Thursday, February 24, 2011

WASU DAGA CIKIN HOTUNAN DA AKA DAUKA A YAYIN GABATAR DA MUZAHARAR MAULIDI A KATSINA

Daga:AbdulAzizi






ISMA TA KAI ZIYARA GIDAN KURKUKU

A ci gaba da gabatar da bukukuwan maulidin Manzon Allah da ‘yanuwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky(H) suke gabatarwa a fadin wannan nahiya, ‘yanuwa mata na sashen kiwon lafiya(ISMA) dake Katsina sun gabatar da wata ziyara a gidan kurkukun garin Katsina a ranar Alhamis 21/ 3/ 1432.




A lokacin da suke ganawa da tsararrun, ‘yanuwan sun gabatar masu da nasiha gami da tausaya masu akan wannan hali da suka sami kansu.Malama Hajara wadda ta yi Magana a madadin ‘yanuwan ta bayyana wannan ziyara da cewa, sun kawo ta ne sakamakon shiryarwar Sayyid Zakzaky(H) da ya ke yi ma ‘yanuwa na su maida hankali wajen gabatar da ayyuka na taimaka ma al’umma,sannan ta bukaci ‘wadanda suke tsaren da su sa tsoron Allah a cikin al’amarin rayuwarsu. Ta nuna takaicin ganin yadda wadannan matan suke tsare kasantuwarsu iyayen al’umma, amma wani yanayi ya sa sun sami kansu a wannan wuri.Sai ta bukaci su dauki darasi am wannan zama da suka yi, ta hanyar kyautata halayyarsu tare da sauran jama’a da suke rayuwa da su kuma ta bukace su da su kara hakuri da al’amarin rayuwa da kuma fatan ba zasu sake komowa a wannan wuri ba.

Itama ‘yaruwa Mariya Zakariyya kira ta yi garesu da su guji aikata duk wani hali da zaya sa su sami kansu a wannan gida, ta ce abin bakin ciki ne ace matan suna tsare a wannan wuri, sakamakon aikata wani abu da bai dace ba.sai ta yi fatan zasu yi amfani da wannan wuri wajen gabatar da Istigfari da bauta da addu’o’in neman tsari da sake kawosu dama sauran mata wannan gida tare da fatan zasu koma gidajensu domin ci gaba da gabatar da abinda ya kamace su kasancewar su iyaye.

Wanda ya karbi yanuwan a madadin shugaban gidan yarin, Muhammad Bello, ya nuna matukar godiya da farin ciki akan wannan ziyara, kuma ya yi fatan Allah ya taimaka .

Ita dai wannan ziyara, an kai ta ne a bangaren mata da suke tsare a wannan gidan yari da ke cikin birnin Katsina.

Tuesday, February 15, 2011

AN GABATAR DA MUZAHARAR MAULIDIN MANZON ALLAH A KATSINA

ABDULAZIZI
‘Yan uwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky(H) na da’irar Katsina da kewaye sun gabatar daMuzaharar Murnar zagayowar Wata da ranar da aka haifi Fiyayyen halitta( a wata ruwaya) Manzon Rahama Muhammad (S)  a ranar Talata12/ 3/1432.

Da yake bada amsoshin tambayoyin manema labari bayan kammal wanna gagarumar muzahra, Malam Yakubu Yahaya Katsina, ya bayyana cewa,  sakon Maulidin  wannan shekara ya na albishir ne ga al’ummar musulmi.Inda yace, wanda yake da dimbin magoya baya  kamar Manzon Allah (S), to shine ya kamata ya shige ma mutane gaba. Ya nuna cewa,lokaci ya yi da za a dawo abi bayan Manzon, ya kara da cewa,idan har mutane suna ganin mafita a wani tsari ba  na Manzon ba,to shi tsarin ya karye, domin yanzu abin da ake ga ni a tsarin duniya wanda kuma ake tutiya da takama da shi tun farkon karnin da ya gabata ya fara karyewa ya kuma fara cin tura. Ya  ce yanzu ya zama lazim komawa tushe musamman ma ga al’ummar musulmi.
 Ya kuma bayyana cewa,rashin riko da addini da musulmi suke yi ne ya sa wadanda ba musulmi ba su ke yin nesa-nesa da musulunci, duk kuwa da sha’awar da suke yi da addinin sannan ya ce,da musulmi za su lazimci riko da addinin, da Allah(T) za ya karkato da zukatan sauran mutane zuwa ga son addinin wanda kuma dama hakki ne akan su musulmin domin kusan wanda ya fandare wanda ba musulmi ba, to alhakin sa yana bi sa wuyan musulmi ne, saboda Allah ya nuna cewa,idan musulmi basu dunkulu waje daya ba, za a sami babbar fitina a bayan kasa.Aikin musulmi ne su hadu bayan Manzon Allah domin su kawo karshen fitinun da matsalolin da duniya take fama da su.
Ya bayyana yadda aka samu ci gaba ta fuskacin kawata wannan mauludi na bana duk kuwa da bambance-bambancen dake tsakaninn al’umma   a fahimta da cewa, abin sha’awa ne, domin haduwa wajen gudanar da irin wannan taro na Muzahara domin nuna murna da zagayowar wannan lokaci, ga kuma yabo da ake ji daga bakunan sauran jama’a a bayan fage lokacin wannan taro,duk yana haifar da ci gaba tsakanin musulmi, fahiomtar juna da kuma gane cewa wannan Manzo shi kadai ne tsirarmu, kuma kowa yana fafutikar binsa ne.to ya sa an fara kusantar juna, kuma wannan kusantar junan da hada kai, ba yana nufin ka aje abinda kake yi ka zo ka yi nawa bane, a a saidai yana nufi mu yi aiki inda muka hadu,inda bamu hadu ba mu  yi ma juna uziri, to sai abubuwa su tafi daidai.
Ita dai wannan muzahara ta bana ta kayatar da al’ummar musulmi na wannan gari ta inda duk kane mi jin ta bakunan jama’a zaka ji suna yaba sabon salon da ta dauka.
‘yanuwa na bangarorin da’irorin yankuna , bangarorin halkoki yankunan ‘yanuwa maza da,mata ‘yan Islamiyyu da fudiyyoyin yankunan Katsina Daura Dutsinma ,Jibiya da ma wasu garuruwan duk sun hadu a wannan muzahara, hakama mawakan Musulunci, ga  kuma tawagar Malam da Motocin ‘yanuwa suke biye sannan Harisawa  suna tafe suna taka faretin da kusan ya dada daukar hankalin masu kallo.
An dai kammala wannan muzahara cikin nasara da fatan ganin ta shekaru masu zuwa cikin nasara da Imani.

Monday, February 7, 2011

YANKIN AMINA UMMUR'RASUL NA BANGAREN 'YANUWA MATA YA GABATAR DA MAULIDIN MANZON ALLAH(S)


