Sunday, December 5, 2010

ZIYARAR DANDALIN MATASA A ASIBITIN MASU FAMA DA RASHIN HANKALI

 Daga:Abdul Azizi
Bangaren Dandalin Matasa na harkar Musulunci da Malam Zakzaky(H) yake yi ma jagoranci da  ke  Katsina ya kai ziyarar bada agaji a asibitin masu fama da rashin lafiyar tabin hankali dake cikin birnin Katsina, a ranar Litinin 23/ 12/ 1431 albarkacin bukukuwan Idil gadeer.  

Shamsuddini Ahmad yana mika kyauta ga daya daga cikin masu kula da marasa lafiyar
 
 
Da yake gabatar da takaitaccen bayani bayan kammala wannan ziyara, Malam AbdulKarim Usamatu ,ya bayyana cewa, matashi shine fata da al'umma ke da ita, kuma wannan harka ta addini da Malam(H) ke yi ma jagoranci tana alfahari da matasa.Sai ya ce, wannan harka da Malam (H)yake yi ma jagoranci mune ake so mu yi dakon ta zuwa ga al'umma. Ya ce, idan matashi bai yi addini ba, to dole ne kuma ya yi wani abu daban wanda kuma ba addinin ba ne.sai ya shawarci matasan dasu tsayu akan al'amarin addini domin su bar kyakkyawan ambato ga masu zuwa nan gaba tare da samun kyakkyawan sakamako gobe kiyama. ya ja hankalin matasa dasu  gode ma Allah(T) da ya yi masu baiwa da fahimtar addini a irin wannan lokaci.
Ita dai wannan  ziyara 'yanuwan na dandalin matasa sun gabatar da ita ne karkashin jagorancin Shamsuddini Ahmad, 'yanuwa maza da mata ne suka rufa masa baya yayin gabatar da wannan ziyarar, inda kuma suka sami tarba daga Jami'an da ke kula da marasa lafiyar tare da nuna farincikinsu da kawo wannan ziyara.
Andai zagaya da su matasan inda suka ga yanayin marasa lafiyar gami da bayar da kyutuka garesu albarkacin wanna rana ta gadeer mai girma.
Yanuwa na dandalin matasa yayin da suka kai ziyara a asibitin masu fama da lalurar rashin hankali

Yanuwa na dandalin matasa tare da Jami'an asibitin a lokacin da suka kai ziyarar
Yanuwa mata na dandalin matasa a yayin ziyarar da suka kai a Asibiti marasa hankali da ke Katsina

No comments:

Post a Comment