Monday, May 30, 2011

BUKUKUWAN MAULUDIN SAYYIDA AZZAHARA(AS) DA 'YANUWA MATA NA DA'IRAR KATSINA SUKA GABATAR

mediaforumkatsina


Kamar sauran takwarorinsu, ‘yanuwa mata almajiran Sayyid Zakzaky(H) na da’irar Katsina da kewaye sun gabatar da bukukuwan murnar zagayowar wata da ranar da aka haifi diyar shugaban halittun Allah Manzo Muhammad(S) Sayyida Fadima Azzhara(AS) ranakun Assabat 25/ 6/ da Lahadi 26/ 6/1432.

An soma gabatar da bukukuwan ne da gabatar da muzahara wadda su ‘yanuwa matan gami da ‘yan makarantun islamiyyu suka gabatar da ita tare da share fage da harisawa suka yi ma muzaharar. Kamar yadda aka saba , muzaharar ta bi wasu muhimman titunan garin katsina, inda ta zagaya su tare da rera wasu wakokin yabon Sayyida Azzahara(AS), an kuma aiwatar da ita cikin tsarin da su ‘yanuwa matan ne suka aiwatar da ita yayin da ‘yanuwa maza suka zama ‘yan kallo, abin da ya zama abin sha’awa ga al’ummar gari.Muzaharar an kawata ta da tutoci da sauran kayan ado dake nuna murna da zgayowar wannan lokaci.

A jawabin da ta gabatar bayan kammala muzaharar, Malama Safiya Kabir ta kawo wasu kadan daga darajojin Sayyida (AS) wadda daga ciki ta ce, ya isa daraja ,kasantuwar ita Sayyida itace wadda Allaha (T) ya hukunta cewa ita ce uwa ga limaman shiriya wadanda suke sune jagororin Addini bayan Manzon Allah(S), ta bayyana mamakin jin yadda wasu musulmi ke musanta irin wadannan darajoji na diyar Manzon Allah,sai ta yi kira ga al’ummar musulmi baki daya da su yi karatun addini domin sanin ainafin shi sakon na musulunci,amma ta yi karin bayani da cewa, idan mutum zaya yi karatun ya zama wajibi ya sami Malamai masu tsoron Allah wadanda zasu bayyana masu gaskiya kada su je wajen irin malamanda suke babatu da murguda ayoyin Allah suna dangana su ga azzaluman mahukunta, ta ce, irin wadannan Malamai ba zasu fadi ma musulmi da sauran jama’a gaskiya ba.

A ci gaba da bukukuwan, a ranar Lahadi 26/ 6/1432, sai kwamitin na ‘yanuwa matan suka ziyarci wasu daga cikin makarantun allo dake cikin garin Katsina, inda aka ziyarci makaranta hudu daya daga kowace shiyya ta garin. A duk makarantun da aka je, Malama Hajara Sani ta kan bayyana ma Malaman cewa, ana wannan ziyara ne domin tunawa da zagayowar watan haifuwar diyar Manzon Allah ne,watau Sayyida Fatima Azzahara(AS)sannan kuma ana yin wadannan ziyarori ne domin aikata shiryarwar Malam Zakzky(H).

Malaman sun bayyana jin dadinsu da wannan ziyara tare da bayyana farincikinsu gami da kyakkyawar fata ga Malam Zakzaky da yake aiwatar da wannan kira. A karshen ziyarar, an gabatar da kayututtuka

Na sabulai da Omo ga ‘yan makarantar yayinda ake bayar da abinc ga malaman domin neman albarka.

An kamala wannan biki ne da yammacin ranar ta Lhadi,inda bikin ya sami tagomashi dahalartarsa da Sayyid Khidir Kano ya yi. A jawabin day a gabatar Sayyid Khidir, ya fadakar da al’umma akan baiwa da falala da wannan baiwar Allah take da ita wadda yace Ta wuce Maza, kuma samunta ta faskara gare su, ya ce yana daga cikin falalolinta haifar diya da suka ilmantar da duniya,inda y ace duk wani ilmin da ake tunkaho das hi daga Imam Ja’afar yake .

A wani bangaren ya bayyana cewa duk da darajojin da Allah ya yi mata, shine aurenta da Imam Ali(AS) wanda Manzon Allah ya bayyana da cewa ba domin Alin ba da Fatima bata da mijin aure a nan duniya. Ya bayyana cewa duk da darajojin Da Allah ya bata.Sai ya yi kira ga wadanda basu san Fatima bad a su yi bincike su san ta su ji abinda ya faru da ita su tambaya ina kabarinta yake ne, a ina aka binne ta , mi yasa bamu taba jin wani ya je aikin hajji yace yaje kabarinta ba. Ya ce ya kamata aje ayi karatu ayi bahasi . Ya ce, ko sawa da tayi aka binne ta, akwai sako da take so Ta isar ma na baya su sani,tare da cewa bata dade ba bayan rasuwar Annabi ita ma ta rasu,”to wannan darasine aje ayi bincike a san halin da addini ya shiga bayan rasuwar Annabi.”

Ya yi fatan Allah ya saka ma wadanda suka shirya wannan biki na tunawa da haifuwar Sayyida(AS)
sayyid Khidr tare da Malam Yakubu Yahaya a wajen mauludin Sayyida zahara (AS)

'Yanuwa mata a wajen maulidin sayyida a Katsina


No comments:

Post a Comment