Tuesday, December 6, 2011

AN GABATAR DA MUZAHARAR JUYAYIN ASHURA TA SHEKARAR 1433 A KATSINA


A wannan rana ce ta Talata 11 / 1/ 1433, ‘yanuwa musulmi almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) a karkashin jagorancin Malam Yakubu Yahaya  Katsina kamar sauran takwarorinsu na duniya, suka gabatar da Muzaharar juyayi da nuna bakin ciki akan kisan da Yazidawa makiya zuriyar Manzon Allah suka yi ma Imam Husaini Dan Ali dan Abi Dalib Dan Fatima diyar Manzon Allah (S) da zuriyarsa tare da abokansa a filin karbala.

A jawabin da ya gabatar bayan kamala wannan  gagarumar muzahara, Malam Yakubu Yahaya wakilin ‘yanuwa na garin Katsina, ya bayyana  cewa, manufar wannan jerin gwano shine jajantawa tare  mika ta’aziyya ga Manzon Allah(S), Imamul Asr(AJ), Sayyi Ali Khaminei da Sayyid Zakzaky(H) da sauran bayin Allah.Ya ce , mika  wannan ta’aziyya  duk duniya ne ake  yi ba nan kawai bane kamar yadda wasu suke dauka, ya ce , zaman makoki da irin wannan muzahara duk ta’aziyya ce zuwa ga Manzon Allah, domin shine wanda aka cutar, kuma wannan ya faru tun bayan wafatinsa.ya kara da cewa, bayan wannan ta’addanci ,an tafi  da zuriyar Manzon Allah mata da kananan yara  da suka  yi saura daga filin Karbala  zuwa Sham fadar Yazidu dan Mu’awiyya (LA) a kasa ana tafe ana tozarta su a duk garin da aka wuce ta cikinsa. ya ce, sakamakon wannan ta’addanci ne Allah ya sallada  ma musulmi Kaskanta  a hannun Magolawa kafiarai  abin da ya tafo har wannan zamani da musulmi suke cikin kaskancin Kafiran duniya.

Sannan ya ce, lokacin dawowar musulmi akan lamarinsu na addini ya yi,domin addinin ne zaya hada su waje daya. Sai ya ce, dole ne abinda ya dami Manzo ya dame ka, kuma dole ne ranar bakin cikinsa kaima ta zama rana ce ta bakin cikinka idan dai har Manzon kake bi kai ba munafuki bane ba kai
.
Malam Yakubu ya nasihanci masu sukar abinda muke yi da ganin ba daidai bane, da su binciki littattafansu indai har da gaske suke yi ba munafunci bane.Ya kara da cewa, Allah ya kawo lokacin da za’a gane abinda aka yi ma wadannan bayin Allah, kuma ko bamu nan  ga ‘ya’yanmu nan zasu ci gaba da wannan al’amari.”Ya nasihanci malamai da su ji tsoron Allah, su tsaya ma gaskiya domin jama’a suna kallonsu, ya ce “wannan lamari na Shi’a yazo zama ne”.

Ya kuma ja kunnuwan mahukunta dake hankoron hanawa ko afkama wannan lamari da cewa,”wannan Shi’a din ita ce ajalin gwamnatin wannan kasa, sai ya gargade su da cewa”su ja bakinsu su tsuke, su sama wannan al’amarin  ido, “idan kuma kuka ce ba haka ba,  za ku yi rigima ne da al’umma, domin al’umma adalci take so kuma a addini ne ake samunsa,  ya kuma ce,” babu wanda zaya fahimci wannan gida na Annabi, sannan ya rabu da shi . “idan ba za ku zo ayi da ku ba, kusa ido.Kawo jami’an tsaro da kuke kokarin yi  kuma ku yi ta kawowa, kuna amfani da zahirine shi kuma Allah yana amfani ne da zukata.

 Ya kare da cewa, da Imamu Husaini bai tashi ba da yanzu ba addini ne ake yi ba , domin su Umayyawa sun shirya maido da Jahiliyyar da Manzon Allah ya kawar ne, mikewar Imam it ace ta tsaida su.

Ita dai wannan muzahara, dubunbubatar ‘yanuwane maza da mata da kananan yara suka gabatar da ita a cikin yanayi na juyayi da nuna bakin cikin abinda aka yi ma zuriyar Manzon Allah bayan rasuwarsa.









