Friday, August 13, 2010

YADDA AKA FARA GABATAR DA TAFSIR NA BANA A KATSINA, MALAM YAKUBU YAHAYA KATSINA KE GABATARWA DUK SHEKARA A BABBAN MASALACIN JUMA'A NA KATSINA

DAGA ABDULKWANARYA, KATSINA.
A yammacin ranar Lahadi 28/08/1431. Aka fara gabatar da tafsirin Al'Qur'an mai tsarki na watan Ramadan na wannan shekarar ta 1431, da Da'irar 'yan uwa Musulmi Almajiran Malam Ibraheem Zakzaky (H) ke gabatarwa a karkashin jagorancin Malam Yakubu Yahaya Katsina a harabar babban Masalacin Juma'a na cikin garin Katsina.


A gabatarwar da ya yi, Malam Yakubu ya bayyana muhimmacin wannan watan na Ramadan da cewa wata ne da aka saukar da Al'qur'ani a cikin sa, sannan hadisai da dama sun yi bayani akan mahimmacin karatun Al'qu'ani a cikin watan, ya kara da cewa daga cikin mahimmancin kuwa har da tafsirin sa “ana karatun al'qu'ani ne domin fahimtar sa” ya kara da cewa mutum ya dauki Al'qur'ani ya yi ta karantawa. Wasu sukan yi kokari su sauke shi cikin kwana uku, wasu kwana shida gwargwadon zuruf din mutun”

Malam Yakubu ya karanto hudubar Manzon Allah da ya yi akan wannan wata na Ramadan, inda ya bayyana falalolin da Allah ya aje a wannan watan na Azumi, daga cikin wadannan falalolin har da cewa “barcin mai Azumi Ibada ne, addu'o'insa abin karbawa ne. Sai  Manzo ya ce “ ku roki Allah ya baku damar azumtar wannan wata ya kuma baku damar karanta Littafin sa mai tsarki domin tababbe shine wanda aka haramta masa gafarar Allah a wannan wata.” Sannan Manzon Allah ya yi umarni da bayar da sadaka gami da ciyar da marasa galihu, ya kuma yi umarni da girmama manya da kuma tausaya ma yara. Sai Malam Yakubu ya nuna muhimmancin cewa ya kamata mutun ya dora ne da irin wadancan dabi'un ba kawai sai a lokacin watan Ramadan ba.

Sannan ya ce kamata ya yi mai Azumi ya kame daga kallace-kallace da sauran abubuwan da basu kamata a gani ba, domin mai Azumi ana bukatar kowace gaba tasa ta yi Azuminne ba kawai barin cin abinci ko na sha ba.

Daga cikin abubuwan da Manzo ya kwadaitar akwai kyautata dabi'u a wannan lokaci, ya karanto, cewa wanda duk dabi'unsa suka kyautata a wannan wata, ya sami shedar ketare siradi a ranar da diga-digai ke darjewa, sannan wanda ya tausaya ma wanda ke kasansa, Allah za ya saukake masa Hisabi. Sannan wanda ya yawaita yi ma Manzo da Iyalan gidansa Salati, Allah za ya nauyaya mizanin sa, wanda kuma ya karanta ayar Qur'ani kwara daya a wannan wata, daidai ya ke da wanda ya sauke Qur'ani a wani watan da ba Ramadan ba.

Wannan wata ne da ake bude kofofin Aljanna, ku roki Allah kada ya kulle ma kamu su, kuma wata ne da ake kulle kofofin wuta, ku roki Allah kada ya bude ma maku su.

A karshe Malam Yakubu ya tsoratar da cewa, “kadda ayi buda baki da haramun” sannan ya jawo hankalin jama'a da cewa kadda ya zama babu banbanci tsakain Azuminka da lokacin da ba azumi ka ke yi ba.

Shi dai wannan Tafsiri an saba gabatar da shi a irin wannan lokaci na Azumi tun tsawon shekaru ashirin da daya da suka gabata.

No comments:

Post a Comment