Tun da sanyin safiyar
wannan rana ta Alhamis ne ta 11/1/1435 hijiriyya, dubun dubatar al’ummar
musulmi suka fara yi ma garin Katsina kabbara domin amsa kiran Sheikh Ibrahim
Almagri(H) na gabatar da muzaharar Ashura don nuna jaje ga Manzon Allah da
Iyalansa na kisan da rundunar yazidu (L)
ta yi ma Imam Husaini(AS) da sauran zuriyar Annabi(S) da kuma nSahabban Imam
Husainin a karbala.
malam Yakubu ya mika ta’aziyyar ‘yanuwa da suka halarci wannan muzahara ga Manzon
Allah da iyalansa masu tsarki, sannan ya kuma mika wannan ta’aziyya ga
jagororin gwagwarmayar duni a wannan lokaci haka kuma zuwa ga sheikh
zakzaky(H). Daga nan ya bayyana
cewa,wannan abu da ya faru ga
iyalan Annabi(S) kiyayya ce ,inda ya tabo irin yadda Kuraishawa suka
shiga musulunci akan dole bayan da suka ga an rinjaye su.”Suun shiga musulunci
ne ganin babu yadda zasu yi domin an
rinjaye su, sai suka ga bari su shiga cikinsa
domin su bata addsinin” kawo maganar Abu- jahal da ya ce, ba suna
tuhumar Muhammadu ba ne da wani aibu.Sai malam Yakubu y ace, watsi da wasicin
manzon Allah ne da ya yi a Gadir da aka
yi , shi ne ya jawo hawan Yazidu dan Mu’awiyya mulkihar ya yi aika-aikar da aka
yi.
Malam yakubu ya kara da cewa, bayan wannan kisan ne da suka
yi ,sai aka yi kokarin kawo ruwayoyi da suke nuna matsayin wannan rana ta
ashura domin rufe wannan aibu, ya ci gaba da cewa, an yi kokarin shafa ma
wadannan mabarnata farin fenti aka wanke su aka ce ma su ne masu addinin
gaskiya.sai y ace, wadannan karairayi duk na banu Umayya ne don su rufe laifin
da suka yi ma Allah da manzo.Sai y ace, wannan abiun da muke yi ba wasa bane ba
kuma yayi ba nedomin l;olkacin yayi ya wuce a wajen mu, saboda tun muna yi mu
kadai har gas hi yanzu muna yi tare da jikokinmu,ddon haka addini muke ba wasa
ba.
No comments:
Post a Comment