Tuesday, May 10, 2011

ISMA A KATSINA TA GABATAR DA WALIMA

Daga:Abdul'Karim

A ranar Larabar da ta gabata ne, yan-uwa na ISMA a Katsina suka gabatar da walimar kawo karshen ayyukan agajin da suka bayar sakamakon yajin aikin da hadakar kungiyar lafiya ta jihar ta kira na tsawon kwanaki talatin. Yajin aikin wanda ya share kwanakin wata guda cur a duk fadin jihar ya biyo bayan kin cika alkawurran biyan hakkokin ma’aikatan lafiya da gwamnatin jihar ta yi. Taron walimar ya sami halartar wakilan abokan aikin ISMA a yayin wadannan ayyuka a asibitoci wadanda suka hada da kungiyoyin agaji kamar Nigeria Red Cross Society, Hizbah Health Commitee, JNI First Aid Group, Hospital Friends a Markazin yan-uwa na Katsina.

Yan-uwa na ISMA sun bayar da ayyukan taimako a asibitin Katsina da Daura da Malumfashi da Dutsin-ma, kamar yanda Mallam Abdullahi Abubakar ya shaidawa mahalarta wannan walima. Yace, Yan uwa na ISMA sun sami gayyata ne daga hukumar gudanarwar babbar asibitin Katsina mai rokon cewa su kawo dauki a wannan asibibiti don agajin bayin Allah marasa lafiya. ISMA sun halarci wannan asibiti da wasu asibitocin jihar, har zuwa ranar 13th April, 2011, lokacin da aka kare wannan yajin aiki.
ISMA tare da wasu kungiyoyin agaji kamar Nigeria Red Cross Society, Hizbah Health Commitee, JNI First Aid Group, Hospital Friends da sauransu suka yi tarayya a wannan aiki na taimakawa marasa lafiyar da suka iso harabar asibitin da nufin a duba lafiyar su da wadanda yajin aikin ya rutsa da su a kwance masu karaya da wasu masu matsalolin haihuwa da sauran marasa galihun da basu da halin iya tafiya asibitocin kudi. Mallam Abdullahi ya cigaba da cewa, ISMA ta tsara ma’aikata masu gudanar da aiki a asibitin babbar birnin jihar inda suka tanadi ma’aikata masu kwarewar a ayyukan kiwon lafiya daban-daban kamar Registerd Nurses, Midwives, Community Heath Officers, Environmental Health Officers, Senior Community Extension Workers, Junior Community Extension Workers, Dental Surgeons, First Aiders wadanda aka rabawa ayyukan rike wannan asibiti daidai gwargwadon kwarewa. An tsara gabatar da “Shiftings” na safe da rana da dare da kuma sashen masu kula da tsaftar muhalli.


Babban bako a wannan walima Malam Yakub Yahya ya gabatar da jawabai masu ratsa zukata na karfafa ayyukan yan ISMA da yabo agaresu. Malamin yace, har kullum ina kwana da yinin fatar in zamo dan ISMA tun anan duniya, ko kuma in samu ceton yan ISMA a gobe kiyama. Yace, muddin yan ISMA su ka yi abinda ya dace to lalle babu wata kafa da harkar kiran Malam (H) ke da ita ta saurin yada kyawawan sakonnin wannan harka kamar sashen kiwon lafiya, saboda misalai da dama da suka gabata na rahama da ma’ikatan kiwon lafiya su ka samu. Ya bada misali da Sayyid Tabataba’i marubucin shahararen tafsirin nan mai suna al-Mizan wanda a kullum ya ke alfahari da taimakon lafiyar wani kare a matsayin sanadin samun daukakarsa a fagen ilimi. Mallam Yakub yace to kare kenan, ina ga wanda aikinsa shine son ganin mutane sun sami lafiya? Yace babu aikin da yafi yiwa al’umma hidima saurin daga martabar mutum a wajen Allah Mahalicci da samun karbuwa da tasirantuwa a zukatan mutane. Ya ce, lallai yan ISMA jakadun kwarai ne na wannan harka, ya kuma yi kira ga sauran yan-uwa almajiran Mallam (H) da su lizimci daukar dawainiyar sashen kiwon lafiya na wannan harka da nufin su samu nasu rabon da kason a cikin ayyukan alherin da sashen ISMA ke gabatarwa.


Shugaban sashen ISMA na yankin Malam Abdulkarim Usamah ya kara karfafa yan-uwa na ISMA da cewa har kullum a zamo cikin shirin tunkarar ire-iren wadannan ayyuka kamar yanda Maulanmu Sharfuddeen (H) ke horon mu da aikatawa kuma a sadaukar da gabatar da kome domin Allah. Yayi godiya ta musamman ga yan-uwa da wasu bangarorin harka wadanda suka taimaka masu har Allah ya kawo karshen wannan yajin aiki. Yayi addu’ar Allah Ya kara kariya da taimako ga Malamin mu Shaykh Ibraheem Zakzaky (H) wanda da koyarwarsa da umurninsa sashen ISMA ya samu kafuwa ya na gabatar da ire-iren wadannan ayyuka.


Wakilin yan agaji na JNI da wakilin Red Cross Society da wakilin Hospital Friends duk sun gabatar da takaitaccen bayanan yanda zamansu ya kasance tare da yan-uwa almajiran Mallam (H) a asibitin, sun nuna gamsuwa da jin dadi da fatar Allah Ya dore wannan zumunci na su da ISMA.

No comments:

Post a Comment