Saturday, December 22, 2012

AN BUDE BANGAREN ISLAMIYYA NA MAKARANTAR FUDIYYAH KATSINA



A ranar Laraba 6/2/1434 ne aka  bude bangaren karatun Islamiyya a makarantar Fudiyya dake Katsina.
Da yake gabatar da jawabi a wajen bikin,Malam Yakubu Yahaya wakilin ‘yanuwa almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) na garin Katsina, ya bayyana godiya ga Allah (T) ne Daya bada wannan dama da aka samu na koyar da yara wannan addini wanda shi ne makasudin zowar dan Adam a wannan duniya, kamar yadda Allah (T) ya fada a littafinsa mai tsarki.ya ce ,sai ka san addini ne zaka  san abinda zaka iya saka ma jikinka,sai ya bayyana ilimi da cewa, ba karamin al’amari ba ne,inda ya nuna cewa, duk abinda yak e a wannan duniya , ilimi ne ya samar da shi,sannan ya kara da cewa, sabo da muhimmancinsa ne ,Allah ya umurci Manzonsa da ya roki Karin ilim, kamar yadda ya zo a littafin mai tsarki na al-Qur’ani.Sai ya yi kira da cewa,  bai kamata a bar mu a baya ba a wannan fage.
Malam Yakubu ya kara da cewa, tozarta addini ne ya haifar mana da matsalolin  da muke ciki,inda ya nuna takaicin yadda ake gudanar da al’amarin addini, ya bada misalin yadda al’umma take gabatar da ayyukan bauta  ba bisa ka’idar addinin ba. Kamar gabatar da Sallar magariba tun kafin faduwar rana ta shari’a, da sauran misalai da suka shafi karatun al-Qur’ani mai girma. Ya kawo misalai da dama dangane da haruffan Larabci da yadda suke bambanta da na Hausawa inda ya ce kusan yawanci Bahaushe yana gabatar da karatun sallar sa  da haruffan Hausa ne a madadin na Larabci, sai ya nuna wajabcin mu gyara wadannan matsaloli. Sannan  kuma Malam Yakubun ya yi kira da mu kawo yaranmu su koya yadda ya kamata.Sai ya bayyana kulen da al’ummar  musulmi suke fuskanta  na yunkurin dakile lamurransu na addini da iliminsu ta hanyar bullo da makirce-makirce a kowane lokaci ga kuma kulen gyara tsakanin mu da Mahalicci ta hanyar yin addininmu yadda yake.
Karshe ,malam Yakubu ya kira ga iyaye da su dage su tura yaransu a makaranta neman ilimi sanna suma iyayen su koma makarantar domin gyara abinda ya kubuce masu.
A tun farko. Shugaban makarantar Fudiyyah Malam Kabir Sani , ya bayyana makasudin bude wana bangare ne da cewa, domin ba yaranmu ilimin addini ganin cewa a makarantun book ba a ba ilimin Musulunci muhimmanci ba, sannan kuma a ba yaran kyakkyawar tarbiyya ta addini.

                                      

Sunday, December 9, 2012

AN KAMMALA ZAMAN MAKOKIN SHAHADAR IMAM HUSAINI(AS) A KATSINA


A ranar Talatar da ta gabata ne, aka kawo karshen zaman makokin Shahadar Imam Husaini(AS) wanda Da’irar ‘yanuwa almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) taKatsina ta shirya kuma wakilin ‘yanuwan Da’irar ta Katsina Malam Yakubu Yahaya ya kwashe kimanin kwana ashirin yana gabatarwa.
A wannan karatu na zaman makokin Imam Husaini(AS), Malam Yakubu ya kawo Dalilai da suka jawo wannan waki’a ta ashura, inda ya karanto daga cikin littattafan Ahlussunati, abubuwan da suka faru tun daga lokacin da Manzon Allah ya riski Rahamar Mahaliccinsa, inda ya karanto abubuwan da suka shafi warware bai’a ta hanyar canza nadi tare da zaben halifanci sabanin wanda Manzon Allah ya yi.
Bayan karantar yadda waki’ar ta Ashura ta faru, an kuma karanto abubuwa marasa dadin ji da addini ya gamu da su bayan kisan gillar da aka yi ma Imam Husaini(AS) kamar kisan Sahabbai da ruguza garin Madinar Manzon, yakar Makka tare da rusa Ka’aba ta hanyar jifar ta da majaujawa da rundunar Yazidu ta yi.
Bayan kammala karatun ne , aka yi addu’ar neman samun damar daukar fansar wannan ta’addanci da makiya Allah suka yi wai kuma da sunan su Musulmi ne. Sannan malam Yakubun ya yi kira ga musulmi da su karanci wannan addini na musulunci ta hakikanin koyarwar gidan Annabi, tun da dai wannan addinin Annabi Muhammad ne aka aiko da shi, kuma koyarwarsa tana nan tare da Iyalan gidansa.

Monday, November 26, 2012

MUZAHARAR ASHURA A KATSINA TA KAYATAR


“Imam Husain(AS) ya yi shahada ne tun bayan wafatin manzon Allah(S), dole ne mu tunatar da junan mu wannan, idan bamu fahimci haka ba, ba zamu fahimci abinda ya faru a Karbala ba” Malam Yakubu Yahaya wakilin ‘yanuwa almajiran Sayyid Zakzaky(H) ne ya bayyana haka a yayin rufe Muzahahar nuna jaje da alhini ga Manzon Allah da Iyalaansa masu tsarki   da aka  gabatar a ranar Lahadi 11/1/1434 sakamakon kisan gillar da makiyan Allah suka yi ma Imam Husaini dan Ali dan Abi Dalib(AS) a ranar goma ga Muharram da aka fi sani da ranart Ashura.
A yayin da yake rufe muzaharar, malam Yakubu wanda shi ne  ya jagoranci muzaharar har zuwa karasa ta, ya fara ne da  mika ta’aziyya ga
Manzon Allah wanda   ya ce,”muke da yakinin yana tare da mu, sannan  ga  Sayyida Zahara, Imam Ali (AS) da sauran Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka har ya zuwa ga Imamul Asr (AJ), sannan  ya mikata ga Sayyid Zakzaky (H), Sayyid khamina’I da Sayyid Nasrullah  da  sauran ‘yantattaun bayin  Allah. Sai ya jawo hankalin al’ummar musulmi da cewa, dole mu tunatar da juna wannan dominb idan ba a fahimci wannan ba, ba  za a ma fahimci abinda ya faru a Karbala’I din ba.sannan ya cxe, kafin ManzonAllah ya bar duniya, ya ayyana yadda dduniya zata zauna daidai, amma wadansu manzya suka fadi jarabawa kamarf yadda kowa zaya iya faduwa jarabawa saboda halayya irin ta dan Adam, haka suka fadi jarabawa ta hanyar canja wasiyyar da Manzon Allah ya yi ta wanda za a bi bayan wafatinsa. Ya ce, “Manzo ya ce, ku yi biyayya ga Imam Ali(AS) da yin jihadi da saurarensa, sai  suka canja bayuan wafatin,suka yi, jihadin sukja koyar da karatau da yada addini, amma ba bayan wanda Manzo ya ce ba, a karshe ma suka kashe Imam Alin, haka kuma suka kashe  Imam Hasan sannan wanda ya gada daga baya ya kashe Imam Husaini (AS). Ya kara da cewa, bayan kauce ma waccan wasiyya ce, Imam Husaini ya fita domin kawo gyara,kuma wannan shi ne sanadiyyar kashe shi  kisan wulakanci Kisa irin na rashin mutunci. Ya yi nuni da cewa, wadanda suka kashe Imam Husaini muslmi ne wadanda suka sauya daga turbar da Manzon Allah ya shata suka yi wani abu daban kuma wannan shi ne ya kai mu halin da muke ciki a halin yanzu.Malam Yakubu nya tabo irin yadda aka wulakanta jikokin Manzon Allah  a wannan fili na Karbala cikin yanayi na  tursasawa da kishirwantarwa domin an hana su ko ruwa ma su kurba, sannan bayan an karkashe su aka iza kiyarsu gaba ana wulakanta su, cin mutunci ta tozartawa. Ya ce, duk wadannan abubuwa suna nan cikin littattafan tarihi a rubuce, kjuma wannan wai shi ne sunna.Sannan y ace Allah ya yi mana baiwa da wanda ya haska mana , ya fahimtar da mu yadda abin yake. “dadewa akan ba daidai ba, baya mayar da abin daidai, a komo kan daidai” in ji shi.
