MANUFAR BUDE WANNAN DANDALI NA MEDIAFORUM KATSINA, SHINE YADA HARKOKIN KIRAN DA MAULANA SAYYID IBRAHIM ZAKZAKY(H)YAKE YI NE.TARE DA KAWO LABARAN ABUBUWAN DA KE FARUWA NA WANNAN HARKAR TA MUSULUNCI A WANNAN YANKI NA KATSINA DAMA WASU YANKUNA, NA YUNKURIN WAYAR MA AL'UMMA KAI DANGANE DA AL'AMARIN MUSULUNCI, MUSAMMAN ABINDA YA SHAFI KOYARWAR AHLUL-BAITIN MANZON ALLAH(AS).
Sunday, February 6, 2011
MAULIDIN YANKIN RASULUL AKRAM
A ci gaba da raya al’amarin mauludin Manzon Allah(S) da harkar musulunci karkashin jagorancin Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) ta shirya take gabatarwa a fadin wannan kasa,Yankin Rasulul akram zone(A) na da’irar yanuwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky(H) ta Katsina ya shirya taron wannan mauludi na Manzo a ranar Litinin 27/2/1432 a Unguwar Filin Fayis dake cikin garin Katsina.
Da yake gabatar da wa’azi a wajen , wakilin ‘yanuwa musulmi almajiran Sayyid (H) na Katsina, Malam Yakubu Yahaya, ya tunatar da al’umma ne akan wajabcin kulawa da Ruhi da Allah (T) ya halitta sannan ya saka shi a gangar jikin Dan Adam. Malam Yakubu ya bayyana cewa,Jama’a da dama a halin yanzu sun jahili muhimmancin Ruhi, sai suka koma suna hidimar gangar jiki,abin mamaki kuma har da Malamai. Wannan ya sa Malaman suka koma suna bin jahilai masu mulki bisa tsarin da ya saba ma na Allah(T). Ya ci gaba da cewa,”Annabawa ba su zo duniya domin biyan bukatun gangar jiki ba, shi yasa ma suka rayu ba tare da abin duniya ya dame su ba, sai dai suna amfani da abin duniya ne gwargwadon bukata, kuma wannan shi ne abinda mutane suka jahilta.” in ji shi.
Malam Yakubu ya ce,” bayin Allah wadanda suka dandani sirrin sanin Allah suke jin dadin bautar Allah domin Ruhi bautar Allah ita ce abincinsa”. “Ruhin dan Adam yana tunanin hutawa ne, amma hutawa marar iyaka ba a samunta a wannan duniya”Madamar mutum bai fahinci abinda ya kawo shi duniya ba zai yi nadama a lokain da ya mutu. Inda ya karfafa wannan batu da Hadisin Manzo da ya nuna cewa, “mutane suna barci ne sai sun mutu sai su farka”. “a gaskiya mutum shi ne Ruhinan wanda ba a ga ni, kuma Ruhi shine abinda Annanbawa suka damu da shi “
Malam Yakubu ya kara da cewa, yunkurin Annabawa na tsarkake Ruhin Mutane ya jawo masu rigima da mahukuntan lokacinsu, Abinda ya jawo rigima ken an tsakanin Shehu dan Fodiyo da sarakunan Hausa domin yana kokarin tsarkake Ruhi da maida mutane zuwa ga Allah, su kuma Sarakunan suna hanawa. Sai ya yi mamakin yadda Malamai ahlussunna a nan suke karanta al’Qu’ani , amma suna mika mutane zuwa ga Azzalumai.Malam Yakubu ya karkare da cewa, da muyi abinda babu Allah, gara muyi na Allah komin nisan dadewa ko wahala.
Ya yi fatan samun taimakon Allah domin samun tsira duniya da L:ahira
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment