Daga:Abdul Azizi
An bayyana ranar goma ga watan al’Muharram da cewa, rana ce ta bakin ciki da takaici da juyayi.Malam yakubu Yahaya katsina wakilin ‘yanuwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky(H) na yankin Katsina da kewaye ya bayyana haka a lokacin da yake rufe Muzaharar tunawa da ranar da aka kashe jikan Manzon Allah Imam Husaini dan Ali(AS) a ranar Alhamis 11/0 1/ 1432.
Malam Yakubu ya bayyana cewa, ranar Ashura sanannar rana ce wadda bata boyuwa kuma dukkan Musulmin duniya sun santa sama da shekaru dubu da suka gabata.”A nan ma, al’ummarmu ta santa, saidai da wani suna na cika ciki, watau ranar da ake cika ciki kuma da sunan wai hadisi ne da Manzo ya ce. Malam yakubu ya karyata wanan da cewa,” karya ne, babu wata rana da Manzon Allah ya ware ya ce sunanta cika ciki, bilhasali ma, daga rayuwar Manzon Allah an san cewa,Manzo baya cin abinci sai yunwa ta kai masa ko’ina, sannan kuma lokacin da zaya bar abincin yana marmarinsa, sannan kuma ya fada a sahihin hadisi na Sunna cewa, ’dan Adam bai cika wata jikka ta sharri ba fiye da cikinsa.Sai ya ce wannan Sira ta Manzo da wannan Hadisi, sun Karyata wannan riyawa ta cika ciki a wannan rana. Malam yakubu ya tabbatar da cewa, bayan Yazidu ya yi abinda ya yi na kashe jikokin Annabi ne, ya ga duniya ta juya masa, mutane sun fara la’antarsa, sai ya tara malaman fada wadanda suka kware, suka kirkiro Hadisan falala da suka nuna muhimmanci wannan rana da cika ciki a ranar, har takai ga cewa, wanda bai cika nasa cikinba a wannan rana za a cika masa da wuta”wanna karya ne’ inji shi.
Malam Yakubu ya ci gaba da bayyana cewa,tarihi ba ya zaluntar kowa, yana kawo abinda ka yi ne. Duk abinda mutum ya yi yana nan rubuce. Tarihi ya kiyaye wannan kisa da aka yi ma Iyalan Annabi sama da shekaru dubu da suka wuce .ya yi makin yadda mutane suka nace, suke ganin wadanda suka yi wannan kisa a matsayin gwaraza, ya bukaci mutane su gwama tsaklanin wanda ya yi kisa da wanda aka kashe ya gani. Inda ya dan gutsuro tarihin yazidu kamar yadda malaman tarihi suka bayyana shi.Ya ce, malaman na Tarihi sun ce, Yazidu dan giya ne fasikine mazinci ne wanda yake kwana cikin giya. Haka dan Ziyadu wanda aka bayyana da cewa Shege ne marar uba, da sauran munanan dabi’u da musulunci ke kyama. Ya ci gaba da cewa, shi kuwa Imam husaini jika ne ga Manzon Allah jikan khadija dan Sayyida fatima Zahra dan Ali dan Abi Dalib, danuwan imam Hasan(AS), kuma shine wanda manzon Allah ya ce, ”Husaini bangare ne nawa, nima kuma bangare ne nashi” ya ce wannan bawan Allah shine aka yi ma kisan gilla, saboda ya fita neman gyaran al’umma da ta baci bayan Mu’awiyya ya dora ta akan mummunan tafarki sabanin na addini.
Imam Husaini ya fita ne ba domin neman mulki ba, kamar yadda wasu suke gani cikinsu kuma har da malamai. Ya ce, ”Imam Husaini ba milki yake nema ba, domin mai neman mulki baya bada ransa, sai dai ya nemi a sasanta, amma mai neman Lahira wanda yake da sakon shiriya da manufa, yana shekar da jininsa ne saboda sakonsa ya rayu. Wannan kuma shine abinda Imam Husaini (AS) ya yi. Ya kuma wanzar mana da sakon Musulunci na hakika wanda Annabi ya zo da shi, ka sanshi ko baka sanshi ba.
Malam yakubu ya bayyana mamakin yadda wasu Malamai suka fara gunaguni a masallatai akan wannan al’amari na nuna goyon bayan gidan Annabi gami da nuna al’hini akan wannan mummunan ta’addanci da Iyayen gidansu suka aikata, ya kalubalanci malaman da cewa, ’idan kai malam ne, don Allah don Annabi ka kawo hujja ta hankali da shari’a ka kare uban gidanka, ka kuma karyata abinda ya faru. Karya kake” ya ce, ” shure-shure baya hana mutuwa, surutan ana zagin Sahabbai ana cin mutuncin Mu’awiyya ba zaya fitar ta kai ba.” Ya ce, al’amarin nan baya boyuwa, kuma lallai zaya wuce da duk wanda yake fada da shi.”
A takardar da aka raba ma al’umma wadda ta ke bayyana abin da ya faru a irin wannan rana, wadda Malam yakubu ya sa mata hannu, ta nuna cewa,”Wannan al’amari bana na ‘yan Shi’a kadai bane kamar yadda wasu suke gani, kuma koda nasu ne su kadai, to dole ne Musulmi ya nuna inda goyon bayansa yake tsakanin Iyalan Annabi)(SAW) da aka kashe cikin wulakanci da Yazidawa makisa, domin kuwa ba zai taba yiwuwa mutum ya goyi bayan gaskiya da rashin gaskiya ba a lokaci guda sai dai idan shi munafuki ne”
Muzaharar wadda dubundubatar ‘yanuwa musulmi maza da mata suka halarta, an soma ta ne da misalin karfe tara na safe, inda ta kewaye manyan titunan cikin garin Katsina tana dauke da taken ta’aziyya ga Manzon Allah da Iyalansa masu tsarki, gami da wayar da kan sauran al’umma musulmi hakikanin abinda ya faru a irin wannan rana ta goma ga al’muharram.