mu ce masu, “Kule!Domin a shirye muke mu bayar da jinanenmu a shekar domn kare martabar Manzon allah(S)
Ya yi kira tare da bayyana cewa,wannan abu bay a shafi  wadanda suka  zagaya  bane, a a ya shafi dukkan musuli ne gaba daya, ya mkara da cewa, har ma wanda ba musulmi ba matukar ya san abin da ake ce ma addini, to ba zaya soace ga wani yana cin zarafin addini ba.
Sai ya gargadi wadanda suka saka wani yanki na fim din das u guji saka sauran wannan la’anannen fim, domin kuwa ian suka gigin saka sauran .zasu ga abin da basu tsammani.
Shi dai wannan jerin gwano, an fara shi ne da misalign karfe tara na safiya,sannan an soma shi ne daga  Masallacin kofar gidar Sarkin Maradi yabi titunan garin aka kuma kamala shi  a wata unguwa da ake ce ma Tiribi.
Andai kamala wannan jerin gwano lafi tare da kona tutocin Amerika da zanen kafiranda suka wallafa wannan mummunan fim, gami da tsinuwa ga wadanda suka shirya fim did a masu goya masu baya.

HOTUNAN JERIN GWANON NUNA KYAMA GA FIM DIN ZIN ZARAFIN MANZON ALLAH A GARIN MARADIN JAMHURIYAR NIJAR

Sunday, July 15, 2012

AN GABATAR DA TARON YAUMUTTKLIF A DA'IRAR KATSINA

An bayyana takalifi da cewa shi ne a sa ka yin abinda  baka son yi, a  kuma  hana ka yin abinda kake  son ka yi. Malam Yakubu Yahaya  wakilin ‘yanuwa  almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) na da’irar  Katisna da kewaye  ne  ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da jawabi ga kananan yara  maza da matan  da suka kai shekarun  wajabcin shari’a  a kansu, a bukin “yaumut  taklif” wanda  dandalin matasa na yankin  ya shirya aka gabatar da  shi a ranar Lahadi  19/ 8/1433  a markazin ‘yanuwan dake  garin Katsina.

A farkon jawabin sai da Malam  Yakubu  ya kawo ma yaran wasu abubuwa da yara suka fi fifitawa, inda ya tambaye su abin da yaro ya fi bukata tsakanin ranaikun karatu  da kuma na hutun makaranta, ranar barci  da tashi ayi salla cikin lokaci  dangane  da sallar Asubahi  da dai  sauran misalai  makamantan wadannan. Sai ya  kara bayanin cewa, shi  takalifi baya  nufin Allah ya  dankara ma mutum aiki ne,  sai dai  domin a lahira Allah za ya canja ma mutum din ne da abin da ya hanu  a duniya  da   abinda  yake a lahira.
Malam Yakubu  ya  bayyana  ma yaran cewa, ana fara addini  ne  tun mutum  yana  yaro,  ba sai an girma ba ne ake  fara yinsa, sai  ya ce, idan ka ga tsohon  banza, to babu shakka yaron banza ya  taso, haka ma abin yake  idan  ka ga tsohon kirki, to ya taso ne a yaron kirki, inda ya ba yaran misalin  Shehu  Usman dan Fodiyo muijaddadi (RA)  yadda ya taso da kirki tun yana yaro ya kuma yi  rayuwar  kirki, ga kuma Imam Khomaini(KS) shi ma haka ya taso, kana Sayyid Zakzaky(H) shi ma  haka rayuwarsa  take, sai ya karfafa  cewa, duk inda ka ga yaron kirki  to za ya zama tsohon kirki, haka ma idan kaga sabanin wannan.  Sai ya tambayi  yaran ko akwai wanda ya ke so ya yi irin  tsufan  su Malam Zakzay (H), inda duk cikar su  suka amsa da cewa, E!. Sai ya yi fatan Allah (T)  ya tabbatar da haka.
 Malam  Yakubu, ya jawo hankulan  yaran da cewa, idan aka kai shekaru  irin nasu, to ba a bukatar  yaro ya bata Sallarsa  idan yana yi,  ko kuma ya boye ya ci wani abu idan yana Azumi,  ya ce , wanda duk ya yi haka ,to ana binsa  bashi sai ya rama su, idan ma azumi ne sai ya kara da guda  sittin(kaffara)  sakamakon bata daya da ya yi. Sannan ya kiraye su da cewa, ba a bukatar su zama masu karya , cin amana, su kuma zamo masu biyayya ga iyayensu, su kuima  lizimci yin amfani da  abubuwan  da  suke  koyo a makarantu na addini da aikatawa tun daga wannan rana har zuwa mutuwa. Sannan ya bukaci malamai da iyaye da su kara kulawa da sallar yaran a makarantu  da kuma gidajensu  har ya zamo sun saba. Sannan aka gabatar da salla raka’a  biyu wadda  Malam Yakubun  ya jagoranta  domin  koya ma yaran yadda ake bukatar su rika gabatar da ita a duk  sa’adda lokacin ta ya  gabato.
Shi dai wannan  biki na ‘yaumut taklifi’ an  gabatar da shi ne da zimmar  zaburantar da yaran da shekarunsu  suka  kama  daga tara zuwa sama  ga ‘yan mata, su kuma maza daga goma sha  biyar .
Saidai  a wanna karo an lura da cewa,  wadanda suka halarci wannan taro akwai kananan yaran da shekarun  nasu basu kai wadanda  aka bukata ba, abinda ya jawu yin kira da cewa, wasu sai an sake dawowa da su a wasu shekaru masu zuwa nan gaba, kamar yadda Malam Yakubu ya bukata.  An dai kammala wannan biki karo na  farko cikin nasara.

