Tuesday, December 7, 2010

DA'IRAR KATSINA TA FARA GABATAR DA ZAMAN MAKOKIN IMAM HUSAINI AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SHI


Daga: AbdulAzizi
A yau Talata ne 2 ga watan al-Muharram 1432, Da'irar 'yanuwa Musulmi almajiran Malam Zakzaky Allah Ya kiyaye shi  ta Katsina da kewaye ta fara gabatar da karatun juyayin Ashurar Imam Husaini aminci ya tabbata a gare shi.

A gabatarwar da ya yi, Malam Sabo ATC, ya bayyana cewa, Ita waki'ar Ashura ba al'amari bane wanda ya kebanci 'Yan Shi'a ba kadai, a a al'amari ne na Musulunci kacokaf. Ya karanto wasu daga cikin Hadisan da aka ruwaito daga  cikin litattafan  ahluss Sunnati, ruwayoyin da aka karbo su daga Manyan Sahabban Manzon Allah.

Ya karanto ruwayoyin da suka yi bayanin kisan da za a yi wa Imam Husaini din tun Annabi tsira da amincin Allah su tabbata gare shi yana raye, inda suka nuna Manzon Allah ya yi kuka, kuma Sahabbansa sun taya shi wannan kuka na kisan da makiyansa daga cikin wannan al'umma tasa zasu yi akan wannan jika nasa mai daraja.

Ga wasu daga cikin hotunan wannan zama na makoki nan da aka dauka a wannan rana ta farko.
Harisawa suna sauraen karatu a zaman makokin da aka fara gabatarwa a Katsina
'Yanuwa maza suna sauraren karatun daga Malam Sabo ATC a ranar farko ta ta'aziyyar  kisan Imam Husaini
Wani sashe na 'yanuwa mata a lokacin gabatar da karatun Ashura a Katsina

'Yanuwa na sashen kiwon lafiya a wajen karatun Ashurar Imam Husaini a Katsina

No comments:

Post a Comment