A ranar Alhamis 23/2/1432 ne, Da’irar yanuwa Musulmi almajiran Sayyid zakzaky(H) ta Katsina, ta gabatar da taron yini daya da nufin samar da kyakkyawan tsari da zaya kayatar da bukukuwan mauludin ManzonAllah (SAW) na wannan shekara a karkashin jagorancin wakilin ‘yanuwan na yankin Katsina Malam Yakubu Yahaya a markaz da ke garin Katsina.
A taron, Mallam Yakubu ya bukaci ‘yanuwa da suke a Halkoki da su dinga gudanar da bukukuwan Mauludodin bayin Allah da halkokin suke dauke da sunayensu a duk lokacin da ranar haifuwar wannan bawan Allah ta zagayo. Sannan kuma su ‘yanuwan su fadada kyaututtuka da suke bayarwa ga bangarorin al’umma kamar marayu, tsofaffi, Sharifai zta hada da guragu Kutare da sauran makamantansu.Harwala yau, Malam yakubu ya bukaci ‘yanuwa da su kara shiri domin kayatar da bukukuwan murnar zagayowar watan haifuwar manzon Allah na wannan shekara.
A wannan taron dai, sai da kowane bangare ya tashi ya bayyana irin shirin da yake tsarawa da niyyar a karu da tsare-tsaren juna domin dai bukukuwan maulidin na bana su kayatar.
Damadai halkokin na wannan yanki suna dauke ne da kodai sunayen A’imma (AS) ko kuma sunan Manzo, Iyayensa Da sauran bayin Allah Mujaddadai da waliyyan
Allah maza da mata da suka ba wannan addini gagarumar gudun muwa.
An dai kammala wannan taro cikin nasara, kuma tuni shirye-shirye sun riga sun kankama na ganin nasarar mauludin Annabi (SAW) na wannan shekara.
No comments:
Post a Comment