Kamar sauran takwarorinsu na duniya, ‘yanuwa musulmi almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) na yankin jihar Maradi dakewaye dake Jamhuriyar Nijar, sun gabatar da gagarumin jerin gwano na nuna kyama da kiyayya ga fim din batanci ga Annabin rahama Muhammad (S) a ranar Assabat 13/ 11/ 1433.
Malam Sulaiman Gidan Runji ne ya gabatr da jawabin rufe wannan jerin gwano,inda ya bayyana godiya ga allah (T) da ya yi mu musulmi a karkashin jagorancin Manzon allah(S),sannan ya bayyana ma al’umma manufar wannan jerin gwano da cewa, manufar it ace nuna goyon baya ga Mnazon alla, tare da nuna kin yarda ga abinda wannan la’ananne ya yin a cin mutunci annabi Muhammad(S).
Malam Sulaiman Gidan runji ya bayyana cewa, masu wannan yunkuri na bata martabar Manzon Allah . sun riga sun makara,domin tuni alla madaukakin Sarki ya riga ya daukaka bawansa.ya kara da cewa, wannan yunkuri, sun yi shi ne domin su tsokani musulmi, su kuma gwada su ga ko su musulmin barci suke.to sai mu ce masu, “Kule!Domin a shirye muke mu bayar da jinanenmu a shekar domn kare martabar Manzon allah(S)
Ya yi kira tare da bayyana cewa,wannan abu bay a shafi wadanda suka zagaya bane, a a ya shafi dukkan musuli ne gaba daya, ya mkara da cewa, har ma wanda ba musulmi ba matukar ya san abin da ake ce ma addini, to ba zaya soace ga wani yana cin zarafin addini ba.
Sai ya gargadi wadanda suka saka wani yanki na fim din das u guji saka sauran wannan la’anannen fim, domin kuwa ian suka gigin saka sauran .zasu ga abin da basu tsammani.
Shi dai wannan jerin gwano, an fara shi ne da misalign karfe tara na safiya,sannan an soma shi ne daga Masallacin kofar gidar Sarkin Maradi yabi titunan garin aka kuma kamala shi a wata unguwa da ake ce ma Tiribi.
Andai kamala wannan jerin gwano lafi tare da kona tutocin Amerika da zanen kafiranda suka wallafa wannan mummunan fim, gami da tsinuwa ga wadanda suka shirya fim did a masu goya masu baya.
No comments:
Post a Comment