Da yammacin ranar Juma’a 1/ 3/ 1432, Lajnar Islamiyyu ta harkar musulunci a Katsina ta gabatar da bikin murnar shigowar watan Mauludin Manzon Allah Muhammad (S) a harabar babban Masallacin Juma’a dake garin na Katsina.
Taron da aka gabatar da yammaci ya kunshi karance –karancen al’Qur’ani mai girma, wakokin yabon Manzon Alla (S) tare da gabatar da fared da daliban makarantu da dama da suka halarci wannan buki.
Bayan kammamal wannan bangare na karance-karance, daliban sun ci gaba da gabatr da wannan biki bayan kamala sallar Isha’I, inda suka gabatar da wata tattaunawa mai kayatarwa, mai taken “wanda ya fi bayar da gudunmuwa ga musulunci tsakanin Maza da mata”
Wannan muhawara ta kayatar , inda a karshenta Dalibai Mata suka zo na Daya , yayinda su kuma mazan suka zo na biyu.
Abinda ya kara burge mahalarta, shine yanda daliban mata suka rika bayar da hujjojin da suka doke na dalibai maza tare da halartowa da littafai masu dauke da hujjojin da suke kare matsayinsu, abinda ya jawo masu yawan maki.
An dai kamala wannan buki na bude tarukan mauludi da dama daliban suka saba gabatarwa duk shekara .
Mawakan gwagwrmaya suna daga cikin wadanda suka kawata wannan biki ta hanyar kara nishadantar da mahalarta da rero wakokin yabon Manzo da Iyalanbsa masu tsarki.
Mawakan gwagwrmaya suna daga cikin wadanda suka kawata wannan biki ta hanyar kara nishadantar da mahalarta da rero wakokin yabon Manzo da Iyalanbsa masu tsarki.
Jama’a da dama sun nuna gamsuwa da yadda aka gudanar da wannan muhawara, inda suka yi fatan wannan zata sa baki dayan ‘yanuwa su dukufa wajen tallafa ma wannan gwagwarmaya da Malam (H)( ya ke yi ma jagoranci.
No comments:
Post a Comment