Malam Yakubu Yahaya wakilin ‘yanuwa musulmi almajiran Sheikh
Ibrahim Zakzaky(H) na da’irar Katsina, ya kai ziyarar ta’aziyya ga gwamnan
Jihar ta katsina Alhaji Ibrahim Shehu Shema sakamakon rasuwa da mahaifin gwamnan ya yi a ranar Litinin
11//11/2013 da ta gabata.
Malam yakubu ya jajanta ma gwamnan da zuriyar sa akan wannan
rashi na mahaifinsu. Malam yakubu ya bayyana ma gwamnan muhimmancin yin addu’a
ga mamacin inda ya sheda masa bukatuwa da mamata suke da ita ta addu’a da kuma
hakkin day a rataya ga wuyan ‘ya’ya na yin addu’a ga iyaye.
Gwamnan na Katsina Alhaji Ibrahim Shema ya gode ma Malam
yakubun dangane da wannan ta’aziyya day
a kai masu, sannan ya yi rokon isar da godiyarsa ga Sheikh Ibarahim Zakzaky(H)
saboda wannan karamci da aka yi masu.
Wasu daga cikin ‘yanuwa ne dai suka raka Malam yakubu wannan ta’aziyya.
No comments:
Post a Comment