Malam Yakubu ya ce, Allahya so ya kuma ga dammar maido da addini kamar yadda ya ce” domin ya bayyanar da addini akan dukkan addinai ko da kafirai sun ki” to lokacin yin hakan ya yi.Sannan y ace waki’ar Karbala bayan shekartu dbu da kimanin dari kusan hudu, yanzu ta motsa zukata, ta kuma nuna cewa, lallai irin abin da Imam Husaini ya yi, shi ne ya kamata al’umma ta yi domin kwatar kai daga  zalunci.
Sai ya yi kira ga musulmi su dawo kan saiti , madamar ba a saita ba, to za ayi ta tafiya akan addinin da Mu’awiyya ya gina wasu suka zo suka gadsa ake ce masaa sunna wal jama’a, sai ya ce “dole tunani ya canza.”
Ya nuna takaicin yadda malamai suka koma kayan aikin hukumomi sakamakon irin wannan koyarwa ta Umayyawa.Ya nuna yadda ake rayuwa a wannan kasa, inda yace da akwai gara,da sai ace4 gara kafircin Yazidu da na wannan kasa, domin shi kafircin Yazidu an yi masa rumfa ne da cewa, musulunci har ma an ace ma Yazidun sarkin Musulmi, amma shi mkafircin Nigeriya bai yarda da Qur’ani ba, bai yarda a buda Qur’anin ba ace Allah ya ce ba.Don haka akwai matsala babba inji Malamin.Ya kara da cewa, a loikacin Yazidu ana zuwa jihadi, amma na wannan kasa, dan musulmi ne zaya buda bakinsa ya ce babu ruwansa da addini.”don haka kafirci  ake yi a wannan kasa, mahukuntan wannan kasa kafirci suke jagoranta, kuma wanda duk ya mutu yana biyayya ga kafirci, zaya karba tambayta gaban Allah (T) kujma baya da amsa, saannan kada murtum ya dauka da saauki, babu sauki.
Sai ya kamala da cewa, “abinda yasa mu ka dauki wannan hanya, shi ne domin mun yanke kauna akan gyaruwar wanna  kasa, shi yasa muka zabi hanyar komawa lahira, kuma zamu iya tunkarear kowace hanyar zuwa lahira, idan akwai ja ,ko baka ko fara ko dorowa, to shirye muke mu tunkare ta, saboda mun riga mun yanke shawara, dam nu yi asarar lahira, gara mu yi asarar  duniya, idan ma zamu ga wanda yake so ya aika mu lahirar, muna maraba da shi, wannan shi ne abinda shugabanmu Sayyid Zakzaky(H) yak e ce mana, idan muka ga inda ake bude wuta , mu sa kai wajen”Sannan y ace wannan shi ne mafitarmu, idan Allah ya ga dama ya wanzar mana da addini, mu bauta ma Allah, idan kuma yagta dama ya yi mana irin na Imam Husaini, to mu bamu kai sharer takalmin Imam din ba, amma maganar biyayya ga kafircin waannan kasa na dad a na yanzu , ba bu domin dai sun riga sun yi asarar mu da duk zuriyarmu,”
Muzaharar wadda aka kwashe kimanin awa uku da rabi ana gabatar da ita ta kewaye manyan titunan birnin Katsina cikin natsuwar da take dauke da sakon nuna juyayi akan cin mutuncin da aka yi ma Manzon Allah a bayan wafatinsa, kusan dukkan wadanda suke a sahun muzahgarar suna tafe ne suna rera wakokin jaje wasuma suna tafe ne suna zubar da hawaye na nuna alhinin musibar da ta sauka ma iyalan Annabin Rahama(S) a wannan ranar ta Ashura.
Al’ummar garin Katsina  dfa dama sun  taya ‘yanuwa wannan juyayi, a lokacin da ake aiwatar da ita wannan muzahara.


AN GABATAR DA KARATUN IDUL GHADIR NA KWANA UKU A KATSINA


 
 Kimanin kwana ukku aka kwashe ana gabatar da tarurrukan tunawa da munasabar  Idil Ghadir, domin tuna ma al’ummar musulmi wasiyyar da Manzon rahama ya yi a hajjin bankwana ,a ranar 18 ga watan zulhijja  bayan da ya kammala aikin  hajji  zaya koma Madina, taron da Da’irar ‘yanuwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky(H) ta Katsina ta shirya tare da gabatar da shi tun daga ranar Talata 21 har zuwa Alhamis 23 ga zulhajjin wannan shekara ta 1433.

A wannan taro Malam Yakubu Yahaya ya gabatar da karanto falalolin Iyalan gidan Manzon  Allah Musamman Imam Ali(AS) domin al’umma ta fahimci irin matsayinsa da jarumtakarsa hada da ilimin da Allah ya bashi domin dai ya zamo Halifar Manzon Allah bayan wafatinsa. Haka kuma a wannan biki, malam Yakubu ya karanto doguwar hudubar da Annabin rahama ya karanta a wancan lokaci.
Bayan kammala karance-karancen ne, malam yakubu ya ankarar da al’umma cewa, wannan al’amarin da ya faru na bijire ma wasicin Annabi da wasu suka yi, ba ana karantawa ba ne domin ana kiyayya da wasu kamar yadda wasu suke gani, a’a saidai ana karantawa ne domin al’umma ta san hakikanin sakon da wadanda aka ce abi bayan wafatin Manzon.
A jawabin nasa ya yi nuni da yadda sakamakon bijire ma wasicin aka kirkiro abubuwa na addini wadanda ba Manzon Allah ne ba  ya yi umurni da yinsu , inda ya bada misalin kiran salla biyu da ake yi a ranar Juma’a, abinda ya ce  mai Risala ya bayyana da cewa, banu Umayya ne suka kirkiro shi, haka kuma a kokarin rufe matsayi na Imama Ali(A) sannan ya ce, kimanin kashi saba’in da biyar  cikin dari na addini da ake yi  duk an kirkiro su ne bayan wafatin Manzon Allah duk dai domin ganin an kauce ma wasicin  bin Imam Ali (AS) , ya kara da cewa, akan haka ne ma Mu’awiyya ya tara malamai suka yi ta kirkiro Hadisan falalar wasu Sahabbai don rufe matsayuin Iayalan Annabi, wannan ya sa aka kwashe shekaru ana zagin Imam Ali(AS)  da Iyayensa , matarsa , ‘ya’yansa dama duk wanda ke binsa, Malam Yakubu ya ce, bayan zagin imam din wasu ma sun kara da yin izgili, inda halifa Mutawakkil yake yin shiga irin ta Imam Ali ya  fito fada , yadda da an gan shi sai ayi ta keta dariya waidai domin nuna izgili. Ya ce, Mutanen da Allah ya yi  Umurnin a girmama, sune aka  koma ana zagi da yi masu izgili.
Malam Yakbu ya bayyana cewa,akwai bukatar al’umma ta fahinci abinda muke cewa tunda addini muke yi, kuma shi ne zamu yi sannan mu tsira, kuma gaskiya tana nan sannan dole wannan gaskiya ce zamu yi. Sai ya tabbatar da cewa, tabbas an jaraba Sahabbai akan wannan lamari, wasu sun ci jarabawar wasu kuma  sun fadi kamar yadda aka jaraba wasu al’ummu suka fadi.sannan ya tabbatar da cewa, “ duk fa wanda ya gitta ma Manzon Allah. To fa zamu gitta masa kowanene, iyakar gaskiyar wannan Magana kenan, amma ba muna gaba da wani sahabi bane, basu  yi mana laifin komai ba, kuma basu bamu haushi  kuma Allah ya ba su, sun ga Manzon Allah, sun bi shi Sallah sun kuma yi jihadi  tare da shi ,amma daga baya wasu sun fadi jarabawa, wasu kuma sun ci. saboda haka wadanda suka ci jarabawa muna tare da su dari bisa  dari, wadanda suka fadi kuma al’amarinsu yana wurin Allah, amma dai mu, bada muba” sanna yace Muna fatan za a yi mana adalci kada aje ace mun zagi Sahabbai, domin abinda ke faruwa kenan a wasu masallatai. Ya ce, “ba babatu zaka yi ba, yadda na karanta littattafai  da hujjoji da dalilai , kai ma sai ka yi haka. Idan wani yana jin ba haka bane, shi ma sai ya tara mutane ya karanto masu littatafai da suke nuna ba haka ba ne.”
An dai kammala wannan taro da majalisin mawaka, inda mawakan gwagwarmaya suka hadu suka wake  munasabar Ghadir sannan aka rufe taro da addu’a tare  da  yin fatar Allah ya dawwamar da mu akan wilaya da Imam Ali(AS).

