Monday, May 30, 2011

YANKIN SHAHID HAMZA YA GABATAR DA TARON KARAWA JUNA SANI NA WUNI DAYA

mediaforumkatsina
A ranar Lahadi 26/6/1432 ne, yankin Shahid Hamza na Mu’assasatus Shuhada’u shiyyar Katsina da kewaye shirya taron bita na wuni daya a Markazin ‘yanuwa musulmi dake Katsina ga ‘yanuwa dake dauke da masa’uliyyar tattaro hakkin shahidai, da niyyar ankarar da su nauyin day a rataya a wuyansu.


Malam Ibrahim Potiskum, ya jawo hankalin ‘yankwamitin da cewa , batun karbo infakin shahidai, babban aiki ne da ya doro akan ‘yan kwamitin sannan aiki ne mai falala, inda ya tabo muhimmancin kulawa da da ‘ya’yan shahidai tare da kulawa da tarbiyyarsu abinda ya alakanta da tattaro wadannan hakkoki na shahidai.Sai ya jawo hankalin ‘yan kwamitin da su kara kokari wajen sauke nauyin shahidan da iyalansu ta hanyar dagewa wajen karbo wadannan kudade a hannun ‘yanuwa ,ya yi kira ga ‘yanuwa da su fahimci muhimmancin wadannan hakkoki na shahidai ta hanyar biyan nasu da na iyalansu baki daya, inda ya kara da cewa, abin koyinmu Sayyid Zakzaky(H) haka ya yi a lokacinda kwamitin shuhada’u ya kai Masa ziyara, kuma ya biya na shekara ne baki daya. Ya kuma yi kira ga wakilan mu’assasa da su zama masu bayarda nasu hakkokin dunkule a farkon lokaci domin samun nasarar ayyukansu, bai dace ba kaje karbar kudin wani ba tre da ka sauke naka nauyinba.

A dan takaitaccen jawabin da ya gabatar, Dakta Mustapha Sa’id wanda yana daga cikin masu jawabi, ya yi kira ne da a kara dogewa wajen fadakar da ‘yanuwa muhimmancin sauke wannan nauyi na hakkin shahidai,inda yace kada a gajiya, domin al’amarin yana bukatar aita fadkarwa har jama’a su fahinci muhimmancin infakin na shahidai.

A nasa jawabin,Malam Shehu Dalhatu ya fara ne bayyna ma’anar Mas’uliyya da cewa aba ce dake nufin wani nauyi da aka dora maka , sannan yace kuma ita mas’uliyaabin tambayace;idan ba zaka iya ba,to ya kamata ka bayyana,ya ce wannan aiki na tara hakkin shahidai abu ne mai muhimmanci, kuma kin karbowa saryarda hakkin shahidai ne. Ya kara da cewa wannan wakilci na Malam a cikin ‘yanuwadomin shi ne ya samar da wannan mu’assasa ta shahidai.” Ya kara da cewa,”yi ma ‘ya’yan shahidai hidima yi ma shahidin ne domin shi maraya ne kuma yi masa hidima ba karamar falala bace, inda ya karfafa magananarsa da kawo kissoshin wasu da suka ciyar da dabbobi suka samu rahama da kuma wadda ta azabtar da kyanwa ta shiga wuta. Sai ya yi kira ga ‘yanuwa das u auna tsakanin wadannan domin su fahinci falala ta wannan aiki na tara hakkin shahidai.ya yi kira ga ‘yankwamitin das u rika karama ‘yanuwa haske da bayanai da suke samu daga Bakunan su sayyid Zakzaky(H), domin suna samun bayanai da sauran ‘yanuwa basa samu, kuma wannan zaya taimaka wajen kara fahimtar wannan lamari.Sai ya yi kira ga wakilan kwamitinda su yi aiki tukuru domin samun nasara.

