‘Yan uwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky(H) na da’irar Katsina da kewaye sun gabatar daMuzaharar Murnar zagayowar Wata da ranar da aka haifi Fiyayyen halitta( a wata ruwaya) Manzon Rahama Muhammad (S) a ranar Talata12/ 3/1432.
Da yake bada amsoshin tambayoyin manema labari bayan kammal wanna gagarumar muzahra, Malam Yakubu Yahaya Katsina, ya bayyana cewa, sakon Maulidin wannan shekara ya na albishir ne ga al’ummar musulmi.Inda yace, wanda yake da dimbin magoya baya kamar Manzon Allah (S), to shine ya kamata ya shige ma mutane gaba. Ya nuna cewa,lokaci ya yi da za a dawo abi bayan Manzon, ya kara da cewa,idan har mutane suna ganin mafita a wani tsari ba na Manzon ba,to shi tsarin ya karye, domin yanzu abin da ake ga ni a tsarin duniya wanda kuma ake tutiya da takama da shi tun farkon karnin da ya gabata ya fara karyewa ya kuma fara cin tura. Ya ce yanzu ya zama lazim komawa tushe musamman ma ga al’ummar musulmi.
Ya kuma bayyana cewa,rashin riko da addini da musulmi suke yi ne ya sa wadanda ba musulmi ba su ke yin nesa-nesa da musulunci, duk kuwa da sha’awar da suke yi da addinin sannan ya ce,da musulmi za su lazimci riko da addinin, da Allah(T) za ya karkato da zukatan sauran mutane zuwa ga son addinin wanda kuma dama hakki ne akan su musulmin domin kusan wanda ya fandare wanda ba musulmi ba, to alhakin sa yana bi sa wuyan musulmi ne, saboda Allah ya nuna cewa,idan musulmi basu dunkulu waje daya ba, za a sami babbar fitina a bayan kasa.Aikin musulmi ne su hadu bayan Manzon Allah domin su kawo karshen fitinun da matsalolin da duniya take fama da su.
Ya bayyana yadda aka samu ci gaba ta fuskacin kawata wannan mauludi na bana duk kuwa da bambance-bambancen dake tsakaninn al’umma a fahimta da cewa, abin sha’awa ne, domin haduwa wajen gudanar da irin wannan taro na Muzahara domin nuna murna da zagayowar wannan lokaci, ga kuma yabo da ake ji daga bakunan sauran jama’a a bayan fage lokacin wannan taro,duk yana haifar da ci gaba tsakanin musulmi, fahiomtar juna da kuma gane cewa wannan Manzo shi kadai ne tsirarmu, kuma kowa yana fafutikar binsa ne.to ya sa an fara kusantar juna, kuma wannan kusantar junan da hada kai, ba yana nufin ka aje abinda kake yi ka zo ka yi nawa bane, a a saidai yana nufi mu yi aiki inda muka hadu,inda bamu hadu ba mu yi ma juna uziri, to sai abubuwa su tafi daidai.
Ita dai wannan muzahara ta bana ta kayatar da al’ummar musulmi na wannan gari ta inda duk kane mi jin ta bakunan jama’a zaka ji suna yaba sabon salon da ta dauka.
‘yanuwa na bangarorin da’irorin yankuna , bangarorin halkoki yankunan ‘yanuwa maza da,mata ‘yan Islamiyyu da fudiyyoyin yankunan Katsina Daura Dutsinma ,Jibiya da ma wasu garuruwan duk sun hadu a wannan muzahara, hakama mawakan Musulunci, ga kuma tawagar Malam da Motocin ‘yanuwa suke biye sannan Harisawa suna tafe suna taka faretin da kusan ya dada daukar hankalin masu kallo.
An dai kammala wannan muzahara cikin nasara da fatan ganin ta shekaru masu zuwa cikin nasara da Imani.
No comments:
Post a Comment