Daga:Abdul'Azizi
Dandalin dalibai na harkar Musulunci na yankin katsina, ya gabatar da taron karama juna sani da ya saba shirya ma dalibai da suke karatu a matakai daban-daban na Ilimi musamman makarantun gaba da primary a duk lokutan huto. wannan taro an gabatar da shi ne a harabar Makaratar Fudiyyah dake Unguwar Sabuwar kofa Katsina.
A taron an gabatar da darussa wadanda suka fi ba daliba dalibai wahala da suka hada da:Lissafi ,turanci science da sauransu a bangaren karatun boko,sai kuma abinda ya shafi darussan Addinin Musulunci, gami da ankarar Da su daliban abubuwan da suke faruwa a rayuwar yau da kullum a duniya baki daya.
Malam Isma’ila Yahuza wanda shine shugaban wannan dandali ,ya bayyana cewa, ana gabatar da wannan taro ne a duk lokutan hutu da niyyar kara horar da su daliban abubuwan da suka shafi karatunsu ,sannan a sanar da su abinda ya shafi Addini da wannan harka ta Musulunci da su Sayyeed Zakzak(H) yake yi ma jaagoranci, sannan a fadakar da su hikimomi da ya kamata su yi amfani da su a makarantu koda sukan sami kansu cikin wata matsala irin ta makaranta, duk wannan da niyyar su sami abinda zasu rika daga fara karatun zango zuwa dawowa wani hutun.
Taron wanda aka fara gabatar da shi tun daga ranar Laraba 4/2/1432 da yazo daidai da 5/1/2011, ya sami halartar dalibai da dama, sannan Malamai da dama ne suka bada tasu gudunmuwar wajen karantar da su daliban don ganin an cimma nasarar da ake bukata.
An dai kammala wannan taro na karawa juna sani cikin nasara da amfanuwa ga duk wadanda suka sami halartarsa.
Wasu daga cikin Daliban da suka sami halartar Mu'utamar da aka shiya a katsina
No comments:
Post a Comment