Friday, December 2, 2011

DANDALIN MATASA YA KAI ZIYARA A GARIN JIIYA


 A yunkurin da yake yi  na fadada ayyukansa, dandalin Matasa na harkar Musulunci  a da’irar Katsina da kewaye,ya kai ziyarar murnar zagayowar Idul Gadeer na wannan shekara a garin Jibiya a ranar Talata 26/12/1432.


Da yake bayyana manufar wannan ziyara, danuwa Shamsuddini Ahmad  wanda daya ne daga cikin jagororin wannan Dandali a Katsina, ya ce, wanna  ziyara na da nufin ankarar da matasa  ‘ya’yan ‘yanuwa na Jibiya ne  tare da jawo su a jiki domin sauke nauyin wanna  Harka da ya rataya  a wuyansu a matsayinsu na manyan gobe ta hanyar danfara su da harkar tare da isar da ita ga abokansu na cikin gari

Malam Iliya Jibiya wakilin ‘yanuwa almajiran Sayyid Zakzaky(H) shine ya gabatar da takaitaccen jawabin maraba ga bakin wanda a ciki ya bayyana bukatuwar da gwagwarmayar nan keda ita ga matasan kasantuwarsu masu jini a jiki da zaya basu damar tsayuwa akan ayyukan tallafama al’umma, sannan ya ce,kasantuwarsu matasa suna da cikakkiyar damar gabatar  da Ibada zuwa ga maliccinsu sannan ya neme su su dage akan Imani da bauta ma Allah (T) da kuma gwagwarmayar tabbatar addini domin tsamo al’umma daga halin da azzalumai da zalunci ya saka su a ciki.ya yi tir da dabi’ar wasu matasan da mamakin kin halartar al’aummurran addini, ta yadda bazaka iya bambance su da sauran abokai  da basu da fahimtar addini. sannan ya nemi matasan su dage wajen neman ilimin addini da  zamani don fahimtar halin da ake ciki musaman ma a wannan zamani na dunkulewar duniya. Ya yi fatan dandalin zaya rika aike matasansu da duk wata gayyatar  wani taro nasu na wannan harka.

Shidai wannan dandali na matasa a wannan yanki na Katsina ya na iya kokarin hada kan matasan na wannan harka dake sassan da’irori domin su fahimci bukatar dake da akwai ta maido hankulansu domin halartar duk wasu al’amurra na addini da harkar ke gabatarwa tare da aiwatar da ayyukan taimakon jama’a kamar yadda Sayyid Zakzak(H) ke kira akai.





Sunday, November 20, 2011

DANDALIN MATASA YA GABATAR DA TARON MURNAR ZAGAYOWAR RANAR DA MANZON ALLHA YA NADA WAKILINSA


Dandalin matasa Na harkar musulunci a karkashin jagorancin Sayyid Ibarahim Zakzaky(H) dake garin Abukur dake karamar hukumar Rimi ta jihar Katsina sun gabatar da taron tunawa da Idul Gadeer a harabar makarantar Fudiyyah Islamiyya dake garin na Abukur a ranar Assabat 23/ 12/ 1432.


Malam Aminu Jakara wakilin ‘yanuwa almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) na Da’irar Rimi ne babban bako da ya gabatar da jawabi a wannan taro, ya bayyana wannan Idi na gadeer da cewa shine babban Idi kamar yadda aka tambayi Imam Ja’afarus Sadiq (AS) ko akwai wani Idi bayan idin karamar salla da babba da ake dasu , inda ya amsa da cewa, akwai wanda ya fisu, shine idil Gadeer watau ranar da Manzon Allah(S) ya ayyana Imam Ali (AS) wakilinsa bayansa.

Malam Aminu ya bayyana cewa, samun kanka a cikin wadanda suka yi wila’a ga Iayalan gidan Annabi ba dubararka ba ce, ni’ima ce daga Allah (T), domin wasu suna gaba ne da su, don  haka ya zama wajibi gode ma wanna ni’ima ta hanyar yin aiki.Ya ce kallon ayyukan  Sayyid Zakzaky (H) da kyakkyawar fahimta da aiki akan abinda Sayyid din ya ke kira akansa yana daga cikin godiya da wannan ni’ima.

