Sunday, April 22, 2012

MU'ASSASATUS SHUAHADA'U TA GABATAR DA TARON KARA MA JUNA SANI NA WUNI UKU A KATSINA







A karo na biyar, Mu’assasatus Shuhada’u a Harkar musulunci a  Najeriya  da Sayyid Ibrahim Zazaky(H)     yake yi ma jagoranci, ta shirya taron karama juna sani  na ‘ya’yan Shahidan Harkar wanda yankin Shahid Hamza da ke KAtsina  ya shirya  a  garin  tun daga ranar Juma’a  29/5/ ha r  zuwa 1/6/ 1433.
A jawaban da  aka gabatar da suka kunshi muhadarori da masu jawabai . Dokta Abdullahi  Dan Ladi wanda ya yi jawabi aklan ‘ Ilimi ginshikin rayuwa” ya  bayyana  ilimin  da cewa, haske ne da Allah yake jefa shi a cikin zuciyar wanda ya ga dama, inda  ya  bayyana cewa, kowace halitta da Allah ya samar, to tana da nata ilimi da aka kimsa mata sai dai ilimin yakan bambanta  da na  juna. Dokta Abdullahi  ya bayar da misalai akan halittu na dabbobi da yadda suke rayuwa a tsakaninsu  abisa  ilimi  da Allah  ya hore masu, sai  ya  ce  amma ilimi dan  Adam ya bambanta dana dabba.
Dangane da ilimin Dan Adam,  cewa  ya yi,akwai wanda  mutum  ya  gada  kuma  yake koyo acikin al’uimmar da yake rayuwa  a cikinta sannan wanda ake koyowa a hannun malamai.
Dokta  ya  bayyana cewa, rayuwar mutum bata takaita anan duniya ba, akwai wata rayuwar ta bayan mutuwa, sai  ya ce, duk  wanda aka halitta , to za a yi masa Hisabi, kuma  ana  yi ma mutum  Hisabinne gwargwadon Iliminsa , ya bayyana  cewa, sai mutum  ya san Mahaliccinsa  sannan ne zaya iya bauta masa yadda ya kamata, sannan dole aikin mutum ya tafi kafada da kafada da iliminsa. Sai ya bayyana ilimin boko da cewa da shi da na addini duk daya ne matukar dai mutum ya yi  ilimin  domin Allah  da kuma niyyar taimakama al’umma. Ya kara da cewa, kamar yadda za a iya yi ma mutum azaba akan ilimin boko, to haka ma za a iya yin azabar ga mai ilimin addini madamar mai na  addini  bai yi amfani da ilimin  ba. Sai ya bayyana al’amarin karatu da cewa, ba abune mai sauki ba sai an dage sannan ne ake samunsa. Sai ya bukaci ‘ya’yan Shahidan da su  dage su kokarta su taka duk wani fage na ilimi da ake da shi, kuma a shirye Mu’assasar  take ta dauki  nauyin duk dan Shahidin da ya sami damar kara karatu kowane iri ne .
A jawabin da ya gabatar  Malam Abdull Hamid Bello Shugaban wannan Mu’assasa ta Shahidan Harkar musulunci, ya yi Magana ne akan kyawawan dabi’u, inda ya karanto Hadisai masu dama da suke Magana akan matsayin dabvi’u masu kyawu. Malam Abdul Hamid ya bayyana  tarbiyya   da cewa, ita ce,yin aiki mai kyau da barin maras kyau” Sannan ya bayyana cewa, Allah ya aiko mana da abin koyi watau Manzon Allah (S) wanda yake rahama a cikin halittu,sannan wannan Manzo shine madubi  da zamu kalla domin koyon dabi’u  daga wajen sa.Sai ya bukaci mahalarta da su siffantu da duk dabi’u  kyawawa  na  addini kamar ,gaskiya ,hakuri, yakini akan abinda mutum yake yi ,kyauta da dabi’ar mutunta kai”muru’a”ya kuma bukaci mahalarta su yi dubi cikin lamurransu domin siffantuwa da irin wadannan dabi’u saboda da irinsu ne kawai za a iya kawo gyara a cikin al’umma..
