A yunkurin da yake yi na fadada ayyukansa, dandalin Matasa na harkar Musulunci a da’irar Katsina da kewaye,ya kai ziyarar murnar zagayowar Idul Gadeer na wannan shekara a garin Jibiya a ranar Talata 26/12/1432.
Da yake bayyana manufar wannan ziyara, danuwa Shamsuddini Ahmad wanda daya ne daga cikin jagororin wannan Dandali a Katsina, ya ce, wanna ziyara na da nufin ankarar da matasa ‘ya’yan ‘yanuwa na Jibiya ne tare da jawo su a jiki domin sauke nauyin wanna Harka da ya rataya a wuyansu a matsayinsu na manyan gobe ta hanyar danfara su da harkar tare da isar da ita ga abokansu na cikin gari
Malam Iliya Jibiya wakilin ‘yanuwa almajiran Sayyid Zakzaky(H) shine ya gabatar da takaitaccen jawabin maraba ga bakin wanda a ciki ya bayyana bukatuwar da gwagwarmayar nan keda ita ga matasan kasantuwarsu masu jini a jiki da zaya basu damar tsayuwa akan ayyukan tallafama al’umma, sannan ya ce,kasantuwarsu matasa suna da cikakkiyar damar gabatar da Ibada zuwa ga maliccinsu sannan ya neme su su dage akan Imani da bauta ma Allah (T) da kuma gwagwarmayar tabbatar addini domin tsamo al’umma daga halin da azzalumai da zalunci ya saka su a ciki.ya yi tir da dabi’ar wasu matasan da mamakin kin halartar al’aummurran addini, ta yadda bazaka iya bambance su da sauran abokai da basu da fahimtar addini. sannan ya nemi matasan su dage wajen neman ilimin addini da zamani don fahimtar halin da ake ciki musaman ma a wannan zamani na dunkulewar duniya. Ya yi fatan dandalin zaya rika aike matasansu da duk wata gayyatar wani taro nasu na wannan harka.
Shidai wannan dandali na matasa a wannan yanki na Katsina ya na iya kokarin hada kan matasan na wannan harka dake sassan da’irori domin su fahimci bukatar dake da akwai ta maido hankulansu domin halartar duk wasu al’amurra na addini da harkar ke gabatarwa tare da aiwatar da ayyukan taimakon jama’a kamar yadda Sayyid Zakzak(H) ke kira akai.
No comments:
Post a Comment