Daga: AbdulAzizi
MANUFAR BUDE WANNAN DANDALI NA MEDIAFORUM KATSINA, SHINE YADA HARKOKIN KIRAN DA MAULANA SAYYID IBRAHIM ZAKZAKY(H)YAKE YI NE.TARE DA KAWO LABARAN ABUBUWAN DA KE FARUWA NA WANNAN HARKAR TA MUSULUNCI A WANNAN YANKI NA KATSINA DAMA WASU YANKUNA, NA YUNKURIN WAYAR MA AL'UMMA KAI DANGANE DA AL'AMARIN MUSULUNCI, MUSAMMAN ABINDA YA SHAFI KOYARWAR AHLUL-BAITIN MANZON ALLAH(AS).
Saturday, February 18, 2012
YADDA AKA GABATAR DA TARON KARA MA JUNA SANI NA 'YANUWA 'YAN KASUWA A KATSINA
Kadan daga cikin hotunan da aka dauka yayin gabatar da taron karama juna sani na kwana biyu da 'yanuwa 'yankasuwa suka shirya a katsina, kwanakin baya.
Daga: AbdulAzizi
Daga: AbdulAzizi
Saturday, February 11, 2012
A CI GABA DA BUKUKUWAN MAULUDIN MANZON ALLAH, AN GABATAR DA FARETI A KATSINA
Akaro na biyu, Lajnar Islamiyyu ta harkar musulunci dake da’irar Katsina da kewaye, ta kaddamar da gasar farertin girmamawa ga Manzon Allah (S) na wannan shekara a ranar Assabat 19/3/1433, a Unguwar filin samji dake Katsina.
Makarantun islamiyyu, daga sassa daban-daban ne suka halarci wannan gasa, cikin makarantun da suka shiga wannan gasa, akwai Fudiyyoyin, Batagarawa,Magamar Jibiya,Rimi Abukur, Bindawa,sai Islamiyyu irinsu Baharul’Fatimiyya,Shabbabul’Mahadi,Tarbiyyatul’islam da sauransu,inda kowace makaranta ta fito ta gabatar da irin shirin da take da shi da zaya kayatar da faretin.
A jawabin da ya gabatar bayan Kammala wannan gasa, Malam Yakubu Yahaya Wakilin ‘yanuwa na Katsina, ya Godema daliban Makarantun ,malamansu tare da wadanda suka koyar da su irin wannan Fareti . Malam Yakubu ya bayyana cewa, irin duk abinda mutum zaya gabatar da zaya nuna murna ga samuwar Manzon Allah , to halal ne matukar ba ya sabama koyarwar Musulunci ba ne.Ya ce, ga masu ganin an zurfafa ga son Manzon Allah kuwa, “sai su nuna mana iyakar darajar Annasbi, mu kuma mutsaya a nan”.Daga nan sai ya kirayi iyaye da su kula sosai akan tarbiyyar ‘ya’yansu, musamman a wannan lokaci da makiya suke kirkiro da wasu hanyoyi na lalata tarbiyyar ‘ya’yan musulmi. Ga wadanda ‘ya’yansu suke da wayoyi kuwa ,ya kiraye su da su rika kulawa da irin abubuwan da suke cikin wayoyin yaran nasu don sanin halinda suke a ciki, sai ya ce mafita daga irin wannan tarko shine kusantar Allah (T) da ibadu tare da aza yaran bisa tsayuwa da ibadun,Ya yi nuni da cewa ,kada kaga yaranka yana karatu,wannan bai isa ba sai an kula da irin abokan da suke tare da su.
Ita dai wannan gasa ta fareti a tabakin Malam Yakubu Idris wanda shine shugaban Lajnar ta Islamiyyu, cewa ya yi, an shirya wannan gasa ce, domin girmamawa ga Manzon Allah(S) kuma wannan sababben abu ne cewa, idan wani wanda ake girmamawa ya kai ziyara a wasu kasashe, to ana shirya masa fareti, saboda haka wannan Lajna ta tsara gabatar da shi domin girmama Manzon Allah(S).