A jawabin kammal  wannan taro da ya  gabatar,  Malam Yakubu Yahaya  ya fara ne da gode ma Allah (T) da ya hukumta yin wannan taro na ‘ya’yan Shahidai masu albarka  a wannan Gari na Katsina,sai ya bayyana Shahada da cewa, ita ce sirrin nasara ”bama addini ba har lamurran rayuwa  ana bukatar sadaukarwa inada ya nusar  ta hanyar kawo wasu misalan al’ummu da suka sadaukar domin  su kubutar da kansu daga danniyar ‘yan mulkin mallaka inda  ya bayar da misalin gwagwarmayar mutanen Kenya da Aljeriya  a yayin kwatar kansu daga Turawa,sannan ya ce. Gwargwadon  sadaukarwarmu, daidai nasara da zamu samu sai ya nuna muhimmancin mu kara sadaukarwa  akan wannan tafarki na Addini” yadda  tarbiyya ta gurbata a wannan al’umma tamu, mafita daga wannan yanayi yana bukatar sadaukarwa”. Malam Yakubu  ya ce, Allah ya yi mana baiwar kasha  99 bisa dari domin ya albarkace  mu da  jagoranci , kuma wannan jagoranci  shi ne  makami na nasar saura kashi  daya  ake bukatar mu aikata, wannan  kashi guda kuma  shi ne “ji da  bi” ga wannan jagora . Malam Yakubun ya jawo hankalin ‘ya’yan Shahidan  da  cewa, su tsayu akan abinda  iyayensu suka sadaukar da rayuwarsun akansa watau gwagwarmayar addini sannan su guji aikata duk abinda za ya bakanta ran mahaifansu domin suna kawo masu ziyara lokaci-lokaci kamar yadda ya tabbata a Hadisin Annabi(S) Ya kuma bukaci  masu kula da iyalan shahidan  da s kara u kula da abubuwan da  yaran  su kanyi , a kwabe su idan suka yi abin da bai kamata ba. Ya tsoratar da yaran cewa, su guji yi kahon cewa, su ‘ya’yan sahidai ne  amma  su basu yin aikin da iyayen nasu suka  yi,  inda  ya  ce wannan ba zaya  fitar da su ba a lahira  sai dai idan sun yi aiki na kwarai . ya  kuma ankarar akan al’amarin wayoyin yaran da cewa, akwai  bukatar a rika kulawa da halin da wayoyin yaran suke ciki, domin akwai makircin bata  tarbiyyar ‘ya’yanmu da aka bollo da shi ta hanyar wayoyin tafi da gidanka.
A wannan mu’tamar an  samu nasarar kai ziyarori a wuraren  tarihi  da suka hada da Hasumiyar Gobarau,da Makabartar Dan Marna  wani waliyyi da aka yi  a Katsina  sai zuwa rijiyar  Gusugu dake birnin Daura tare da ziyatar shahid Ibrahim Muhammad Zariya da ya sami shahadarsa a lokacin waki’ar  janar Abacha.
Manufar shirya wannan taro dai  kamar yadda  Malam Abdul Hamid ya bayyana ma almizan shi   ne gina tarbiyyar ‘ya’yan  shahidai  a tafarkin da iyayensu  suka sadaukar da rayukansu  tare da wayar masu da kawunansu akan muhimman wurare na tarihi dake cikin wannan kasa. 