“Musulunci ne ya kawo juyinjuya hali  na tunani dangane da daidaita maza da mata.” Malam yakubu Yahaya  ya bayyana haka a lokacin gabatar jawabi a wurin taron Maulidi  Annabi (S) da yanuwa mata na yankin Amina Ummur Rasul(zone A) na Katsina suka shirya.
Malam yakubu ya yi nuni da cewa,mata basu da hakki a lokacin jahiliyyar Larabawa sannan basu da wani amfani a wajensu, sai dai biyan bukatar rayuwa,shi ya sa ma suka aibata manzo da cewa, ya kawo daidaito tsakanin mazan da mata,saboda su basu dauki matan da wata kima ba.wannan kuma ya sa suke ganin ya yi masu laifi, abinda ya sa suka ki yin Imani da shi.ya kara da cewa, da namiji da mace, darajarsu guda a wajen Allah(T) . jingina su da  Musulunci  ya yi ga maza, ba gazawa ba ne gare su, sai dai kowane bangare akwai aikin da aka hore masa. Ya ce, kasantuwar mata suna tsayuwa da ayyukan gida, taimakon juna ne domin shi namiji shi ne ke tsayuwa da hidindumun waje. Sai ya ce,”a gwagwarmayar neman duniya, babu yadda za a yi mace ta yi gogayya da namiji,amma a gwagwarmaya neman Addini da Ilimi,mace na iya wuce namiji domin zuciya da kwakwalwa iri daya Allah ya yi masu.”
Da yake fadakar da masu mamakin yin addini tare da mata, cewa  ya yi, jama’a sun yarda siyasa a yi tare da mata amma Addini banda su, ya kara da cewa,akai bukatar mace ta yi addini, domin babu wanda zaya so mahaifiyarsa ta sha bugu a kabari Kakarsa ko matarsa da suka yi zaman mutunci.” Babu yadda za a yi a kauce ma wannan bugu sai idan an yi addini”
A wani bangare na jawabin ,Malam Yakubu ya bayyana cewa,”Manzon Rahama ya ’yanta mata, kuma ya suturta su,inda ya wajabta masu saka Hijabi” hijabi  da Sallah ga mace matsayinsu daya saboda Mala’ika Jibrilu ne ya zo da ayar Sallah da hijabi, ba Hadisi bane balle kace rarrauna ne” ya ce, “idan har zaka hana matarka ko diyarka ko kuma kanwarka sa hijabi, to gara ma ka hana ta yin Sallah domin wanda ya ce ayi Sallar shi ne kuma yace su sa hijabin, kuma cewa su sa hijabin karramasu aka yi sabanin yadda Turawa suke yekuwar cewa an takura masu”
A karshen taron ,an rarraba kyautuka ga bangarori da dama da suka hada da wata dattijiyar yaruwa, marayu,'yayan Shahidai da wasu mata masu Suna irin na mahaifiyar Manzon Allah (S) da sauransu.
 

WASU HOTUNAN MURNAR SHIGOWAR WATAN HAIFUWAR MANZON ALLAH DA LAJNAR ISLAMIYYU TA KATSINA TA SHIRYA

Hotuna daga Abdul"Azizi Nasir
Wata daliba tana karanta Ayoyin al'Qur'ani mai tsarki a wajen bikin murnar shigowar watan maulidi a Katsina
 Wasu 'yan makarantar Islamiyya suna fareti a ranar murnar shigowar watan haifuwar manzon Alla(S)
Dalibai daga wata makarantar Islamiyya a wajen bikin
Bangaren wasu 'yan makaranta suna kallon fareti da aka gabatar a lokacin taron

Wata daliba tana karatu a wajen taron





LAJNAR ISLAMIYYU A KATSINA TA SHIRYA BIKIN MURNAR ZAGAYOWAR WATAN HAIFUWAR MANZON ALLA(S)



Da yammacin ranar Juma’a 1/ 3/ 1432, Lajnar Islamiyyu ta harkar musulunci a Katsina ta gabatar da bikin murnar shigowar watan Mauludin Manzon Allah Muhammad (S) a harabar babban Masallacin Juma’a dake garin na Katsina.
Taron da aka gabatar da yammaci ya kunshi karance –karancen al’Qur’ani mai girma, wakokin yabon Manzon Alla (S) tare da gabatar da fared da daliban makarantu da dama da suka halarci wannan buki.
Bayan kammamal wannan bangare na karance-karance, daliban sun ci gaba da gabatr da wannan biki bayan kamala sallar Isha’I, inda suka gabatar da wata tattaunawa mai kayatarwa, mai taken “wanda ya fi bayar da gudunmuwa  ga musulunci tsakanin  Maza da mata”
Wannan muhawara ta kayatar , inda a karshenta Dalibai Mata suka zo na Daya , yayinda su kuma mazan suka zo na biyu.
Abinda ya kara burge mahalarta, shine yanda daliban mata suka rika bayar da hujjojin da suka doke na dalibai maza tare da halartowa da littafai masu dauke da hujjojin da suke kare matsayinsu, abinda ya jawo masu yawan maki.
An dai kamala wannan buki na bude tarukan mauludi da dama daliban suka saba gabatarwa duk shekara .
Mawakan gwagwrmaya suna daga cikin wadanda suka kawata wannan biki ta hanyar kara nishadantar da mahalarta da rero wakokin yabon Manzo da Iyalanbsa masu tsarki.
Jama’a da dama sun nuna gamsuwa da yadda aka gudanar da wannan muhawara, inda suka yi fatan wannan zata sa baki dayan ‘yanuwa su dukufa wajen tallafa ma wannan gwagwarmaya da Malam (H)( ya ke yi ma jagoranci.  

