Saturday, October 6, 2012

AN KADDAMAR DA MAKARANTAR HARDAR AL'QUR'ANI MAI GIRMA A YANKIN KATSINA




Gatancin da zaka yi ma danka shi ne ka ba shi ilimi, musamman ma na addini.Malam Yakubu Yahaya ya bayyana haka a yayin kaddamar da  makarantar hardar alkur’ani mai girma da Da’irar ‘yanuwa Musulmi almajiran Sayyid Ibrahim ZakzakY(H) yankin Katsina ta gabatar a ranar 20 / 11/ 1433 a  matsugunnin  makarantar na gajeren lokaci da ke tsohuwar Markaz dake Unguwar vyari a cikin birnin Katsina.
A farkon jawabin nasa, Malam Yakubu ya tabo kadan daga cikin tarihin yadda aka fara gabatar da karatun harder al’Qur’ani tun daga lokacin Sahabban Manzon Allah, a lokacin da suka fahinci cewa, mahardatan al’Qur’ani suna karanta sakamakon Shahada da wasunsu suka yi a fagen fama.
Malam Yakubu ya ci gaba da bayyana cewa, al’Qur’ani shi ne jogon tafiya a wnnan harka ta Musulunci, shi ne kuma zaya gyara al’umma kamar yadda ya gyara al’ummomin baya.Ya tabo yadda turawa suka sami ci gaba sakamakon shiga kaashen musulmi da suka yi suka karanto ilmomi da malaman musulunci suka rubuta sakamakon karantar al’Qur’ani, sai ya nuni da cdewa da Bature bai zo ya yi mana barna ba, da yanzu mun kai wani matsayi na ci gaba.sai ya bayyana cewa, za a karantar da al’Qur’ani da manufar samar da ilimomi da fannoni daban-daban domin samar dam asana da suka san duniya kuma suka san Lahira.Ya ce,” za a koyar da duk wani fanni na ilimi, wannan shi ne gurinmu”
A wani sashen jawabin nasa,Malam Yakubu ya ankrar da dukkan ‘yanuwa cewa, kasancewar wannan makaranta ta fara ne a mazauni na gajeren lokaci kafin samar da mazaunin tan a dindindin, akwai bukatar ‘yanuwa su san da cewa, akwai aikin samar da wannan mazauni sannan kuma ga shirin samar da makarantar Sakandare ta Fudiyya da shi ma ake yunkurin yi domin samar da ingantaccen ilimi ga ‘ya’yanmu.Saai ya gode ma wadanda aka dora ma nauyin ganin an fara wannan karatu sannan ya bukaci iyaye das u koma makaranta domin gyara ma yaransu duk wani nkuskure da zasu yi a lokacin da suke bita a gida, domin wanda baida abu ba zaya iya bayar da shi ba.
A karshe, Malam Yakubu ya nasihanci malaman wannan makaranta da yin hakuri da matsalolin da zasu iya fuskanta a yayin tafiyar da harkokin wannan makaranta.
A zantawar da almizan ta yi das hi, shugaban Lajnar makarantar ta Tahfizul Qur’ni, malam Shehu karkarku, ya bayyana cewa samar da wannan makaranta aiwatar da irshadin da sayyid Ibrahim Zakzaky(H) ne ya yi a shekaru biyu da suka gabata a kano yayin saukar karatu da aka gabatar, inda ya bukaci kowane yanki ya samar da irin wannan makaranta.
An kammalam wannan taro na kaddamarwa ta hanyar yanke zare da Malam Yakubu ya yi ,sannan ya fara karantar da yaran a matsayin fara karatu a wannan sashe na harder littafin Allah mai girma. 

No comments:

Post a Comment