Saturday, February 18, 2012

YADDA AKA GABATAR DA TARON KARA MA JUNA SANI NA 'YANUWA 'YAN KASUWA A KATSINA

Kadan daga cikin hotunan da aka dauka yayin gabatar da taron karama juna sani na kwana biyu da 'yanuwa 'yankasuwa suka shirya a katsina, kwanakin baya.

Daga: AbdulAzizi




















Saturday, February 11, 2012

A CI GABA DA BUKUKUWAN MAULUDIN MANZON ALLAH, AN GABATAR DA FARETI A KATSINA

Akaro na biyu, Lajnar Islamiyyu ta harkar musulunci dake da’irar Katsina da kewaye, ta kaddamar da gasar farertin girmamawa ga Manzon Allah (S) na wannan shekara a ranar Assabat 19/3/1433, a Unguwar filin samji dake Katsina.
Makarantun islamiyyu, daga sassa daban-daban ne suka halarci wannan gasa, cikin makarantun da suka shiga wannan gasa, akwai Fudiyyoyin, Batagarawa,Magamar Jibiya,Rimi Abukur, Bindawa,sai Islamiyyu irinsu Baharul’Fatimiyya,Shabbabul’Mahadi,Tarbiyyatul’islam da sauransu,inda kowace makaranta ta fito ta gabatar da irin shirin da take da shi da zaya kayatar da faretin.
A jawabin da ya gabatar bayan Kammala wannan gasa, Malam Yakubu Yahaya Wakilin ‘yanuwa na Katsina, ya Godema daliban Makarantun ,malamansu tare da wadanda suka koyar da su irin wannan Fareti . Malam Yakubu ya bayyana cewa, irin duk abinda mutum zaya gabatar da zaya nuna murna ga samuwar Manzon Allah , to halal ne matukar ba ya sabama koyarwar Musulunci ba ne.Ya ce, ga masu ganin an zurfafa ga son Manzon Allah kuwa, “sai su nuna mana iyakar darajar Annasbi, mu kuma mutsaya a nan”.Daga nan sai ya kirayi iyaye da su kula sosai akan tarbiyyar ‘ya’yansu, musamman a wannan lokaci da makiya suke kirkiro da wasu hanyoyi na lalata tarbiyyar ‘ya’yan musulmi. Ga wadanda ‘ya’yansu suke da wayoyi kuwa ,ya kiraye su da su rika kulawa da irin abubuwan da suke cikin wayoyin yaran nasu don sanin halinda suke a ciki, sai ya ce mafita daga irin wannan tarko shine kusantar Allah (T) da ibadu tare da aza yaran bisa tsayuwa da ibadun,Ya yi nuni da cewa ,kada kaga yaranka yana karatu,wannan bai isa ba sai an kula da irin abokan da suke tare da su.
Ita dai wannan gasa ta fareti a tabakin Malam Yakubu Idris wanda shine shugaban Lajnar ta Islamiyyu, cewa ya yi, an shirya wannan gasa ce, domin girmamawa ga Manzon Allah(S) kuma wannan sababben abu ne cewa, idan wani wanda ake girmamawa ya kai ziyara a wasu kasashe, to ana shirya masa fareti, saboda haka wannan Lajna ta tsara gabatar da shi domin girmama Manzon Allah(S).
Makarantunn da suka samu nasara a wannan gasa ta bana, sune, Fudiyya Batagarawa a matsayin ta hudu, Baharul Fatimiyya ta uku, Fudiyyah Rimi ta biyu sai Tarbiyyatul Islam Marnar Kadabo matsayin wadda tazo zakara watau ta daya.
Ashekarar da ta gabata ne dai aka fara gabatar da irin wannan gasa a cikin tsare-tsaren bukukuwan Mauludi. An dai kamala gasar cikin nasara da farin ciki daga al’ummar da suka sami halarta. 














