Monday, February 7, 2011

YANKIN AMINA UMMUR'RASUL NA BANGAREN 'YANUWA MATA YA GABATAR DA MAULIDIN MANZON ALLAH(S)


“Musulunci ne ya kawo juyinjuya hali  na tunani dangane da daidaita maza da mata.” Malam yakubu Yahaya  ya bayyana haka a lokacin gabatar jawabi a wurin taron Maulidi  Annabi (S) da yanuwa mata na yankin Amina Ummur Rasul(zone A) na Katsina suka shirya.
Malam yakubu ya yi nuni da cewa,mata basu da hakki a lokacin jahiliyyar Larabawa sannan basu da wani amfani a wajensu, sai dai biyan bukatar rayuwa,shi ya sa ma suka aibata manzo da cewa, ya kawo daidaito tsakanin mazan da mata,saboda su basu dauki matan da wata kima ba.wannan kuma ya sa suke ganin ya yi masu laifi, abinda ya sa suka ki yin Imani da shi.ya kara da cewa, da namiji da mace, darajarsu guda a wajen Allah(T) . jingina su da  Musulunci  ya yi ga maza, ba gazawa ba ne gare su, sai dai kowane bangare akwai aikin da aka hore masa. Ya ce, kasantuwar mata suna tsayuwa da ayyukan gida, taimakon juna ne domin shi namiji shi ne ke tsayuwa da hidindumun waje. Sai ya ce,”a gwagwarmayar neman duniya, babu yadda za a yi mace ta yi gogayya da namiji,amma a gwagwarmaya neman Addini da Ilimi,mace na iya wuce namiji domin zuciya da kwakwalwa iri daya Allah ya yi masu.”
Da yake fadakar da masu mamakin yin addini tare da mata, cewa  ya yi, jama’a sun yarda siyasa a yi tare da mata amma Addini banda su, ya kara da cewa,akai bukatar mace ta yi addini, domin babu wanda zaya so mahaifiyarsa ta sha bugu a kabari Kakarsa ko matarsa da suka yi zaman mutunci.” Babu yadda za a yi a kauce ma wannan bugu sai idan an yi addini”
A wani bangare na jawabin ,Malam Yakubu ya bayyana cewa,”Manzon Rahama ya ’yanta mata, kuma ya suturta su,inda ya wajabta masu saka Hijabi” hijabi  da Sallah ga mace matsayinsu daya saboda Mala’ika Jibrilu ne ya zo da ayar Sallah da hijabi, ba Hadisi bane balle kace rarrauna ne” ya ce, “idan har zaka hana matarka ko diyarka ko kuma kanwarka sa hijabi, to gara ma ka hana ta yin Sallah domin wanda ya ce ayi Sallar shi ne kuma yace su sa hijabin, kuma cewa su sa hijabin karramasu aka yi sabanin yadda Turawa suke yekuwar cewa an takura masu”
A karshen taron ,an rarraba kyautuka ga bangarori da dama da suka hada da wata dattijiyar yaruwa, marayu,'yayan Shahidai da wasu mata masu Suna irin na mahaifiyar Manzon Allah (S) da sauransu.
 

No comments:

Post a Comment