Makarantunn da suka samu nasara a wannan gasa ta bana, sune, Fudiyya Batagarawa a matsayin ta hudu, Baharul Fatimiyya ta uku, Fudiyyah Rimi ta biyu sai Tarbiyyatul Islam Marnar Kadabo matsayin wadda tazo zakara watau ta daya.
Ashekarar da ta gabata ne dai aka fara gabatar da irin wannan gasa a cikin tsare-tsaren bukukuwan Mauludi. An dai kamala gasar cikin nasara da farin ciki daga al’ummar da suka sami halarta.
Saturday, January 21, 2012
DANDALIN MATASA NA YANKIN KANO YA ZIYARCI NA KATSINA
A ranar Laraba ne 25/ n2/ 1433 A.H,tawagar ‘yanuwa na Dandalin matasa na yankin Kano, suka kawo ziyara ga takwarorinsu da ke Katsina domin sada zumunci tare da gabatar da jawabai na karfafa juna.
A jawabin da ya gabatar , shugaban dandalin na matasan harkar musulunci a karkashin jagorancin Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) Malam Hafizu Dauda Kano, ya ankarar da ‘yanuwa matasa na gwagwarmaya akan manufar wannan ziyara , inda yace,domi sada zumunci ne da tattauna yadda za a iya haduwa a karfafa juna , sai ya ce, akwai bukatar kowanensu ya kula da kansa ta hanyar siffatuwa da kyawawan dabi’u, ganin cewa a yanzu akwai gurbacewar tarbiyya. Ya kuma ya karfafi ‘yan dandalin da suci gaba da nemo malaman harka, ko masana su rika yi masu bayani akan wasu bangarori na harka, ya kuma yi kira ga Malaman harkar nan da kara sa kula su fahinci matsalolin matasan domin a shigowa da magancce su.
A wani sashen jawabin , Malam Hafizu ya tunanatar da ‘yanuwan cewa,Sayyid (H) ya bayyana matasa a maatsayin jari na wannan harka,sai ya nuna wajabcin siffantuwa da kyawawan ayyuka kamar yadda Sayyid din yake koyarwa, sannan ya bukaci matasan su kauce ma munanan ayyuka da za su jawo suka ga wannan kira da Sayyid din ke ma jagoranci. ya kuma bukaci matasa su kara kulawa da al’amurran harka ta hanyar nazartar tarihinn kiran, yaddad harkar ta taso da irin sadaukarwar da magabatanta suka yi domin samun damar tsayuwa akan ta.Sai yayi kira akan dagewa da ibada ta hanyar azumomi da sallolin na da makamantansu. A karshen jawabin nasa, ya bukaci kowane matashi ya zamo yana da wata gudunmuwa da yake bayarwa a wannan harka domin ta ci gaba.
A nasa jawabin, danuwa Sanusi Idris Musa, jawo hankalin matasa ya yi ta hanyar nuna takaicin yadda suke wahalar da maluman harka ta yin watsi da shiryarwar da suke yi a kodayaushe, sai ya bukaci matasan su sa tunani tare da nazartar maganganun Maluman, da kuma yin aiki da su.Ya ce koda kashi Hamsin cikin Dari na maganganunsu aka yi aiki da su, to da an ga sauyi a rayuwar matasan. Ya shawarci matasan da cewa, kowanensu ya duba ya ga inda yake da gajiyawa ya yi aiki domin gyara matsalarsa saboda ana yin wannan harka ne domin neman yardar Allah(T).
Malama Fatima Yusuf Ali , daya daga cikin wadanda suka kawo ziyarar daga Kano, ta bukaci ‘yanuwa maza da mata da su himmatu akan neman sanin ilmomi tare da sanin ilimin computer da harkar internet domin yada da’awar Malam (H),ta kuma jawo hankali akan dagewa dai da mujahada domin iya tunkarar halin da ake ciki a yanzu haka.
