MANUFAR BUDE WANNAN DANDALI NA MEDIAFORUM KATSINA, SHINE YADA HARKOKIN KIRAN DA MAULANA SAYYID IBRAHIM ZAKZAKY(H)YAKE YI NE.TARE DA KAWO LABARAN ABUBUWAN DA KE FARUWA NA WANNAN HARKAR TA MUSULUNCI A WANNAN YANKI NA KATSINA DAMA WASU YANKUNA, NA YUNKURIN WAYAR MA AL'UMMA KAI DANGANE DA AL'AMARIN MUSULUNCI, MUSAMMAN ABINDA YA SHAFI KOYARWAR AHLUL-BAITIN MANZON ALLAH(AS).
Monday, January 31, 2011
BA A ZABI MUSULMI BA NE MAFITA SAI DAI KOMA MA BIN TSARIN MUSULUNCI
An bayyana cewa ba a tallar gaskiya ta hanyar yin amfani da barna,amma dai ana tallar gaskiya ne da gaskiya.Malam Yakubu Yahaya ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da wa’azin mauludin Annabi (SAW) da yankin zone © suka shirya aka gabatar a Tudun Matawalle Sabuwar Unguwa Katsina.
Malam yakubu ya ci gaba da bayyana cewa, ta hanyar da Manzon Allah ya shata ne kawai zaka iya kawo Addini bata hanyar a zabi Musulmi da wasu Malamai suke ta yekuwa ba.ya ce, “ai Manzon Allah an yi masa tayi na shiga tsarin gwamnatin Kuraishu,amma bai shiga ba.”da ta haka ake taimakon Addini, da Manzon ya karba wannan tayi” ya gargadi musulmin kasar nan da su yi hattara da wutar rikici tsakanin musulmi da kafirai da ake yayatawa a halin yanzu ta hanyar cewa, a zabi musulmi ba kafiri ba, domin dai duk tsarin ba musulunci bane. Ya ce, kuma ko an yi rigima tsakanin musulmi da kafirai a kasar nan, to babu wata nasara da musulmin za su samu domin Allah baya taimakon komi sai gaskiya. Kuma wani makirci ne ake kitsawa da nufin bada dama kafiran duniya su kafa sansaninsu a wannan yanki na musulmi da niyyar kwasar arzikin da Allah ya aje shimfide a bayan wannan kasa” wannan tarko ne da aka dana ma musulmin wannan kasa, matukar basu koma ma addini ba akwai matsala”
Malam yakubu ya karyata masu cewa yin rajista da zaben musulmi a wannan tsarin Jihadi ne.ya ce , “idan kuwa jihadi ne, to da Manzon Allah da Sahabbansa duk kuskure suka yi kenan ,Waliyazu bil’Lahi” Sannan yace,”kifar da gwamnatin zalunci da mayar da tsarinta na Addini shjine mafita ba rudanin a zabi musulmi ba.”
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment