Sadaukar da
jini don bayarwa ga masu bukatarsa a irin wannan lokaci na nuna juyayin Ashura
kamar zaburantarwa ne a gare mu, dokmin Imam Husaini (AS)ba jininsa kawai ya
sadaukar ba, yama sadaukar da rayuwarsa ne gaba daya data iyalansa dama Sahabbansa.Malam
Yakubu Yahaya wakilin ‘yanuwa musulmi
almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky(H) na katsina ya b ayyana haka a lokacin da
yake tattaunawa da wakilinmu a yayin bayar da jini da ‘yanuwan suka yi
albarkacin sadaukarwar Imam Husaini(AS).
Malam Yakubu
yahaya ya bayyana cewa, “an san muhimmancin bayar da jini a wannan zamani,
domin shi jini jigo ne a rayuwa, shi yasa ma zaka ga ana farautar jini harma da kudi domin mutane
su samu su rayu, musamman yayin bukata,
ko saboda haihuwa, hadari da makamantansu. Shi ya sanya masana suka muhimmantar
da bayar das hi.”Sai ya karfafa bukatar bayar da jini muddin hakan zaya amfanar
da dan Adam.
Ta fuskacin
addini, malam Yakubu ya bayyana cewa, idan mutum ya bayar da jini aka ceto
rayuwar mutum daya, ladar da zaya samu kamar ya ceto rayuwar al’umma ne baki
daya.Ya karfafa maganar da ayar nan dake nuni da cewa, ‘wanda ya kasha rai, kamar ya kasha rayuka ne baki
daya, wanda ya raya rai daya, ,kamar ya raya rayuka ne gaba daya” Ya kara da
cewa, ba a la’akari da wanene kaba jinin musulmi ne,ko ba musulmi ba,in dai
sunan sa rai, za a bas hi jinni domin ya
rayu, idan yaso shi ya yanke ma kansa hukuncin zabin abin da zaya yi.
Malam Yakubu
ya tabbatar da cewa, bayar da jinni yana kara lafiyar mutum,sannan kuma ta
hanyar bayarwar za a iya fahimtar yanayin lafiyar mutum ta yadda idan mutum
yana da wata matsala, za a iya shawo kanta cikin sauri ba tare da ta ketara
zuwa ga wani ba.’ka gay a sami lada kuma ya san matsayin lafiyarsa’ daga nan
sai malam Yakubu ya karfafa sadaukar da jinin da cewa, ba sai lokacin Ashura ba
ne kadai za a iya bayarwa, a’a akwai bukatar mutum ya bayar idan akwai
bukata matukar dai za a iya yin
hakan.Sai ya yi fatan ganin Allah ya kai
mu lokacin da zamu bayar da rayuwar mu gaba daya domin daukar fansar zaluncin
da aka yi ma Imam Husain(AS).
Likitan da
yake jagorantar kungiyar karbar jinin da rabashi ga mabukata a wannan aikin, Dakta
Iisma’il Buhari, kira ya yi ga jama’a da suke dari-darin bayar da gudunmuwar
jini da cewa, bayarwar ba bata da wata matsala, domin ba haka nan ake dibar
jinin mutum ba har sai an gabatar da tambayoyin da za su kai ga fahintar cewa,
za a iya dibar jinin mutum lafiya lau ba tare da ya sami wata matsala ba, idan
kuwa aka fahinci cewa, dibar zata haifar masa da matsala, to bama za a diba ba.
Sai ya nemi
sauran jama’a da a daure a rika bayarwa,
domin bayarwar abu ne mai muhimmanci, saboda ceton rayuwa. Ya kara da cewa,
‘abin lura shi ne, idan jama’a basu bayar da wannan gudunmuwa ba, to babu inda
za a je a samo shi.” Sai ya tabbatar da cewa,bayarwar ba matsala ba ce sai ma
lafiya ta za a kara samu. ‘kodai mutum ya bayar, ko bai bayarba, jinin
yakan lalace a cikin kowane wata Allah ya sake samar da wani’Sai ya yaba ma
‘yanuwa musulmi da suke kokarin
tallafawa da jinin kyauta ba tare da ana biyansu kudi ba.
Malam Abdul
karim Usamatu, shi ne wanda yake jagorantar kwamitin ISMA a
wannan yanki, ya bayyana karuwar jama’a
da suke bayar da wannan gudunmu da cewa, ‘ fahimtar muhimmanci bayarwar ne da jama’a suke yi sakamakon bayanin da
kwamitin yake yi lokaci-lokaci musamman lura da suke yi cewa, bayar da jinin
ibada ne sannan kuma yana kara lafiya ne ga duk wanda ya bayar.
A bana dai
adadin wadanda zasu bayar da jinin ya
nunka na bara idan aka lura da al’kalumman da kwamitin kiwon lafiya na harkar musulunci (ISMA) ya tattara a
wannan shekara.