Sunday, January 9, 2011

ISMA TA GABATAR DA KACIYA GA KANANAN YARA A WANNAN SHEKARA

Daga: AbdulAzizi
Bangaren kiwon lafiya na harkar Musulunci da Sayyeed Ibrhim Zakzaky(H) yake yi ma jagoranci da ke yankin Da’irar Katsina da kewaye ya kwashe mako uku yana gabatar da kaciyama yara a markazin ‘yanuwa dake cikin garin na katsina.


Aikin wanda aka fara gabatar da shi tun a ranar Assabat 20 ga watan al’Muharram 1432, ana cigaba da yinsa a duk ranakun Assabat da Lahadi.

Yusuf AbdulLahi ya bayyana cewa, Sashen na kiwon lafiya da ke karkashin harkar ta Islamiyya,yana gudanar da wannan kaciyar ne domin taimaka ma alumma kamar yadda Sayyeed Zakzaky(H) yake shiryarwa akan tallafa ma jama’a.

Kimanin yara sittin ya zuwa yanzu aka yi ma wannan kaciya, kuma har yanzu ana ci gaba da aiwatar da ita.

Shidai wannan aiki na kaciya sashen ya saba gabatar da shi, a duk shekara.

1 comment: