Monday, November 18, 2013

'YANUWA SUN BAYAR DA GUDUNMWAR JINI A KATSINA


Sadaukar da jini don bayarwa ga masu bukatarsa a irin wannan lokaci na nuna juyayin Ashura kamar zaburantarwa ne a gare mu, dokmin Imam Husaini (AS)ba jininsa kawai ya sadaukar ba, yama sadaukar da rayuwarsa ne gaba daya data iyalansa dama Sahabbansa.Malam Yakubu Yahaya  wakilin ‘yanuwa musulmi almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky(H) na katsina ya b ayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a yayin bayar da jini da ‘yanuwan suka yi albarkacin sadaukarwar Imam Husaini(AS).
  
Malam Yakubu yahaya ya bayyana cewa, “an san muhimmancin bayar da jini a wannan zamani, domin shi jini jigo ne a rayuwa, shi yasa ma zaka ga  ana farautar jini harma da kudi domin mutane su  samu su rayu, musamman yayin bukata, ko saboda haihuwa, hadari da makamantansu. Shi ya sanya masana suka muhimmantar da bayar das hi.”Sai ya karfafa bukatar bayar da jini muddin hakan zaya amfanar da dan Adam.
Ta fuskacin addini, malam Yakubu ya bayyana cewa, idan mutum ya bayar da jini aka ceto rayuwar mutum daya, ladar da zaya samu kamar ya ceto rayuwar al’umma ne baki daya.Ya karfafa maganar da ayar nan dake nuni da cewa, ‘wanda ya  kasha rai, kamar ya kasha rayuka ne baki daya, wanda ya raya rai daya, ,kamar ya raya rayuka ne gaba daya” Ya kara da cewa, ba a la’akari da wanene kaba jinin musulmi ne,ko ba musulmi ba,in dai sunan sa  rai, za a bas hi jinni domin ya rayu, idan yaso shi ya yanke ma kansa hukuncin zabin abin da zaya yi.
Malam Yakubu ya tabbatar da cewa, bayar da jinni yana kara lafiyar mutum,sannan kuma ta hanyar bayarwar za a iya fahimtar yanayin lafiyar mutum ta yadda idan mutum yana da wata matsala, za a iya shawo kanta cikin sauri ba tare da ta ketara zuwa ga wani ba.’ka gay a sami lada kuma ya san matsayin lafiyarsa’ daga nan sai malam Yakubu ya karfafa sadaukar da jinin da cewa, ba sai lokacin Ashura ba ne kadai  za a iya bayarwa, a’a  akwai bukatar mutum ya bayar idan akwai bukata matukar dai  za a iya yin hakan.Sai ya yi fatan ganin Allah  ya kai mu lokacin da zamu bayar da rayuwar mu gaba daya domin daukar fansar zaluncin da aka yi ma Imam Husain(AS).
Likitan da yake jagorantar kungiyar karbar jinin da rabashi ga mabukata a wannan aikin, Dakta Iisma’il Buhari, kira ya yi ga jama’a da suke dari-darin bayar da gudunmuwar jini da cewa, bayarwar ba bata da wata matsala, domin ba haka nan ake dibar jinin mutum ba har sai an gabatar da tambayoyin da za su kai ga fahintar cewa, za a iya dibar jinin mutum lafiya lau ba tare da ya sami wata matsala ba, idan kuwa aka fahinci cewa, dibar zata haifar masa da matsala, to bama za a diba ba.
Sai ya nemi sauran jama’a  da a daure a rika bayarwa, domin bayarwar abu ne mai muhimmanci, saboda ceton rayuwa. Ya kara da cewa, ‘abin lura shi ne, idan jama’a basu bayar da wannan gudunmuwa ba, to babu inda za a je a samo shi.” Sai ya tabbatar da cewa,bayarwar ba matsala ba ce sai ma lafiya ta za a kara samu. ‘kodai mutum ya bayar, ko bai bayarba, jinin yakan  lalace a cikin kowane wata  Allah ya sake samar da wani’Sai ya yaba ma ‘yanuwa musulmi da suke  kokarin tallafawa da jinin kyauta ba tare da ana biyansu  kudi ba.
Malam Abdul karim Usamatu, shi ne wanda yake jagorantar kwamitin  ISMA  a wannan yanki, ya  bayyana karuwar jama’a da suke bayar da wannan gudunmu da cewa, ‘ fahimtar muhimmanci bayarwar ne  da jama’a suke yi sakamakon bayanin da kwamitin yake yi lokaci-lokaci musamman lura da suke yi cewa, bayar da jinin ibada ne sannan kuma yana kara lafiya ne ga duk wanda ya bayar.
A bana dai adadin wadanda zasu  bayar da jinin ya nunka na bara idan aka lura da al’kalumman da kwamitin kiwon lafiya  na harkar musulunci (ISMA) ya tattara a wannan shekara.  

No comments:

Post a Comment