Daga: AbdulAzizi
An bayyana aibin Ilmi da cewa shine rashin aiki da shi.Malam Bashir Kankia ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen bikin yaye dalibai mata na makartantar Fudiyyah katsina,da suka kammala karatunsu a matakin farko da aka gabatar a markazin ‘yanuwa dake katsina, a ranar Lahadi 29/ 12/ 1431.
Malam bashir Kankia, ya fadakar da ‘yanuwa gabadaya wajabcin dake da akwai na aiki da Ilimin da Allah (T) ya sanar da mutum, ya kuma tsoratar da ‘yanuwan akan rashin aiki da Ilimi, inda ya karanto kissar bil’am dan Ba’ura da Allah ya bayar a cikin Qur’ani mai tsarki, da kuma mummunan karshen da ya yi sakamakon take sanin da ya yi. Malam bashir ya ce,Ilimi yana da dadi kuma yana da hadari,kuma hadarinsa shine rashin aiki da shi. Sannan ya ce, “idan baka aikata abinda ka koya ba,to tabbas zaka manta da wannan abin da ka koya”, sannan yace, duk wanda ya yi aiki da abinda ya sani ,to Allah zaya gada masa ilimin abinda bai sani ba . sannan ya tabbatar da cewa,idan muka yi aiki da Ilmi, zaya haifar mana dab alkhairi Duniya da Lahira.Sai ya nemi ‘yanuwa da su roki Allah ya basu Ilimi da lafiya, lafiyar kuma itace aiki da Ilimin.
A karshe Malam bashir ya yi kira ga ‘yanuwa mazansu da matansu da su nuna ma ‘ya’yansu karatu da aiki da shi, ya ce, idan ba haka ba , suma yaran ba zasu yi aiki da karatu ba. Ya ce,’Annabawa da Imamai da sauran bayin Allah na kwarai, basu tara dukiya ba, domin su abin koyi ne, da dukiya suka tara da sun bar abin koyi. Sai ya karfafa da cewa, Maulanmu Malam Zakzaky(H) shi ma ba dukiya yake koyarda Tarawa ba, amma dai yana koyar da mu Ilimi ne,Sai ya yi kira ga dukkan ‘yanuwa da su riki Malam Abin koyinsu”mu ji tsoron Allah sai ya sanar damu”.
A tun farko da yake jawabin maraba, shugaban makarantar Malam Kabir Sani, ya dan gutsuro tarihin makarantar bangaren ‘yanuwa matan ,inda ya bayyana cewa, su dai ‘yanuwa matan sun fara wannan karatu tsawon shekaru,amma rashin jurewa ga halartar makarantar ya sa sai a wannan karo aka fara yaye su a matsayin karatu mai tsayayyen lokaci na shekara biyar a matakin farko. Sai ya yi kira ga iyaye da mazajen matan da su bayar da cikakken hadin kai domin cimma abin da aka sa a gaba.
Shi dai wannan biki na yaye dalibai bangarori uku ne aka shirya ma shi, bangaren karatun shekara biyar, sai kuma wani bangaren na sheka uku da Malam Yakubu Yahaya ya kaddamar domin bada horo ga ‘yanuwa mata da zasu iya koyarwa koda a mataki na kananan makarantu, gami da wa’azantarwa. Sanan sai bangaren yaran da suke a makarantun boko inda ake basu karatun addini su kuma sun sami kamala kartun al’qur’ani ne.
A karshen taro an bayar da takardun shedar kamala karatu a wadancan matakai guda biyu sannan daliban da suka yi saukar al’qur’ani suka karanto wasu sassa na surorin al’qur'anin, inda daga karshe aka bayar da kyututtuka ga bangarori daban-daban da suke bayar da gudunmuwarsu a ci gaban wannan karatu.
Bangaren daliban da suka sauke al'qur'ani mai girma a yayin bikin da aka shirya masu a Katsina
Daliban da suka kammala karatunsu na tsawon shekaru biyar a yayin da ake gabatar da walimar kammala karatun da aka shirya masu
Sashen yanuwanda suka kammala karatun su na shekaru uku a makarantar fudiyyah katsina a bikin da aka gabatar domin taya su murna
Wani bangare na 'yanuwa mata suna sauraren jawabin da aka gabatar a wajen walimar kammala karatunsu a Fudiyyah Katsina
No comments:
Post a Comment