A jiya Alhamis ne aka kawo karshen tarurrukan mauludin Fatima(AS) da 'yan'uwa mata na Da'irar Katsina da kewaye suka shirya.
Malam Yakubu Yahaya ne ya rufe wannan biki da karanto wani yanki da Hudubar Sayyida da ta yi a gaban Halifar musulmi Abubakar bayan hana ta hakkinta da aka yi bayan wafatin Manzon Allah(S).
Ba muna jin dadin
karanto abubuwan da suka faru bayan wafatin Manzon ba ne, sai dai muna
karantawa don mu san inda gaskiya ta ke , mu yi riko da ita ,mu kuma ji inda
karya ta ke, mu bar ma masu karyar
abinsu.Malam Yakubu a wajen karatun Kammala Mauludin Fatima da ‘yan’uwa
mata suka shirya a katsina
A karshe Malam Yakubu ya yi fatan Allah ya karba mana ya
tabbatar da mu bisa shiriya, ya kuma nuna mana na wsu shekaru masu zuwa. Ya
kuma yi fatan Allah ya saka ma kowa da alheri musamman wadanda suka shirya da kuma wadanda suka taimaka har abin ya yiwu.