Dandalin matasa Na harkar musulunci a karkashin jagorancin Sayyid Ibarahim Zakzaky(H) dake garin Abukur dake karamar hukumar Rimi ta jihar Katsina sun gabatar da taron tunawa da Idul Gadeer a harabar makarantar Fudiyyah Islamiyya dake garin na Abukur a ranar Assabat 23/ 12/ 1432.
Malam Aminu Jakara wakilin ‘yanuwa almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) na Da’irar Rimi ne babban bako da ya gabatar da jawabi a wannan taro, ya bayyana wannan Idi na gadeer da cewa shine babban Idi kamar yadda aka tambayi Imam Ja’afarus Sadiq (AS) ko akwai wani Idi bayan idin karamar salla da babba da ake dasu , inda ya amsa da cewa, akwai wanda ya fisu, shine idil Gadeer watau ranar da Manzon Allah(S) ya ayyana Imam Ali (AS) wakilinsa bayansa.
Malam Aminu ya bayyana cewa, samun kanka a cikin wadanda suka yi wila’a ga Iayalan gidan Annabi ba dubararka ba ce, ni’ima ce daga Allah (T), domin wasu suna gaba ne da su, don haka ya zama wajibi gode ma wanna ni’ima ta hanyar yin aiki.Ya ce kallon ayyukan Sayyid Zakzaky (H) da kyakkyawar fahimta da aiki akan abinda Sayyid din ya ke kira akansa yana daga cikin godiya da wannan ni’ima.
Sai ya yi kira ga Matasan da su ribanci wannan lokaci na su na kuruciya kafin damar ta kubuce masu. Ya kara da cewa, zaka iya rasa dukiya da makamancin haka kuma ka riske ta, amma idan rayuwarka ta zo karshe baka ribance ta ba, to zaka yi nadamar ayyukan da baka yi ba, haka kuma matashi zai yi nadama idan bai yi abinda ya kamata ba har tsufa ya riske shi.Sai ya jawo hankalin matasan da su yi amfani da damar da suka samu ta fahimtar addini su yi aiki na tallafama addinin kafin damar ta kubuce masu musamman wannan lokaci da al’umma take yayin addini. Sannan ya yi kira ga matasan da su rika tunanin makoma Lahira domin kauce ma fadawa mummunar makoma a nan duniya da gobe kiyama. Ya shawarci matasan da cewa, kamata ya yi tunaninsu ya zama kaka zasu taimaka ma al’umma ta fita daga wannan hali da take ciki na zalunci da rashin hukunci da littafin Allah. Sannan ya bukace su da s u kyautata dabi’unsu, su himmantu ga neman Ilimin addini da kauce ma tunanin tara abin duniya ko ta wane hali gami da sa tunanin tsamar da al’umma fita daga mawuyacin halinda take a ciki na danniya. Sai ya yi fatan Allah ya kara taimaka ma matasan wajen ganin sun tsayu akan yin abinda Sayyid (H) yake da fata akansa.
A tun farko sai da daya daga cikin jagororin dandalin matasan na Katsina, Shamsu ya gabatar da mai jawabi inda ya bayyana makasudin wannan taro da cewa na taya juna murnar zagayowar ranar da Annabi (S) ne ya nada ma Al’umma Imam Ali(AS) matsayin jagora ne a bayansa.
Kafin nan sai da aka gabatar da wata tamsiliyya mai taken”da’awar dandalin matasa” wadda ta yi nuni da rawar da y kamata matasa su taka wajen janyo hankulan abokai akan su yi riko da addini tare da yin watrsi da duk wata dabi’ar da ta saba ma addinin.
No comments:
Post a Comment