A jawabin godiya da ya gabatar, Shamsuddin Ahmad a madadin ‘yan dandalin na yankin Katsina, ya nuna godiya ga , maziyartan da wannan ziyara da suka kawo masu , ya kuma yi fatan su ‘yan kwamitin za su yi amfani da duk abubuwan da suka ji a wannan zama.
An kammala wannan ziyara cikin nasara, kuma tuni bakin suka isa gida lafiya.
Tuesday, December 6, 2011
AN GABATAR DA MUZAHARAR JUYAYIN ASHURA TA SHEKARAR 1433 A KATSINA
A wannan rana ce ta Talata 11 / 1/ 1433, ‘yanuwa musulmi almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) a karkashin jagorancin Malam Yakubu Yahaya Katsina kamar sauran takwarorinsu na duniya, suka gabatar da Muzaharar juyayi da nuna bakin ciki akan kisan da Yazidawa makiya zuriyar Manzon Allah suka yi ma Imam Husaini Dan Ali dan Abi Dalib Dan Fatima diyar Manzon Allah (S) da zuriyarsa tare da abokansa a filin karbala.
A jawabin da ya gabatar bayan kamala wannan gagarumar muzahara, Malam Yakubu Yahaya wakilin ‘yanuwa na garin Katsina, ya bayyana cewa, manufar wannan jerin gwano shine jajantawa tare mika ta’aziyya ga Manzon Allah(S), Imamul Asr(AJ), Sayyi Ali Khaminei da Sayyid Zakzaky(H) da sauran bayin Allah.Ya ce , mika wannan ta’aziyya duk duniya ne ake yi ba nan kawai bane kamar yadda wasu suke dauka, ya ce , zaman makoki da irin wannan muzahara duk ta’aziyya ce zuwa ga Manzon Allah, domin shine wanda aka cutar, kuma wannan ya faru tun bayan wafatinsa.ya kara da cewa, bayan wannan ta’addanci ,an tafi da zuriyar Manzon Allah mata da kananan yara da suka yi saura daga filin Karbala zuwa Sham fadar Yazidu dan Mu’awiyya (LA) a kasa ana tafe ana tozarta su a duk garin da aka wuce ta cikinsa. ya ce, sakamakon wannan ta’addanci ne Allah ya sallada ma musulmi Kaskanta a hannun Magolawa kafiarai abin da ya tafo har wannan zamani da musulmi suke cikin kaskancin Kafiran duniya.
Sannan ya ce, lokacin dawowar musulmi akan lamarinsu na addini ya yi,domin addinin ne zaya hada su waje daya. Sai ya ce, dole ne abinda ya dami Manzo ya dame ka, kuma dole ne ranar bakin cikinsa kaima ta zama rana ce ta bakin cikinka idan dai har Manzon kake bi kai ba munafuki bane ba kai
.
Malam Yakubu ya nasihanci masu sukar abinda muke yi da ganin ba daidai bane, da su binciki littattafansu indai har da gaske suke yi ba munafunci bane.Ya kara da cewa, Allah ya kawo lokacin da za’a gane abinda aka yi ma wadannan bayin Allah, kuma ko bamu nan ga ‘ya’yanmu nan zasu ci gaba da wannan al’amari.”Ya nasihanci malamai da su ji tsoron Allah, su tsaya ma gaskiya domin jama’a suna kallonsu, ya ce “wannan lamari na Shi’a yazo zama ne”.
Ya kuma ja kunnuwan mahukunta dake hankoron hanawa ko afkama wannan lamari da cewa,”wannan Shi’a din ita ce ajalin gwamnatin wannan kasa, sai ya gargade su da cewa”su ja bakinsu su tsuke, su sama wannan al’amarin ido, “idan kuma kuka ce ba haka ba, za ku yi rigima ne da al’umma, domin al’umma adalci take so kuma a addini ne ake samunsa, ya kuma ce,” babu wanda zaya fahimci wannan gida na Annabi, sannan ya rabu da shi . “idan ba za ku zo ayi da ku ba, kusa ido.Kawo jami’an tsaro da kuke kokarin yi kuma ku yi ta kawowa, kuna amfani da zahirine shi kuma Allah yana amfani ne da zukata.
