A ranar Assabat 1/1/1433 ne, Da’iarar ‘yanuwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky(H) ta Katsina karkashin jagorancin Malam YakubuYahaya ta fara zaman makokin domin jajanta ma Manzon Allah (S) akan kisan da makiya suka yi ma jikokinsa a Karbala.
A gabatarwar da ya yi kafin fara karatun, Malam Yakubu ya ce, manufar wannan zama na makoki shine jajanta ma Manzon Allah(S), A’imma(AS) dasauran bayin Allah managarta akan zagayowar wannan musiba domin dole ne son Iyalan Manzon Allah saboda irin al’khairan da ya zo ma al’umma da shi”dole ne ka nuna farin cikinka akan duk abinda ya faranta ma Manzo da Iyalansa, haka kuma, wajibi ne nuna bakin ciki kan duk abinda ya bakanta masu” sai ya bukaci jama’a da basu fahimci abin da muke yi ba su bamu uzuri domin muna sauke wajibin da ya hau kanmu ne.”Malam Yakubu ya yi nuni da cewa,”zamu bi salon da muka saba bi ne na karanta littafan magabata domin sauran jama’a da zasu saurara suma su amfana” sannan ya ce,dukkan abinda ya faru a wannan waki’a, ba kire bane ba kuma kage, sai dai muna karantawa ne daga littafai da aka rubuta su tsawon shekaru kuma a mabambantan garuruwa da zamunna domin mu amfana da tarihi, don yin aiki da kyawawan dabi’u da watsi da munana.”
Malam Yakubu ya tabo tarihin gasar dake tsakanin Kuraishu da Hashimawa da yadda Hashimawa suka yi fice, abin da ya sa sauran Kabilun suka nuna masu gaba da kiyayya musamman wadda Umayyawa suka nuna abinda ya tafo har zuwan musulunci sannan bayan yakokin da Manzon Allah ya jagoranta wanda Imam Ali(AS) ya kashe mayan kafiran Kuraishu, sai gabar ta karu tsakainsu da Zuriyar Annabi abinda ya yi sanadiyyar kisan gillar da Yazidu (L) ya yi ma Imam Husain(AS) da zuriyarsa da magoya bayansa a Karbala domin ya dauki fansa.
Kafin nan,sai da Malam Yakubu ya karanto tarihin da ke nuni da cewa, asalin Abdussamshi wanda ya haifi Umayyam, mutumen Rum ne da aka kamo sa a matsayin bawa daga bisani aka mayar da shi da -ta hanyar Tabanni-
sannan shi kuma Mu’awiyya ba dan Abu Sufyanu ba ne na hakika sai dai da ne ga wani da ake ce ma Musafiru wanda ya samar da cikinsa ta hanyar nema dake tsakaninsa da Hindu,wadda abu sufyanu ya aure ta bayan samun cikinsa.
Sanna ya bukaci jama’a su binciki tarihidomin sanin gaskiyar abinda ya faru tare da sanin asalin gabar su Abu-Sufyanu da Zuriyar Manzon Allah(AS).
Ya yi fatan za a kamala wannan zama tare da fatan wannan jaje ya zama karbabbe gami da fatan tabbata a wannan harka ta Musulunci.
No comments:
Post a Comment