Thursday, February 24, 2011

ISMA TA KAI ZIYARA GIDAN KURKUKU

A ci gaba da gabatar da bukukuwan maulidin Manzon Allah da ‘yanuwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky(H) suke gabatarwa a fadin wannan nahiya, ‘yanuwa mata na sashen kiwon lafiya(ISMA) dake Katsina sun gabatar da wata ziyara a gidan kurkukun garin Katsina a ranar Alhamis 21/ 3/ 1432.




A lokacin da suke ganawa da tsararrun, ‘yanuwan sun gabatar masu da nasiha gami da tausaya masu akan wannan hali da suka sami kansu.Malama Hajara wadda ta yi Magana a madadin ‘yanuwan ta bayyana wannan ziyara da cewa, sun kawo ta ne sakamakon shiryarwar Sayyid Zakzaky(H) da ya ke yi ma ‘yanuwa na su maida hankali wajen gabatar da ayyuka na taimaka ma al’umma,sannan ta bukaci ‘wadanda suke tsaren da su sa tsoron Allah a cikin al’amarin rayuwarsu. Ta nuna takaicin ganin yadda wadannan matan suke tsare kasantuwarsu iyayen al’umma, amma wani yanayi ya sa sun sami kansu a wannan wuri.Sai ta bukaci su dauki darasi am wannan zama da suka yi, ta hanyar kyautata halayyarsu tare da sauran jama’a da suke rayuwa da su kuma ta bukace su da su kara hakuri da al’amarin rayuwa da kuma fatan ba zasu sake komowa a wannan wuri ba.

Itama ‘yaruwa Mariya Zakariyya kira ta yi garesu da su guji aikata duk wani hali da zaya sa su sami kansu a wannan gida, ta ce abin bakin ciki ne ace matan suna tsare a wannan wuri, sakamakon aikata wani abu da bai dace ba.sai ta yi fatan zasu yi amfani da wannan wuri wajen gabatar da Istigfari da bauta da addu’o’in neman tsari da sake kawosu dama sauran mata wannan gida tare da fatan zasu koma gidajensu domin ci gaba da gabatar da abinda ya kamace su kasancewar su iyaye.

Wanda ya karbi yanuwan a madadin shugaban gidan yarin, Muhammad Bello, ya nuna matukar godiya da farin ciki akan wannan ziyara, kuma ya yi fatan Allah ya taimaka .

Ita dai wannan ziyara, an kai ta ne a bangaren mata da suke tsare a wannan gidan yari da ke cikin birnin Katsina.

No comments:

Post a Comment