A tun farko said a wakilai daga wasu garuruwa, suka bayar da rahotannin yadda suke gabatar da ayyukan nasu abin da ke da bukatar tashi tsaye daga wakilan ‘yanuwa na garuruwa wajen wayar ma ‘yanuwa kai a kodayaushe domin fahimtar wannan nauyi tare da sauke shi domin cimma abiubuwan da aka sa agaba.

Shidai wannan mu’utamar an tattauna ne akan bayanai da suka hada da ,ayyukan mu’assasa da kalu bale da ke akan yankwamitin,sai muhimmancin sauke mas’uliyya da kuma hanyoyin bunkasa kudin shiga(hakkin shuhada). Tuni dai aka kamala wannan taro kuma baki suka koma garuruwansu dauke da niyyar aiwatar da abubuwan da aka tattauna a wannan taro.

SHEKARU BIYU BAYAN SHAHADAR ALHAJI IBRAHIM HAMDALA CHARANCI

Kwamitin Ahlid duthur da Mu’assasatus shuhada’u sun gabatar da taron tunawa da shahadar Sahid Alhaji Ibrahim hamdala Charanci,Katsina a ranar Assabat 25/6/ 1432 a garin charancin jihar Katsina.


A jawabin da ya gabatar duk da yanayin ruwan sama da aka samu , Malam yakubu yahaya ya farad a yin jaje ga ‘yanuwa da kuma iyayen Shahidin .Sanna ya tunatar akan shahada, inda ya bayyana ta da cewa falala ce kuma Allah yake daukar daidaikun mutane ya basu.Ya kawo tarihin bayin Allah da suka nemi su sameta amma basu samuba, domin shahada ba kayan wasa bace, sai mutum ya maida tunaninsa zuwa ga Allah ya kakkabe duniya sanna idan Allah ya ga shi kadai ya ke nufi sai ya ba shi. Yace abinda yasa muke tsron mutuwa shine saboda muna da matsaloli ne,domin muna dauke ne da kayan laifi da bamu so mu hadu da Allah.

Da ya juya akan al’amarin wannan harka da Sayyid Zakzaky(H) yake yi ma jagoranci, Malam Yakubu ya bayyana cewa, wannan harka it ace lasisin na yanke matsalolin Lahira,kuma wannan harka ta ginu ne bisa yakini kuma ta faro ne daga tushe ,karancin ilmin al’umma da kuma malamai da muke rayuwa tare dasu ,suna suna gai ana iya yin addini ko yaya sako-sako duk yadda ya samu ba komi. sai ya nuna cewa addini ya umurci mutum ya tsayu ne kyam akansa kada mutum ya karkata zuwa ga azzalumai”ka tsayu kamar yadda aka umurce ka kada ka yi shisshigi, kuma kada ku karkata ga wadanda suka yi zalunci ma kawunansu sai ku shiga wuta tare da su” sai ya yi gargadin bin azzalumai masu tsara ma mutane dokoki sabanin na Allah(T) kuma yace wannan aya ta hada da wadanda suka yarda da sakon manzo domin ta nuna “da wadanda suka tuba tare da kai”.sai ya kara da cewa, bisa dabi’a wadanda suka yi riko da addini ya yi istikama , to abinda ya sami na farko na shahada da abinda ya sami wannan bawan Allah, Alhaji Ibrahim zaya same shi domin ba a kashe su ba sai saboda addinsu.”kowane alhairi akwai na sama das hi har sai an kasha mutum saboda Allah ,to wannan shine alkhairin da babu na sama da shi.”kamar yadda ya malam Yakubu ya karanto.Ya yi fatan Allah ya arzuta mu da samun shahada a wannan tafarki na musulunci.


Taron ya sami halartar Malam Yakubu Yahaya da ‘yan kwamitin mu’assasatus shuhada’u daga Zariya, dakta Mustapha Sa’id da Malam Ibrahim Potiskum da shugaban kwamitin na Katsina Malam Ahmad Abbas da wasu daga cikin ‘yankwamitin sai kuma kwamitin ah –ludduthur na yankin a karkashin jagorancin MAlam AbdulKarin Usama.

A jawabin da Malam Yakubu Yahaya ya gabatr saboda yanayin ruwan sama da aka tabka,

Malam Yakubu ya bayyana shahada da cewa babban matsayi ne da Allah yake ganin zuciyar mutum abinda ta kudurce wanda shi kadai ya sani sai ya arzuta shi da ita, ya kawo darajoji na shahidi,sannan ya gargadi ‘yanuwa da su tsayu kyam akan addini ko kadan kada a karkata ga azzalumai”kada ku karkata ga azzalumai sai wuta ta shafe ku sannan ba za a taimakeku ba” kamar yadda yake a littafin Allah al’kur’ani.Sai malam yakubu

BUKUKUWAN MAULUDIN SAYYIDA AZZAHARA(AS) DA 'YANUWA MATA NA DA'IRAR KATSINA SUKA GABATAR

mediaforumkatsina


Kamar sauran takwarorinsu, ‘yanuwa mata almajiran Sayyid Zakzaky(H) na da’irar Katsina da kewaye sun gabatar da bukukuwan murnar zagayowar wata da ranar da aka haifi diyar shugaban halittun Allah Manzo Muhammad(S) Sayyida Fadima Azzhara(AS) ranakun Assabat 25/ 6/ da Lahadi 26/ 6/1432.

An soma gabatar da bukukuwan ne da gabatar da muzahara wadda su ‘yanuwa matan gami da ‘yan makarantun islamiyyu suka gabatar da ita tare da share fage da harisawa suka yi ma muzaharar. Kamar yadda aka saba , muzaharar ta bi wasu muhimman titunan garin katsina, inda ta zagaya su tare da rera wasu wakokin yabon Sayyida Azzahara(AS), an kuma aiwatar da ita cikin tsarin da su ‘yanuwa matan ne suka aiwatar da ita yayin da ‘yanuwa maza suka zama ‘yan kallo, abin da ya zama abin sha’awa ga al’ummar gari.Muzaharar an kawata ta da tutoci da sauran kayan ado dake nuna murna da zgayowar wannan lokaci.

A jawabin da ta gabatar bayan kammala muzaharar, Malama Safiya Kabir ta kawo wasu kadan daga darajojin Sayyida (AS) wadda daga ciki ta ce, ya isa daraja ,kasantuwar ita Sayyida itace wadda Allaha (T) ya hukunta cewa ita ce uwa ga limaman shiriya wadanda suke sune jagororin Addini bayan Manzon Allah(S), ta bayyana mamakin jin yadda wasu musulmi ke musanta irin wadannan darajoji na diyar Manzon Allah,sai ta yi kira ga al’ummar musulmi baki daya da su yi karatun addini domin sanin ainafin shi sakon na musulunci,amma ta yi karin bayani da cewa, idan mutum zaya yi karatun ya zama wajibi ya sami Malamai masu tsoron Allah wadanda zasu bayyana masu gaskiya kada su je wajen irin malamanda suke babatu da murguda ayoyin Allah suna dangana su ga azzaluman mahukunta, ta ce, irin wadannan Malamai ba zasu fadi ma musulmi da sauran jama’a gaskiya ba.

A ci gaba da bukukuwan, a ranar Lahadi 26/ 6/1432, sai kwamitin na ‘yanuwa matan suka ziyarci wasu daga cikin makarantun allo dake cikin garin Katsina, inda aka ziyarci makaranta hudu daya daga kowace shiyya ta garin. A duk makarantun da aka je, Malama Hajara Sani ta kan bayyana ma Malaman cewa, ana wannan ziyara ne domin tunawa da zagayowar watan haifuwar diyar Manzon Allah ne,watau Sayyida Fatima Azzahara(AS)sannan kuma ana yin wadannan ziyarori ne domin aikata shiryarwar Malam Zakzky(H).

Malaman sun bayyana jin dadinsu da wannan ziyara tare da bayyana farincikinsu gami da kyakkyawar fata ga Malam Zakzaky da yake aiwatar da wannan kira. A karshen ziyarar, an gabatar da kayututtuka

Na sabulai da Omo ga ‘yan makarantar yayinda ake bayar da abinc ga malaman domin neman albarka.

An kamala wannan biki ne da yammacin ranar ta Lhadi,inda bikin ya sami tagomashi dahalartarsa da Sayyid Khidir Kano ya yi. A jawabin day a gabatar Sayyid Khidir, ya fadakar da al’umma akan baiwa da falala da wannan baiwar Allah take da ita wadda yace Ta wuce Maza, kuma samunta ta faskara gare su, ya ce yana daga cikin falalolinta haifar diya da suka ilmantar da duniya,inda y ace duk wani ilmin da ake tunkaho das hi daga Imam Ja’afar yake .

A wani bangaren ya bayyana cewa duk da darajojin da Allah ya yi mata, shine aurenta da Imam Ali(AS) wanda Manzon Allah ya bayyana da cewa ba domin Alin ba da Fatima bata da mijin aure a nan duniya. Ya bayyana cewa duk da darajojin Da Allah ya bata.Sai ya yi kira ga wadanda basu san Fatima bad a su yi bincike su san ta su ji abinda ya faru da ita su tambaya ina kabarinta yake ne, a ina aka binne ta , mi yasa bamu taba jin wani ya je aikin hajji yace yaje kabarinta ba. Ya ce ya kamata aje ayi karatu ayi bahasi . Ya ce, ko sawa da tayi aka binne ta, akwai sako da take so Ta isar ma na baya su sani,tare da cewa bata dade ba bayan rasuwar Annabi ita ma ta rasu,”to wannan darasine aje ayi bincike a san halin da addini ya shiga bayan rasuwar Annabi.”

Ya yi fatan Allah ya saka ma wadanda suka shirya wannan biki na tunawa da haifuwar Sayyida(AS)
sayyid Khidr tare da Malam Yakubu Yahaya a wajen mauludin Sayyida zahara (AS)

'Yanuwa mata a wajen maulidin sayyida a Katsina


Tuesday, May 10, 2011

ISMA A KATSINA TA GABATAR DA WALIMA

Daga:Abdul'Karim

A ranar Larabar da ta gabata ne, yan-uwa na ISMA a Katsina suka gabatar da walimar kawo karshen ayyukan agajin da suka bayar sakamakon yajin aikin da hadakar kungiyar lafiya ta jihar ta kira na tsawon kwanaki talatin. Yajin aikin wanda ya share kwanakin wata guda cur a duk fadin jihar ya biyo bayan kin cika alkawurran biyan hakkokin ma’aikatan lafiya da gwamnatin jihar ta yi. Taron walimar ya sami halartar wakilan abokan aikin ISMA a yayin wadannan ayyuka a asibitoci wadanda suka hada da kungiyoyin agaji kamar Nigeria Red Cross Society, Hizbah Health Commitee, JNI First Aid Group, Hospital Friends a Markazin yan-uwa na Katsina.

Yan-uwa na ISMA sun bayar da ayyukan taimako a asibitin Katsina da Daura da Malumfashi da Dutsin-ma, kamar yanda Mallam Abdullahi Abubakar ya shaidawa mahalarta wannan walima. Yace, Yan uwa na ISMA sun sami gayyata ne daga hukumar gudanarwar babbar asibitin Katsina mai rokon cewa su kawo dauki a wannan asibibiti don agajin bayin Allah marasa lafiya. ISMA sun halarci wannan asibiti da wasu asibitocin jihar, har zuwa ranar 13th April, 2011, lokacin da aka kare wannan yajin aiki.
ISMA tare da wasu kungiyoyin agaji kamar Nigeria Red Cross Society, Hizbah Health Commitee, JNI First Aid Group, Hospital Friends da sauransu suka yi tarayya a wannan aiki na taimakawa marasa lafiyar da suka iso harabar asibitin da nufin a duba lafiyar su da wadanda yajin aikin ya rutsa da su a kwance masu karaya da wasu masu matsalolin haihuwa da sauran marasa galihun da basu da halin iya tafiya asibitocin kudi. Mallam Abdullahi ya cigaba da cewa, ISMA ta tsara ma’aikata masu gudanar da aiki a asibitin babbar birnin jihar inda suka tanadi ma’aikata masu kwarewar a ayyukan kiwon lafiya daban-daban kamar Registerd Nurses, Midwives, Community Heath Officers, Environmental Health Officers, Senior Community Extension Workers, Junior Community Extension Workers, Dental Surgeons, First Aiders wadanda aka rabawa ayyukan rike wannan asibiti daidai gwargwadon kwarewa. An tsara gabatar da “Shiftings” na safe da rana da dare da kuma sashen masu kula da tsaftar muhalli.


Babban bako a wannan walima Malam Yakub Yahya ya gabatar da jawabai masu ratsa zukata na karfafa ayyukan yan ISMA da yabo agaresu. Malamin yace, har kullum ina kwana da yinin fatar in zamo dan ISMA tun anan duniya, ko kuma in samu ceton yan ISMA a gobe kiyama. Yace, muddin yan ISMA su ka yi abinda ya dace to lalle babu wata kafa da harkar kiran Malam (H) ke da ita ta saurin yada kyawawan sakonnin wannan harka kamar sashen kiwon lafiya, saboda misalai da dama da suka gabata na rahama da ma’ikatan kiwon lafiya su ka samu. Ya bada misali da Sayyid Tabataba’i marubucin shahararen tafsirin nan mai suna al-Mizan wanda a kullum ya ke alfahari da taimakon lafiyar wani kare a matsayin sanadin samun daukakarsa a fagen ilimi. Mallam Yakub yace to kare kenan, ina ga wanda aikinsa shine son ganin mutane sun sami lafiya? Yace babu aikin da yafi yiwa al’umma hidima saurin daga martabar mutum a wajen Allah Mahalicci da samun karbuwa da tasirantuwa a zukatan mutane. Ya ce, lallai yan ISMA jakadun kwarai ne na wannan harka, ya kuma yi kira ga sauran yan-uwa almajiran Mallam (H) da su lizimci daukar dawainiyar sashen kiwon lafiya na wannan harka da nufin su samu nasu rabon da kason a cikin ayyukan alherin da sashen ISMA ke gabatarwa.


Shugaban sashen ISMA na yankin Malam Abdulkarim Usamah ya kara karfafa yan-uwa na ISMA da cewa har kullum a zamo cikin shirin tunkarar ire-iren wadannan ayyuka kamar yanda Maulanmu Sharfuddeen (H) ke horon mu da aikatawa kuma a sadaukar da gabatar da kome domin Allah. Yayi godiya ta musamman ga yan-uwa da wasu bangarorin harka wadanda suka taimaka masu har Allah ya kawo karshen wannan yajin aiki. Yayi addu’ar Allah Ya kara kariya da taimako ga Malamin mu Shaykh Ibraheem Zakzaky (H) wanda da koyarwarsa da umurninsa sashen ISMA ya samu kafuwa ya na gabatar da ire-iren wadannan ayyuka.


Wakilin yan agaji na JNI da wakilin Red Cross Society da wakilin Hospital Friends duk sun gabatar da takaitaccen bayanan yanda zamansu ya kasance tare da yan-uwa almajiran Mallam (H) a asibitin, sun nuna gamsuwa da jin dadi da fatar Allah Ya dore wannan zumunci na su da ISMA.