Sai ya yi kira ga Matasan da su ribanci wannan lokaci na su na kuruciya kafin damar ta kubuce masu. Ya kara da cewa, zaka iya rasa dukiya  da makamancin haka  kuma ka riske ta, amma idan rayuwarka ta zo karshe baka ribance ta ba, to zaka yi nadamar ayyukan da baka yi ba, haka kuma matashi zai yi nadama idan bai yi abinda ya kamata ba har tsufa ya riske shi.Sai ya jawo hankalin matasan da su yi amfani da damar da suka samu ta fahimtar addini su yi aiki na tallafama addinin kafin damar ta kubuce masu musamman wannan lokaci da al’umma take yayin addini. Sannan ya yi kira ga matasan  da su rika tunanin  makoma Lahira domin kauce ma fadawa mummunar makoma a nan duniya da gobe kiyama. Ya shawarci matasan da cewa, kamata ya yi tunaninsu ya zama kaka  zasu taimaka ma al’umma ta fita daga wannan hali da take ciki na zalunci da rashin hukunci da littafin Allah. Sannan ya bukace su da s u kyautata dabi’unsu, su himmantu ga neman Ilimin addini da kauce ma tunanin tara abin duniya ko ta wane hali gami da sa tunanin tsamar da al’umma fita daga mawuyacin halinda   take a ciki na danniya. Sai ya yi fatan Allah ya kara taimaka ma matasan  wajen ganin sun tsayu akan yin abinda Sayyid (H) yake da fata akansa.

A tun farko sai da daya daga cikin jagororin dandalin matasan na Katsina, Shamsu ya gabatar da mai  jawabi inda ya bayyana makasudin wannan taro da cewa na taya juna murnar zagayowar ranar da Annabi (S) ne ya nada ma Al’umma  Imam Ali(AS)  matsayin jagora ne  a bayansa.

Kafin nan  sai da aka gabatar da wata tamsiliyya mai taken”da’awar  dandalin matasa” wadda ta yi nuni da rawar da y  kamata matasa su taka  wajen  janyo hankulan abokai akan su yi riko da addini tare da yin watrsi da duk wata dabi’ar da ta saba ma addinin.    






DA'IRAR YANUWA MUSULMI TA KATSINA TA GABATAR DA IDUL GADEER NA KWANA BIYU


Da irar ‘yanuwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky(H) ta  Katsina sun gabatar da taro na kwana biyu domin  murnar zagayowar ranar da Manzon Allah(S) ya ayyana magajinsa ga wannan al’umma watau Idil Gadeer  wanda wakilin ‘yanuwan na garin Malam Yakubu Yahaya ya gabatar a ranakun 20 da 21 ga watan Zulhijja  na wannan shekara ta 1432.

A zaman farko, Malam Yakubu ya karanto Hadisai ne masu dama daga cikin littafan magabata na Sunna  ba, da suke nuni da matsayi da fifikon Imam Ali (AS) akan sauran Saahabban Manzon Allah(S). Malam Yakubu ya ce, bamu ce sauran Sahabban Annabi basu da kima bane,sai dai abinda muka ce shine,daga Allah(T) sai Annabi A wajen daraja sannan sai Iyalan gidansa sannan Sahabbai suna bi masu a darja. Ya karanto HAdisan ne daga cikin littattafai irinsu Silsilatul-ahadisil maudu’ah ,al fada’ilu na Ahmad bn Hanbal, iqtibasu siradul mustaqima na ibni Taimiyyah da sauran Tafsirai da dama.Ya kara da cewa, ya kawo wadannan hujjoji ne domin tabbatar matsayi na Imam Ali(AS) domin masu musu su san cewa suna yin e da Manzon Allah(S), sannan ya kara da cewa, duk wadannan littattafai muna karanto sun e ba domin kkure basai domin mu gano gaskiya mu kuma yi riko da ita tunda matsaloli sun faru a wannan addini bayan wafatin Manzon Allah(S).

