A wannan rana ce ta Talata 11 / 1/ 1433, ‘yanuwa musulmi almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) a karkashin jagorancin Malam Yakubu Yahaya Katsina kamar sauran takwarorinsu na duniya, suka gabatar da Muzaharar juyayi da nuna bakin ciki akan kisan da Yazidawa makiya zuriyar Manzon Allah suka yi ma Imam Husaini Dan Ali dan Abi Dalib Dan Fatima diyar Manzon Allah (S) da zuriyarsa tare da abokansa a filin karbala.
A jawabin da ya gabatar bayan kamala wannan gagarumar muzahara, Malam Yakubu Yahaya wakilin ‘yanuwa na garin Katsina, ya bayyana cewa, manufar wannan jerin gwano shine jajantawa tare mika ta’aziyya ga Manzon Allah(S), Imamul Asr(AJ), Sayyi Ali Khaminei da Sayyid Zakzaky(H) da sauran bayin Allah.Ya ce , mika wannan ta’aziyya duk duniya ne ake yi ba nan kawai bane kamar yadda wasu suke dauka, ya ce , zaman makoki da irin wannan muzahara duk ta’aziyya ce zuwa ga Manzon Allah, domin shine wanda aka cutar, kuma wannan ya faru tun bayan wafatinsa.ya kara da cewa, bayan wannan ta’addanci ,an tafi da zuriyar Manzon Allah mata da kananan yara da suka yi saura daga filin Karbala zuwa Sham fadar Yazidu dan Mu’awiyya (LA) a kasa ana tafe ana tozarta su a duk garin da aka wuce ta cikinsa. ya ce, sakamakon wannan ta’addanci ne Allah ya sallada ma musulmi Kaskanta a hannun Magolawa kafiarai abin da ya tafo har wannan zamani da musulmi suke cikin kaskancin Kafiran duniya.
Sannan ya ce, lokacin dawowar musulmi akan lamarinsu na addini ya yi,domin addinin ne zaya hada su waje daya. Sai ya ce, dole ne abinda ya dami Manzo ya dame ka, kuma dole ne ranar bakin cikinsa kaima ta zama rana ce ta bakin cikinka idan dai har Manzon kake bi kai ba munafuki bane ba kai
.
Malam Yakubu ya nasihanci masu sukar abinda muke yi da ganin ba daidai bane, da su binciki littattafansu indai har da gaske suke yi ba munafunci bane.Ya kara da cewa, Allah ya kawo lokacin da za’a gane abinda aka yi ma wadannan bayin Allah, kuma ko bamu nan ga ‘ya’yanmu nan zasu ci gaba da wannan al’amari.”Ya nasihanci malamai da su ji tsoron Allah, su tsaya ma gaskiya domin jama’a suna kallonsu, ya ce “wannan lamari na Shi’a yazo zama ne”.
Ya kuma ja kunnuwan mahukunta dake hankoron hanawa ko afkama wannan lamari da cewa,”wannan Shi’a din ita ce ajalin gwamnatin wannan kasa, sai ya gargade su da cewa”su ja bakinsu su tsuke, su sama wannan al’amarin ido, “idan kuma kuka ce ba haka ba, za ku yi rigima ne da al’umma, domin al’umma adalci take so kuma a addini ne ake samunsa, ya kuma ce,” babu wanda zaya fahimci wannan gida na Annabi, sannan ya rabu da shi . “idan ba za ku zo ayi da ku ba, kusa ido.Kawo jami’an tsaro da kuke kokarin yi kuma ku yi ta kawowa, kuna amfani da zahirine shi kuma Allah yana amfani ne da zukata.
Ya kare da cewa, da Imamu Husaini bai tashi ba da yanzu ba addini ne ake yi ba , domin su Umayyawa sun shirya maido da Jahiliyyar da Manzon Allah ya kawar ne, mikewar Imam it ace ta tsaida su.
Ita dai wannan muzahara, dubunbubatar ‘yanuwane maza da mata da kananan yara suka gabatar da ita a cikin yanayi na juyayi da nuna bakin cikin abinda aka yi ma zuriyar Manzon Allah bayan rasuwarsa.
No comments:
Post a Comment