Friday, December 2, 2011

WASU DAGA CIKIN HOTUNAN KARATUN ASHURA DA MALAM YAKUBU YAHAYA KE GABATRWA NA WANNAN SHEKARA TA 1433











DA'IRAR 'YANUWA MUSULMI TA KATSINA TA FARA GABATAR DA KARATUN JUYAYIN ASHURA NA SHEKARAR 1433 A.H

A ranar Assabat 1/1/1433 ne, Da’iarar ‘yanuwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky(H) ta Katsina  karkashin jagorancin Malam YakubuYahaya ta fara zaman makokin domin jajanta ma Manzon Allah (S) akan kisan da  makiya suka yi ma jikokinsa a Karbala.

A gabatarwar da ya yi kafin fara karatun,  Malam Yakubu ya ce, manufar wannan zama na makoki shine jajanta ma Manzon Allah(S), A’imma(AS) dasauran bayin Allah managarta akan zagayowar wannan musiba domin dole ne son Iyalan Manzon Allah saboda irin al’khairan da ya zo ma al’umma  da shi”dole ne ka nuna farin cikinka  akan duk abinda ya faranta ma Manzo da Iyalansa, haka kuma, wajibi ne nuna bakin ciki kan duk abinda ya bakanta masu” sai ya bukaci jama’a da basu fahimci abin da muke yi ba su bamu uzuri domin muna sauke wajibin da ya hau kanmu ne.”Malam Yakubu ya yi nuni da cewa,”zamu bi salon da muka saba bi ne na karanta littafan magabata domin sauran jama’a da zasu saurara suma su amfana” sannan ya ce,dukkan abinda ya faru  a wannan waki’a, ba kire bane ba kuma kage, sai dai muna karantawa ne daga littafai da aka rubuta su tsawon shekaru kuma a mabambantan garuruwa da zamunna domin mu amfana da  tarihi, don yin aiki da kyawawan dabi’u da watsi da munana.”

Malam Yakubu ya tabo tarihin gasar dake tsakanin Kuraishu da Hashimawa da yadda Hashimawa suka yi fice, abin da ya sa sauran Kabilun suka nuna masu gaba da kiyayya musamman wadda Umayyawa suka nuna abinda ya tafo har zuwan musulunci sannan bayan yakokin da Manzon Allah ya jagoranta wanda Imam Ali(AS) ya kashe mayan kafiran Kuraishu, sai gabar ta karu tsakainsu da Zuriyar Annabi abinda ya yi sanadiyyar kisan gillar da Yazidu (L) ya yi ma Imam Husain(AS) da zuriyarsa da magoya bayansa a Karbala domin ya dauki fansa.

 Kafin nan,sai da Malam Yakubu ya karanto tarihin da ke nuni da cewa, asalin Abdussamshi wanda ya  haifi Umayyam, mutumen Rum ne da aka kamo sa a matsayin bawa daga bisani aka mayar da shi da -ta hanyar Tabanni-
sannan shi kuma   Mu’awiyya ba dan Abu Sufyanu ba ne na hakika sai dai da ne ga wani da ake ce ma Musafiru wanda ya samar da cikinsa ta hanyar nema dake tsakaninsa da Hindu,wadda abu sufyanu ya aure ta bayan samun cikinsa.

Sanna ya bukaci jama’a su binciki tarihidomin sanin gaskiyar abinda ya faru tare da sanin asalin gabar su Abu-Sufyanu da Zuriyar Manzon Allah(AS).

Ya yi fatan za a kamala wannan zama tare da fatan wannan jaje ya zama karbabbe gami da fatan tabbata a wannan harka ta Musulunci.


DANDALIN MATASA YA KAI ZIYARA A GARIN JIIYA


 A yunkurin da yake yi  na fadada ayyukansa, dandalin Matasa na harkar Musulunci  a da’irar Katsina da kewaye,ya kai ziyarar murnar zagayowar Idul Gadeer na wannan shekara a garin Jibiya a ranar Talata 26/12/1432.


Da yake bayyana manufar wannan ziyara, danuwa Shamsuddini Ahmad  wanda daya ne daga cikin jagororin wannan Dandali a Katsina, ya ce, wanna  ziyara na da nufin ankarar da matasa  ‘ya’yan ‘yanuwa na Jibiya ne  tare da jawo su a jiki domin sauke nauyin wanna  Harka da ya rataya  a wuyansu a matsayinsu na manyan gobe ta hanyar danfara su da harkar tare da isar da ita ga abokansu na cikin gari

Malam Iliya Jibiya wakilin ‘yanuwa almajiran Sayyid Zakzaky(H) shine ya gabatar da takaitaccen jawabin maraba ga bakin wanda a ciki ya bayyana bukatuwar da gwagwarmayar nan keda ita ga matasan kasantuwarsu masu jini a jiki da zaya basu damar tsayuwa akan ayyukan tallafama al’umma, sannan ya ce,kasantuwarsu matasa suna da cikakkiyar damar gabatar  da Ibada zuwa ga maliccinsu sannan ya neme su su dage akan Imani da bauta ma Allah (T) da kuma gwagwarmayar tabbatar addini domin tsamo al’umma daga halin da azzalumai da zalunci ya saka su a ciki.ya yi tir da dabi’ar wasu matasan da mamakin kin halartar al’aummurran addini, ta yadda bazaka iya bambance su da sauran abokai  da basu da fahimtar addini. sannan ya nemi matasan su dage wajen neman ilimin addini da  zamani don fahimtar halin da ake ciki musaman ma a wannan zamani na dunkulewar duniya. Ya yi fatan dandalin zaya rika aike matasansu da duk wata gayyatar  wani taro nasu na wannan harka.

Shidai wannan dandali na matasa a wannan yanki na Katsina ya na iya kokarin hada kan matasan na wannan harka dake sassan da’irori domin su fahimci bukatar dake da akwai ta maido hankulansu domin halartar duk wasu al’amurra na addini da harkar ke gabatarwa tare da aiwatar da ayyukan taimakon jama’a kamar yadda Sayyid Zakzak(H) ke kira akai.





Sunday, November 20, 2011

DANDALIN MATASA YA GABATAR DA TARON MURNAR ZAGAYOWAR RANAR DA MANZON ALLHA YA NADA WAKILINSA


Dandalin matasa Na harkar musulunci a karkashin jagorancin Sayyid Ibarahim Zakzaky(H) dake garin Abukur dake karamar hukumar Rimi ta jihar Katsina sun gabatar da taron tunawa da Idul Gadeer a harabar makarantar Fudiyyah Islamiyya dake garin na Abukur a ranar Assabat 23/ 12/ 1432.


Malam Aminu Jakara wakilin ‘yanuwa almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) na Da’irar Rimi ne babban bako da ya gabatar da jawabi a wannan taro, ya bayyana wannan Idi na gadeer da cewa shine babban Idi kamar yadda aka tambayi Imam Ja’afarus Sadiq (AS) ko akwai wani Idi bayan idin karamar salla da babba da ake dasu , inda ya amsa da cewa, akwai wanda ya fisu, shine idil Gadeer watau ranar da Manzon Allah(S) ya ayyana Imam Ali (AS) wakilinsa bayansa.

Malam Aminu ya bayyana cewa, samun kanka a cikin wadanda suka yi wila’a ga Iayalan gidan Annabi ba dubararka ba ce, ni’ima ce daga Allah (T), domin wasu suna gaba ne da su, don  haka ya zama wajibi gode ma wanna ni’ima ta hanyar yin aiki.Ya ce kallon ayyukan  Sayyid Zakzaky (H) da kyakkyawar fahimta da aiki akan abinda Sayyid din ya ke kira akansa yana daga cikin godiya da wannan ni’ima.