Ya kare da cewa, da Imamu Husaini bai tashi ba da yanzu ba addini ne ake yi ba , domin su Umayyawa sun shirya maido da Jahiliyyar da Manzon Allah ya kawar ne, mikewar Imam it ace ta tsaida su.
Ita dai wannan muzahara, dubunbubatar ‘yanuwane maza da mata da kananan yara suka gabatar da ita a cikin yanayi na juyayi da nuna bakin cikin abinda aka yi ma zuriyar Manzon Allah bayan rasuwarsa.
Friday, December 2, 2011
DA'IRAR 'YANUWA MUSULMI TA KATSINA TA FARA GABATAR DA KARATUN JUYAYIN ASHURA NA SHEKARAR 1433 A.H
A ranar Assabat 1/1/1433 ne, Da’iarar ‘yanuwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky(H) ta Katsina karkashin jagorancin Malam YakubuYahaya ta fara zaman makokin domin jajanta ma Manzon Allah (S) akan kisan da makiya suka yi ma jikokinsa a Karbala.
A gabatarwar da ya yi kafin fara karatun, Malam Yakubu ya ce, manufar wannan zama na makoki shine jajanta ma Manzon Allah(S), A’imma(AS) dasauran bayin Allah managarta akan zagayowar wannan musiba domin dole ne son Iyalan Manzon Allah saboda irin al’khairan da ya zo ma al’umma da shi”dole ne ka nuna farin cikinka akan duk abinda ya faranta ma Manzo da Iyalansa, haka kuma, wajibi ne nuna bakin ciki kan duk abinda ya bakanta masu” sai ya bukaci jama’a da basu fahimci abin da muke yi ba su bamu uzuri domin muna sauke wajibin da ya hau kanmu ne.”Malam Yakubu ya yi nuni da cewa,”zamu bi salon da muka saba bi ne na karanta littafan magabata domin sauran jama’a da zasu saurara suma su amfana” sannan ya ce,dukkan abinda ya faru a wannan waki’a, ba kire bane ba kuma kage, sai dai muna karantawa ne daga littafai da aka rubuta su tsawon shekaru kuma a mabambantan garuruwa da zamunna domin mu amfana da tarihi, don yin aiki da kyawawan dabi’u da watsi da munana.”
Malam Yakubu ya tabo tarihin gasar dake tsakanin Kuraishu da Hashimawa da yadda Hashimawa suka yi fice, abin da ya sa sauran Kabilun suka nuna masu gaba da kiyayya musamman wadda Umayyawa suka nuna abinda ya tafo har zuwan musulunci sannan bayan yakokin da Manzon Allah ya jagoranta wanda Imam Ali(AS) ya kashe mayan kafiran Kuraishu, sai gabar ta karu tsakainsu da Zuriyar Annabi abinda ya yi sanadiyyar kisan gillar da Yazidu (L) ya yi ma Imam Husain(AS) da zuriyarsa da magoya bayansa a Karbala domin ya dauki fansa.
Kafin nan,sai da Malam Yakubu ya karanto tarihin da ke nuni da cewa, asalin Abdussamshi wanda ya haifi Umayyam, mutumen Rum ne da aka kamo sa a matsayin bawa daga bisani aka mayar da shi da -ta hanyar Tabanni-
sannan shi kuma Mu’awiyya ba dan Abu Sufyanu ba ne na hakika sai dai da ne ga wani da ake ce ma Musafiru wanda ya samar da cikinsa ta hanyar nema dake tsakaninsa da Hindu,wadda abu sufyanu ya aure ta bayan samun cikinsa.
Sanna ya bukaci jama’a su binciki tarihidomin sanin gaskiyar abinda ya faru tare da sanin asalin gabar su Abu-Sufyanu da Zuriyar Manzon Allah(AS).
Ya yi fatan za a kamala wannan zama tare da fatan wannan jaje ya zama karbabbe gami da fatan tabbata a wannan harka ta Musulunci.
Subscribe to:
Posts (Atom)