Saturday, January 21, 2012

DANDALIN MATASA NA YANKIN KANO YA ZIYARCI NA KATSINA


 
A ranar  Laraba ne  25/ n2/ 1433 A.H,tawagar ‘yanuwa na Dandalin matasa na yankin Kano, suka kawo ziyara ga takwarorinsu da ke  Katsina domin sada zumunci tare da gabatar da jawabai na karfafa juna.
A jawabin da ya gabatar , shugaban dandalin na matasan harkar musulunci a karkashin jagorancin Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) Malam Hafizu Dauda  Kano, ya ankarar da ‘yanuwa matasa na gwagwarmaya akan manufar wannan ziyara , inda yace,domi sada zumunci ne da tattauna yadda za a iya haduwa a  karfafa juna , sai  ya ce, akwai bukatar kowanensu ya kula da kansa ta hanyar  siffatuwa  da kyawawan dabi’u, ganin cewa a yanzu akwai gurbacewar  tarbiyya. Ya kuma ya karfafi  ‘yan  dandalin da suci gaba da nemo malaman harka, ko masana su  rika yi masu bayani akan wasu bangarori na harka, ya kuma yi kira ga Malaman harkar nan da kara sa kula su fahinci matsalolin matasan domin a shigowa  da magancce su.
A wani sashen jawabin , Malam Hafizu ya tunanatar da ‘yanuwan cewa,Sayyid (H)  ya bayyana matasa a maatsayin jari na wannan harka,sai ya nuna wajabcin siffantuwa da kyawawan ayyuka  kamar  yadda Sayyid din yake koyarwa, sannan ya  bukaci matasan su kauce ma munanan ayyuka da za su jawo suka ga wannan kira da Sayyid din ke ma jagoranci. ya kuma bukaci matasa su kara kulawa da al’amurran harka ta hanyar nazartar tarihinn kiran, yaddad  harkar ta taso da irin sadaukarwar da magabatanta suka yi  domin samun damar tsayuwa akan ta.Sai yayi kira akan dagewa da ibada ta hanyar azumomi da sallolin na da makamantansu. A karshen jawabin nasa, ya bukaci kowane matashi ya zamo yana da wata gudunmuwa da yake bayarwa a wannan harka domin ta ci gaba.
A nasa  jawabin, danuwa Sanusi  Idris Musa, jawo hankalin matasa ya yi ta hanyar nuna takaicin  yadda suke wahalar da maluman harka  ta yin watsi da shiryarwar da suke yi a kodayaushe, sai  ya bukaci matasan su sa tunani tare da nazartar maganganun  Maluman, da kuma yin aiki da su.Ya ce  koda  kashi Hamsin cikin Dari na maganganunsu  aka yi aiki da su, to  da an ga sauyi a rayuwar  matasan. Ya shawarci matasan da cewa, kowanensu ya  duba  ya ga inda yake da gajiyawa ya yi aiki domin gyara matsalarsa saboda ana yin wannan harka ne domin neman  yardar  Allah(T).
Malama Fatima Yusuf Ali , daya  daga cikin wadanda suka kawo ziyarar daga Kano, ta bukaci ‘yanuwa maza da mata da su himmatu akan neman sanin ilmomi tare da sanin ilimin computer da harkar internet  domin yada  da’awar  Malam (H),ta kuma  jawo hankali akan dagewa  dai  da mujahada  domin iya tunkarar halin da ake ciki a yanzu haka.

A jawabin godiya da ya gabatar, Shamsuddin  Ahmad  a madadin ‘yan dandalin na yankin  Katsina, ya nuna godiya  ga , maziyartan da wannan  ziyara da suka kawo masu , ya kuma yi fatan su ‘yan kwamitin za su yi amfani da duk abubuwan da suka ji a wannan zama.
An kammala wannan ziyara cikin nasara, kuma tuni bakin suka isa gida lafiya.
   

Tuesday, December 6, 2011

AN GABATAR DA MUZAHARAR JUYAYIN ASHURA TA SHEKARAR 1433 A KATSINA


A wannan rana ce ta Talata 11 / 1/ 1433, ‘yanuwa musulmi almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) a karkashin jagorancin Malam Yakubu Yahaya  Katsina kamar sauran takwarorinsu na duniya, suka gabatar da Muzaharar juyayi da nuna bakin ciki akan kisan da Yazidawa makiya zuriyar Manzon Allah suka yi ma Imam Husaini Dan Ali dan Abi Dalib Dan Fatima diyar Manzon Allah (S) da zuriyarsa tare da abokansa a filin karbala.