AN GUDANAR DA BIKIN YAYE DALIBAN FUDIYA TA KATSINA A KARO NA GOMA

A ranar Assabat 25/8/1433 da ya zo daidai 14/ 7 2012, makarantar Fudiyya Nursery and Primary Katsina ta gabatar da bikin yaye dalibanta karo na goma na wannan shekara wanda aka gabatar a unguwar Filin Sanji Katsina.

A jawabin da ya gabatar babban bako kuma Daraktan makarantar, Malam Yakubu Yahaya ya bayyana cewa, hakuri shi ne maganin dukkan matsala, ya tabo tarihin fara karatu a wannan makaranta inda ya bayyana yadda mkarantar ta somo tun ana karantarwa a zaurukan jama’a da aka ara, kama-kama har zuwa wannan wuri bayan samun damar ginawa, ya kara da cewa, duk da matsalolin da aka fuskanta, an sami nasarar kutsamasu ne saboda hakuri da malamai suka yi,amma bangare iyayen yara sun kasa yinirin  wannan hakuri da wadannan matsaloli saboda kasa tsayuwa da nauyin da ya rataya ga wuyansu ta fuskar sauke nauyin makaranta, daga nan Malam Yakubu ya bukaci iayaen da su samar da wani asusu wanda za su rika amfani da kudin suna juya su domin bayar da tallafi ga malamai dama  makarantar.

A yunkurin samar da makarantar sakandare da hadin gwiwar kwamitin ahl-duthour da Lajnar Fudiyya suka fara, Malam Yakubu ya yi tuni garesu da su yi kokari su samar da koda karamar Sakandare(JSS) ta yadda idan Dairar ta sami dama sai ta samara da babbar sakandare(SSS), sanna ya ce, idan zai yiwu yaran da za su fita shekara mai zuwa su  fara  da ita, musamman idan aka yi la’akari da  tabarbarewar tarbiyya a makarantu. Sannan Malam Yakubu ya bayyana cewa,”muna da babban guri akan yaranmu, tunda a yanzu komai ya ruguje a wannan kasa kuma babu wani abu da yake ginuwa a yanzu sai wannan harka”. Sai ya yi kira ga kungiyar tsofaffin dalibai na fudiyyar(FOSA) da su yi kokari su shige ma yaran makarantar  gaba domin  kawo ma makarantar ci gaba”.

A tun farko da yake gabatar da jawabi, shugaban makarantar Fudiyya, Malam Kabir Sani, godiya ya nuna ga da’irar “yanuwa ta Katsina akan fadada makarantar da ta yi, sannan ya bayyana shirin da ake yi na fara karatu bangaren Islamiyya  wanda za a fara gabatar da shi bayan dawowa hutun sabuwarv shekarar karatun makaranta.

An dai kammala wannan biki da bayar da kyaututtuka ga wasu iyaye da suka yi fice wajen bayar da gudunmuwa ga makaranta a wannan shekara tare da nada sabbin shugabannin dalibai na wannan shekara.  

Sunday, July 8, 2012

AN GABATAR DA BIKIN YAUMUT TAKLIF A GARIN KATISANA