Sunday, January 9, 2011

YANKIN IMAM HASAN MUJTABA( AS) NA DA'IRAR KATSINA YA GABATAR DA MU'UTAMAR KARO NA BIYAR A GARIN WAGINI

Daga: AbdulAzizi

A karo na biyar ,yankin Imam Hasan Mujtaba(AS)dake karkashin Da’irar ‘yanuwa Musulmi al’majiran Sayyed Zakzaky(H)ta katsina ta gabatar da taron karawa juna sani a garin Wagini, karamar hukumar batsari ta jihar katsina.
Malam Sabo ATC tare da wakilin 'yanuwa na Wagini a Mu'utamar da aka gabatar a Yankin Imam Hasan Mujtaba(AS)
Kamar yadda aka tsara, Malamai takwas ne suka gabatar da jawabai a maudu’o’i daban-daban da suka hada da ,Ilmi,Mujahada,Kiyada ,Sadaukarwa da kuma Makoma,sannan Malam Yusuf Yamai ya gabatar da wa’azin dare a babban masallacin juma’a na garin.

A jawabin nasa,malam yusuf yamai, ya fadakar ne akan kalmar Shahada. Ya nuna cewa,ya kamata al’umma ta lura da abinda zaya gyara inganta wannan kalma ko bata ta. Ya ce, duk abinda ka ji ya sami wani Annabi na jarabawa tsakaninsa da wadnda aka aiko shi ,to sakamakon aiki da wannan kalma ce ta shahada, kisane ko kora daga gari.Sai ya yi nuni da cewa,mi ya sa a yanzu ake furta wannan kalma,amma babu wanio abu da yake faruwa na jarabawa kamar yadda ya faru ga magabata.

Malam Yusuf, ya bayyana cewa,babu yadda za a yi ka aikatawannan kalma ta shahada, sai ka sami mutum biyu.Watau Annabi da Allah ya aiko shi da sakon kalmar ,sai kuma shugaba mai hana abi sakon Annabin.ya ci gaba da cewa,Allah ya tsara tun azal cewa,akwai mai zowa da sako daga Allah,akwai kuma mai kawo ma sakon tarnaki.Sai ya e, dole sai kabi Annabi ko Wasiyyinsa ko kuma mujaddadaiko wanda suka wakiltar sannan zaka sami tsira a lahira.

Da yaker kara bayani dangane da masu ganin cewa shugabannin yanzu musulmi ne, sai ya bada misalin yaadda Shehu Usman dan Fodiyu ya fafata dada yumfa duk kuwa da cewa,shi yumfa Musulmi ne, hasalima al’majirin Shehu ne kafin ya zama Sarki ya dauki matakin hana Shehu da’awa.sannan ya yi nuni da sayyeed Zakzaky(H) a wannan lokaci da yake yunkurin kira da shugabannin yanzu suke ta yunkurin takura masa.sai ya kirayi Musulmi da su bi jagorancin da zaya kai su ga tsira sannan ya tsoratar akan rayuwa akan yin rayuwa babu shugaban da zaya kai mutum zuwa ga tsira gobe Kiyama, domin Shugabanci fa shine ma’anar kalmar shahada.

A jawabinda ya gabatar a madadin Malam yakub yahaya da bai sami halarta ba saboda wasu ayyukan na harka, ya yi kokarin karin bayanim akan darussan da aka gabatar a tsawon wadannan kwanaki, inda ya karfafa akan dagewa wajen neman Ilimi da aikin da shi kamar yadda maulana Sayyeed Zakzaky(H) yake ta ankararwa ,sannan ya koka akan yanda ‘yanuwa suka yi sanyi da Mujahada abinda ya ke kawo ma ‘yanuwa tsogunguma marasa tushe balle makama, sannan ya bukaci mahalartan da adawon ma wannan Mujahada tunda babu wata rana da mallam(H) ya ce a daina yi.ya yi fatan dukkan ‘yanuwa zasu dage domin samun tabbata abisa tafarkin da Malam (H) yake kira akansa.

A tun farko ,Malam Hamza Musa Wagin wakilin ‘yanuwa na gabri, ya nuna godiya da banhakuri ga mahalarta musamman da suka daure duk da yanayin sanyi da ake ciki,sannan ya yaba ma al’ummar wannan gari akan hadin kai da goyon baya da suka bayar domin ganin wannan Mu’utamar ya gudana cikin nasara.

Wani sashe na 'yanuwa da suka halarci Mu'utamar din da aka gabatar a Wagini



'Yanuwa mata a Mu'utamar da aka gabatar a Garin Wagini, katsina

No comments:

Post a Comment