A jawabin da ya gabatar bayan kamala wannan  gagarumar muzahara, Malam Yakubu Yahaya wakilin ‘yanuwa na garin Katsina, ya bayyana  cewa, manufar wannan jerin gwano shine jajantawa tare  mika ta’aziyya ga Manzon Allah(S), Imamul Asr(AJ), Sayyi Ali Khaminei da Sayyid Zakzaky(H) da sauran bayin Allah.Ya ce , mika  wannan ta’aziyya  duk duniya ne ake  yi ba nan kawai bane kamar yadda wasu suke dauka, ya ce , zaman makoki da irin wannan muzahara duk ta’aziyya ce zuwa ga Manzon Allah, domin shine wanda aka cutar, kuma wannan ya faru tun bayan wafatinsa.ya kara da cewa, bayan wannan ta’addanci ,an tafi  da zuriyar Manzon Allah mata da kananan yara  da suka  yi saura daga filin Karbala  zuwa Sham fadar Yazidu dan Mu’awiyya (LA) a kasa ana tafe ana tozarta su a duk garin da aka wuce ta cikinsa. ya ce, sakamakon wannan ta’addanci ne Allah ya sallada  ma musulmi Kaskanta  a hannun Magolawa kafiarai  abin da ya tafo har wannan zamani da musulmi suke cikin kaskancin Kafiran duniya.

Sannan ya ce, lokacin dawowar musulmi akan lamarinsu na addini ya yi,domin addinin ne zaya hada su waje daya. Sai ya ce, dole ne abinda ya dami Manzo ya dame ka, kuma dole ne ranar bakin cikinsa kaima ta zama rana ce ta bakin cikinka idan dai har Manzon kake bi kai ba munafuki bane ba kai
.
Malam Yakubu ya nasihanci masu sukar abinda muke yi da ganin ba daidai bane, da su binciki littattafansu indai har da gaske suke yi ba munafunci bane.Ya kara da cewa, Allah ya kawo lokacin da za’a gane abinda aka yi ma wadannan bayin Allah, kuma ko bamu nan  ga ‘ya’yanmu nan zasu ci gaba da wannan al’amari.”Ya nasihanci malamai da su ji tsoron Allah, su tsaya ma gaskiya domin jama’a suna kallonsu, ya ce “wannan lamari na Shi’a yazo zama ne”.

Ya kuma ja kunnuwan mahukunta dake hankoron hanawa ko afkama wannan lamari da cewa,”wannan Shi’a din ita ce ajalin gwamnatin wannan kasa, sai ya gargade su da cewa”su ja bakinsu su tsuke, su sama wannan al’amarin  ido, “idan kuma kuka ce ba haka ba,  za ku yi rigima ne da al’umma, domin al’umma adalci take so kuma a addini ne ake samunsa,  ya kuma ce,” babu wanda zaya fahimci wannan gida na Annabi, sannan ya rabu da shi . “idan ba za ku zo ayi da ku ba, kusa ido.Kawo jami’an tsaro da kuke kokarin yi  kuma ku yi ta kawowa, kuna amfani da zahirine shi kuma Allah yana amfani ne da zukata.

 Ya kare da cewa, da Imamu Husaini bai tashi ba da yanzu ba addini ne ake yi ba , domin su Umayyawa sun shirya maido da Jahiliyyar da Manzon Allah ya kawar ne, mikewar Imam it ace ta tsaida su.

Ita dai wannan muzahara, dubunbubatar ‘yanuwane maza da mata da kananan yara suka gabatar da ita a cikin yanayi na juyayi da nuna bakin cikin abinda aka yi ma zuriyar Manzon Allah bayan rasuwarsa.