A rana ta biyu,Malam Yakubu ya karanto doguwar khudubar Manzon Allah wadda ya yi a wannan rana,ya karanto ta daga wasu littafai da suka kawo wani sashe na khudubar, sananan ya karanto ta a kammale daga ruwayar ahlul baiti(AS).
Ranar Gadeer, ran ace wadda Manzon Allah ya nada Imam Ali (AS) da umurnin Allah a matsayin Khalifarsa bayan wafatinsa.

A rana ta biyu bayan kammala wannan karatu, Malam Yakubu ya jagoranci  yanka cake na murnar wannan biki wanda ‘yanuwa na Acadamic forum suka tanada.An kamala wannan taro cikin nasara kamar yadda aka tsara tare da fatan Allah ya nuna mana zagayowar na badi.
















Sunday, October 16, 2011

ITTIHADUS SHU'ARA YANKIN KATSINA, KANO DA JIGAWA SUN GUDANAR DA TARON KARAMA JUNA SANI NA KWANAKI BIYU A KATSINA


Bangaren mawakan gwagarmayar musulunci karkashin jagorancin Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) na yankin Kano , Katsina da Jigawa, sun shirya tare da gabatar da taron karawa juna sani (Mu’tamar) na kwana biyu da aka gabatar da shi a Markazin “yanuwa musulmi dake Katsina daga ranar Juma’a 17/11 1432 zuwa Lahadi 19/11/ 1432.



A jawabin da ya gabatar, a loacin kammala wannan Mu’tamar, Malam Yakubu Yahaya wakilin ‘yanuwa na Katsina, ya yi kira ga mawakan gwagwarmayan da su fahimci cewa, Allah (T) ya yi masu baiwa, don haka su yi amfani da ita wajen isar da sakon gwagwarmaya ta yadda za su wayar ma jama’a da kai akan bara’a da wilaya gami da fadakar da su zaluncin da ke tafiyar ra rayuwar al’umma musamman Musulmi, domin ita waka tana da wani tasiri a zukatan al’umma.Ya ce,amma akwai bukatar su mawakan su kasance masu kyawawan dabi’u a dukkan ma’amalarsu da sauran jama’a, gami da tsayuwa akan muahada, ta yadda za su iya ba harkar kariya, sannan akwai bukatar sakonsu ya rika fitowa daga zuciya, domin duk sakon da ya fito daga zuciya ,to dole ne ya ratsa zukata, amma wannan za ya samu ne kawai idan an dage akan mujahada , tsarkin niyya tare da yi domin Allah, sanna kuma abin da kake fada ya dace da abin da kake aikatawa.

A wani sashe na jawabin , Malam Yakubu ya bayyana wajabcin mawakan su dage wajen neman Iliomi na addini tare da sanin tarihin A’imma(AS) ta yadda za su iya bayyana hakikanin yadda suka suka rayu, domin wanda baya da sani akan abu babu yadda za ya iya yin bayani a kansa. Ya kuma yi kira ga mawakan da su himmatu wajen tsara wakoki a bangarorin Addini daban –daban da suka hada da Tauhidi ingatacce, Kyawawan dabi’u, Gudun duniya da sauran bangarori da dama kari akan na gwagwarmaya da na ahlu-baiti(AS). A karshe ya karfafa yin dukkan al’amari domin Allah.

Taron na kara ma una sanin na kwana biyu , ya sami halartar malamai da suka hada da ; Malam Shehu Karkarku, Malam Abdul Karim Usama, Malam Ibrahim Ya’u da Malam Abubakar Kofar Durbi, inda suka gabatar da jawabai a lokuta daban-daban, jawaban da suka hada da Muhimmancin Ilimi ga mawakin gwagwarmaya, makarimul akhlaq, gudunmuwar mawaka ga harkar Musulunci , kyautata dangantaka a tsakanin juna.

Mawaka daga yankin Kano da Katsina suka sami halartar wannan Mu’tamar da suka hada da Mustafa Limanci, Gambo dan kaka, Aminu Jakara Abdussalam Ibrahim da sauran mawaka da dama, tuni aka kammala taron a cikin nasara.
Wani sashe na mawakan da suka halarci taron

wasu daga cikin mahalarta suna sauraren jawabi