Friday, August 20, 2010

TUKIYYA TANA NAN A AL’QUR’ANI DA HADISAN MANZON ALLAH

Tare da Malam Yakubu Yahaya Katsina

DAGA: ABDUL AZIZI

An karyata tuhumar da ake yi ma mabiya Ahlul-Bayt (A.S) na cewar su munafukai ne ko suna fadar abin da ba haka yake ba a cikin zukatansu. saboda wai suna yin tukiyya ne. Malam yakubu Yahaya ya yi wannan karyatawa a lokacin da yake Karin bayani akan fassarar ayar nan da Allah madaukakin Sarki yake bayanin cewa” muminai kada su riki kafirai majibinta al’amurransu koma bayan Muminai, wanda duk ya aikata haka, shi ba bakin komai yake ba a wurin Allah, sai in kun ji tsoro da ‘yar kariya ( watau tukiyya) , Allah yana maku kashedin kansa, kuma makoma a wajen Allah take” ya kara da cewa, irin wannan Magana jahiltar al’Qur’ni ne domin wannan al’amari na Tukiyya karar yake a cikin littafin Allah.

Ya ce Ma’anar tukiyya shine Mutum ya kare kansa daga wani wanda zaya cutar da rayuwarsa ko dukiyarsa ko mutuncinsa, kuma ana yin ta ne domin kare addini” kana hanya ta addini , kana kira zuwa ga Allah, amma ga wani zai takura maka ko zai raba ka da rayuwarka ko dukiyarka ko ya cutar da kai sai dai kace Allah ya isa, ka samu ka yi Tukiyya anan , ka nuna kamar ka bari, amma a zuciyarka ba da gaske ba ne, kuma da ka sami dama kana ci gaba da abubuwanka” Ya yi bayanin cewa an samu wannan ne daga abinda ya faru ga babban Sahabin Annabi(S.A.W) Ammar bn Yasir a lokacin da Mushirikai suka rika azabtar da shi gami da mahaifansa Yasir da Sumayya abin da ya yi sanadiyyar shahadar mahaifan nasa, shi kuma Ammar ya kasa daurewa da irin wannan azaba har sai da ya yi maganganu marasa kyau ga Annabi sannan suka rabu da shi.

Da ya koma wurin manzon Allah tsirar Allah ta tabbabata gare shi da Iyalan gidansa yana kuka, da Manzo ya tambaye shi cewa, ya ya yake ji? Ammar ya tabbatar da cewa daram yake ji a zuciyarsa. Sai Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi da Iyalan gidansa ya ce,” Ammar yana cike da Imani tun daga kwakwalwar kansa har zuwa akaifar kafarsa, idan gobe suka kara yi maka irin wannan ka kara yi masu”. Wannan ya sa Allah (T) ya saukar da aya “ sai wanda aka tursasa shi, alhali zuciyarsa na cike da Imani”

Malam Yakubu ya kuma karanto Hadisai na Annabi a ruwayoyin Ahlulsunna da dama, da suka nuna ana yin Tukiyyah idan bukatar yin nata ta taso. sannan ya ce ya kamata a kara bincikawa domin a fahinci yadda al’amarin yake. Sannan ya ce, wannan batu na Tukiyya ya samo asali ne tun a farkon Musulunci, ba ‘yan Shi’a ba ne suka kirkiro, amma su suka fi yinta sabo da halin da suka sami kansu na takura da fafara da ake yi masu alokacin mulkin Umayyawa da Abbasiyawa, sai ya zamo sune suka fi bukatuwa zuwa ga yinta. Su kuwa Sunna basu shahara da yinta ba saboda basu da matsala da mahukunta, bilhasilima sune suke bayar da fatawa ga mahukuntan.” Wannan ya isa hujja ga mai neman gaskiya “

Malam Yakubu ya kara karanto wasu ruwayoyi da suka nuna yadda Sahabban Manzon Allah suka rika yin ta bayan rasuwar manzon Allah saboda abubuwan da suka biyo bayan rasuwar ta Annabin. Sai ya bayyana bukatar Musulmi su kara karantar Musuluncin domin kauce ma shiga cikin hadari.

No comments:

Post a Comment