Sunday, February 6, 2011

MAULIDIN YANKIN RASULUL AKRAM



A ci gaba da raya al’amarin mauludin Manzon Allah(S) da harkar musulunci karkashin jagorancin Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) ta shirya take gabatarwa a fadin wannan kasa,Yankin Rasulul akram zone(A) na da’irar yanuwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky(H) ta Katsina ya shirya taron wannan mauludi na Manzo a ranar Litinin 27/2/1432 a Unguwar Filin Fayis dake cikin garin Katsina.



Da yake gabatar da wa’azi a wajen , wakilin ‘yanuwa musulmi almajiran Sayyid (H) na Katsina, Malam Yakubu Yahaya, ya tunatar da al’umma ne akan wajabcin kulawa da Ruhi da Allah (T) ya halitta sannan ya saka shi a gangar jikin Dan Adam. Malam Yakubu ya bayyana cewa,Jama’a da dama a halin yanzu sun jahili muhimmancin Ruhi, sai suka koma suna hidimar gangar jiki,abin mamaki kuma har da Malamai. Wannan ya sa Malaman suka koma suna bin jahilai masu mulki bisa tsarin da ya saba ma na Allah(T). Ya ci gaba da cewa,”Annabawa ba su zo duniya domin biyan bukatun gangar jiki ba, shi yasa ma suka rayu ba tare da abin duniya ya dame su ba, sai dai suna amfani da abin duniya ne gwargwadon bukata, kuma wannan shi ne abinda mutane suka jahilta.” in ji shi.

Malam Yakubu ya ce,” bayin Allah wadanda suka dandani sirrin sanin Allah suke jin dadin bautar Allah domin Ruhi bautar Allah ita ce abincinsa”. “Ruhin dan Adam yana tunanin hutawa ne, amma hutawa marar iyaka ba a samunta a wannan duniya”Madamar mutum bai fahinci abinda ya kawo shi duniya ba zai yi nadama a lokain da ya mutu. Inda ya karfafa wannan batu da Hadisin Manzo da ya nuna cewa, “mutane suna barci ne sai sun mutu sai su farka”. “a gaskiya mutum shi ne Ruhinan wanda ba a ga ni, kuma Ruhi shine abinda Annanbawa suka damu da shi “

Malam Yakubu ya kara da cewa, yunkurin Annabawa na tsarkake Ruhin Mutane ya jawo masu rigima da mahukuntan lokacinsu, Abinda ya jawo rigima ken an tsakanin Shehu dan Fodiyo da sarakunan Hausa domin yana kokarin tsarkake Ruhi da maida mutane zuwa ga Allah, su kuma Sarakunan suna hanawa. Sai ya yi mamakin yadda Malamai ahlussunna a nan suke karanta al’Qu’ani , amma suna mika mutane zuwa ga Azzalumai.Malam Yakubu ya karkare da cewa, da muyi abinda babu Allah, gara muyi na Allah komin nisan dadewa ko wahala.

Ya yi fatan samun taimakon Allah domin samun tsira duniya da L:ahira