Sai ya yi kira ga Matasan da su ribanci wannan lokaci na su na kuruciya kafin damar ta kubuce masu. Ya kara da cewa, zaka iya rasa dukiya  da makamancin haka  kuma ka riske ta, amma idan rayuwarka ta zo karshe baka ribance ta ba, to zaka yi nadamar ayyukan da baka yi ba, haka kuma matashi zai yi nadama idan bai yi abinda ya kamata ba har tsufa ya riske shi.Sai ya jawo hankalin matasan da su yi amfani da damar da suka samu ta fahimtar addini su yi aiki na tallafama addinin kafin damar ta kubuce masu musamman wannan lokaci da al’umma take yayin addini. Sannan ya yi kira ga matasan  da su rika tunanin  makoma Lahira domin kauce ma fadawa mummunar makoma a nan duniya da gobe kiyama. Ya shawarci matasan da cewa, kamata ya yi tunaninsu ya zama kaka  zasu taimaka ma al’umma ta fita daga wannan hali da take ciki na zalunci da rashin hukunci da littafin Allah. Sannan ya bukace su da s u kyautata dabi’unsu, su himmantu ga neman Ilimin addini da kauce ma tunanin tara abin duniya ko ta wane hali gami da sa tunanin tsamar da al’umma fita daga mawuyacin halinda   take a ciki na danniya. Sai ya yi fatan Allah ya kara taimaka ma matasan  wajen ganin sun tsayu akan yin abinda Sayyid (H) yake da fata akansa.

A tun farko sai da daya daga cikin jagororin dandalin matasan na Katsina, Shamsu ya gabatar da mai  jawabi inda ya bayyana makasudin wannan taro da cewa na taya juna murnar zagayowar ranar da Annabi (S) ne ya nada ma Al’umma  Imam Ali(AS)  matsayin jagora ne  a bayansa.

Kafin nan  sai da aka gabatar da wata tamsiliyya mai taken”da’awar  dandalin matasa” wadda ta yi nuni da rawar da y  kamata matasa su taka  wajen  janyo hankulan abokai akan su yi riko da addini tare da yin watrsi da duk wata dabi’ar da ta saba ma addinin.    






DA'IRAR YANUWA MUSULMI TA KATSINA TA GABATAR DA IDUL GADEER NA KWANA BIYU


Da irar ‘yanuwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky(H) ta  Katsina sun gabatar da taro na kwana biyu domin  murnar zagayowar ranar da Manzon Allah(S) ya ayyana magajinsa ga wannan al’umma watau Idil Gadeer  wanda wakilin ‘yanuwan na garin Malam Yakubu Yahaya ya gabatar a ranakun 20 da 21 ga watan Zulhijja  na wannan shekara ta 1432.

A zaman farko, Malam Yakubu ya karanto Hadisai ne masu dama daga cikin littafan magabata na Sunna  ba, da suke nuni da matsayi da fifikon Imam Ali (AS) akan sauran Saahabban Manzon Allah(S). Malam Yakubu ya ce, bamu ce sauran Sahabban Annabi basu da kima bane,sai dai abinda muka ce shine,daga Allah(T) sai Annabi A wajen daraja sannan sai Iyalan gidansa sannan Sahabbai suna bi masu a darja. Ya karanto HAdisan ne daga cikin littattafai irinsu Silsilatul-ahadisil maudu’ah ,al fada’ilu na Ahmad bn Hanbal, iqtibasu siradul mustaqima na ibni Taimiyyah da sauran Tafsirai da dama.Ya kara da cewa, ya kawo wadannan hujjoji ne domin tabbatar matsayi na Imam Ali(AS) domin masu musu su san cewa suna yin e da Manzon Allah(S), sannan ya kara da cewa, duk wadannan littattafai muna karanto sun e ba domin kkure basai domin mu gano gaskiya mu kuma yi riko da ita tunda matsaloli sun faru a wannan addini bayan wafatin Manzon Allah(S).

A rana ta biyu,Malam Yakubu ya karanto doguwar khudubar Manzon Allah wadda ya yi a wannan rana,ya karanto ta daga wasu littafai da suka kawo wani sashe na khudubar, sananan ya karanto ta a kammale daga ruwayar ahlul baiti(AS).
Ranar Gadeer, ran ace wadda Manzon Allah ya nada Imam Ali (AS) da umurnin Allah a matsayin Khalifarsa bayan wafatinsa.

A rana ta biyu bayan kammala wannan karatu, Malam Yakubu ya jagoranci  yanka cake na murnar wannan biki wanda ‘yanuwa na Acadamic forum suka tanada.An kamala wannan taro cikin nasara kamar yadda aka tsara tare da fatan Allah ya nuna mana zagayowar na badi.