Saturday, October 6, 2012

AN KADDAMAR DA MAKARANTAR HARDAR AL'QUR'ANI MAI GIRMA A YANKIN KATSINA




Gatancin da zaka yi ma danka shi ne ka ba shi ilimi, musamman ma na addini.Malam Yakubu Yahaya ya bayyana haka a yayin kaddamar da  makarantar hardar alkur’ani mai girma da Da’irar ‘yanuwa Musulmi almajiran Sayyid Ibrahim ZakzakY(H) yankin Katsina ta gabatar a ranar 20 / 11/ 1433 a  matsugunnin  makarantar na gajeren lokaci da ke tsohuwar Markaz dake Unguwar vyari a cikin birnin Katsina.
A farkon jawabin nasa, Malam Yakubu ya tabo kadan daga cikin tarihin yadda aka fara gabatar da karatun harder al’Qur’ani tun daga lokacin Sahabban Manzon Allah, a lokacin da suka fahinci cewa, mahardatan al’Qur’ani suna karanta sakamakon Shahada da wasunsu suka yi a fagen fama.
Malam Yakubu ya ci gaba da bayyana cewa, al’Qur’ani shi ne jogon tafiya a wnnan harka ta Musulunci, shi ne kuma zaya gyara al’umma kamar yadda ya gyara al’ummomin baya.Ya tabo yadda turawa suka sami ci gaba sakamakon shiga kaashen musulmi da suka yi suka karanto ilmomi da malaman musulunci suka rubuta sakamakon karantar al’Qur’ani, sai ya nuni da cdewa da Bature bai zo ya yi mana barna ba, da yanzu mun kai wani matsayi na ci gaba.sai ya bayyana cewa, za a karantar da al’Qur’ani da manufar samar da ilimomi da fannoni daban-daban domin samar dam asana da suka san duniya kuma suka san Lahira.Ya ce,” za a koyar da duk wani fanni na ilimi, wannan shi ne gurinmu”
A wani sashen jawabin nasa,Malam Yakubu ya ankrar da dukkan ‘yanuwa cewa, kasancewar wannan makaranta ta fara ne a mazauni na gajeren lokaci kafin samar da mazaunin tan a dindindin, akwai bukatar ‘yanuwa su san da cewa, akwai aikin samar da wannan mazauni sannan kuma ga shirin samar da makarantar Sakandare ta Fudiyya da shi ma ake yunkurin yi domin samar da ingantaccen ilimi ga ‘ya’yanmu.Saai ya gode ma wadanda aka dora ma nauyin ganin an fara wannan karatu sannan ya bukaci iyaye das u koma makaranta domin gyara ma yaransu duk wani nkuskure da zasu yi a lokacin da suke bita a gida, domin wanda baida abu ba zaya iya bayar da shi ba.
A karshe, Malam Yakubu ya nasihanci malaman wannan makaranta da yin hakuri da matsalolin da zasu iya fuskanta a yayin tafiyar da harkokin wannan makaranta.
A zantawar da almizan ta yi das hi, shugaban Lajnar makarantar ta Tahfizul Qur’ni, malam Shehu karkarku, ya bayyana cewa samar da wannan makaranta aiwatar da irshadin da sayyid Ibrahim Zakzaky(H) ne ya yi a shekaru biyu da suka gabata a kano yayin saukar karatu da aka gabatar, inda ya bukaci kowane yanki ya samar da irin wannan makaranta.
An kammalam wannan taro na kaddamarwa ta hanyar yanke zare da Malam Yakubu ya yi ,sannan ya fara karantar da yaran a matsayin fara karatu a wannan sashe na harder littafin Allah mai girma.