Monday, November 26, 2012

AN GABATAR DA KARATUN IDUL GHADIR NA KWANA UKU A KATSINA


 
 Kimanin kwana ukku aka kwashe ana gabatar da tarurrukan tunawa da munasabar  Idil Ghadir, domin tuna ma al’ummar musulmi wasiyyar da Manzon rahama ya yi a hajjin bankwana ,a ranar 18 ga watan zulhijja  bayan da ya kammala aikin  hajji  zaya koma Madina, taron da Da’irar ‘yanuwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky(H) ta Katsina ta shirya tare da gabatar da shi tun daga ranar Talata 21 har zuwa Alhamis 23 ga zulhajjin wannan shekara ta 1433.

A wannan taro Malam Yakubu Yahaya ya gabatar da karanto falalolin Iyalan gidan Manzon  Allah Musamman Imam Ali(AS) domin al’umma ta fahimci irin matsayinsa da jarumtakarsa hada da ilimin da Allah ya bashi domin dai ya zamo Halifar Manzon Allah bayan wafatinsa. Haka kuma a wannan biki, malam Yakubu ya karanto doguwar hudubar da Annabin rahama ya karanta a wancan lokaci.
Bayan kammala karance-karancen ne, malam yakubu ya ankarar da al’umma cewa, wannan al’amarin da ya faru na bijire ma wasicin Annabi da wasu suka yi, ba ana karantawa ba ne domin ana kiyayya da wasu kamar yadda wasu suke gani, a’a saidai ana karantawa ne domin al’umma ta san hakikanin sakon da wadanda aka ce abi bayan wafatin Manzon.
A jawabin nasa ya yi nuni da yadda sakamakon bijire ma wasicin aka kirkiro abubuwa na addini wadanda ba Manzon Allah ne ba  ya yi umurni da yinsu , inda ya bada misalin kiran salla biyu da ake yi a ranar Juma’a, abinda ya ce  mai Risala ya bayyana da cewa, banu Umayya ne suka kirkiro shi, haka kuma a kokarin rufe matsayi na Imama Ali(A) sannan ya ce, kimanin kashi saba’in da biyar  cikin dari na addini da ake yi  duk an kirkiro su ne bayan wafatin Manzon Allah duk dai domin ganin an kauce ma wasicin  bin Imam Ali (AS) , ya kara da cewa, akan haka ne ma Mu’awiyya ya tara malamai suka yi ta kirkiro Hadisan falalar wasu Sahabbai don rufe matsayuin Iayalan Annabi, wannan ya sa aka kwashe shekaru ana zagin Imam Ali(AS)  da Iyayensa , matarsa , ‘ya’yansa dama duk wanda ke binsa, Malam Yakubu ya ce, bayan zagin imam din wasu ma sun kara da yin izgili, inda halifa Mutawakkil yake yin shiga irin ta Imam Ali ya  fito fada , yadda da an gan shi sai ayi ta keta dariya waidai domin nuna izgili. Ya ce, Mutanen da Allah ya yi  Umurnin a girmama, sune aka  koma ana zagi da yi masu izgili.
Malam Yakbu ya bayyana cewa,akwai bukatar al’umma ta fahinci abinda muke cewa tunda addini muke yi, kuma shi ne zamu yi sannan mu tsira, kuma gaskiya tana nan sannan dole wannan gaskiya ce zamu yi. Sai ya tabbatar da cewa, tabbas an jaraba Sahabbai akan wannan lamari, wasu sun ci jarabawar wasu kuma  sun fadi kamar yadda aka jaraba wasu al’ummu suka fadi.sannan ya tabbatar da cewa, “ duk fa wanda ya gitta ma Manzon Allah. To fa zamu gitta masa kowanene, iyakar gaskiyar wannan Magana kenan, amma ba muna gaba da wani sahabi bane, basu  yi mana laifin komai ba, kuma basu bamu haushi  kuma Allah ya ba su, sun ga Manzon Allah, sun bi shi Sallah sun kuma yi jihadi  tare da shi ,amma daga baya wasu sun fadi jarabawa, wasu kuma sun ci. saboda haka wadanda suka ci jarabawa muna tare da su dari bisa  dari, wadanda suka fadi kuma al’amarinsu yana wurin Allah, amma dai mu, bada muba” sanna yace Muna fatan za a yi mana adalci kada aje ace mun zagi Sahabbai, domin abinda ke faruwa kenan a wasu masallatai. Ya ce, “ba babatu zaka yi ba, yadda na karanta littattafai  da hujjoji da dalilai , kai ma sai ka yi haka. Idan wani yana jin ba haka bane, shi ma sai ya tara mutane ya karanto masu littatafai da suke nuna ba haka ba ne.”
An dai kammala wannan taro da majalisin mawaka, inda mawakan gwagwarmaya suka hadu suka wake  munasabar Ghadir sannan aka rufe taro da addu’a tare  da  yin fatar Allah ya dawwamar da mu akan wilaya da Imam Ali(AS).

No comments:

Post a Comment