Thursday, August 19, 2010

ISMA NA GUDANAR DA AIKIN TAIMAKO A BABBAR ASIBITIN GWAMNATIN JIHAR KATSINA

DAGA: ABDULKWANARYA
‘Yanuwa musulmi almajiran Malam Ibrahim Zakzaky(H) na sashen kiwon lafiya (ISMA) na Katsina, sun dauki aikin kulawa da majinyata a babbar Asibitin gwamnati da ke Katsina, sakamakon yajin aikin da ma’aikatan lafiyar jihar suka shiga a ‘yan kwanakin nan.
Malam Abdul Karim Usamatu wanda ke jagorantar wannan aiki ya bayyana haka ga manema labarai a Asibitin cewa, sun kawo wannan dauki ne, sakamakon wannan yajin aiki da ake yi a wannan jiha. Da yake bayyana irin aikin da suke yi a Asibitin, ya ce, suna duba marar sa lafiya ne idan suka gano abinda ke damunsa sai su bashi abinda suka tanada na magani, maganin da ba su da shi kuwa sai su sa aje a sayo, sannan suna bayar da maganin ne a kyauta. Ya tabbabatar da cewa, wannan aiki na al’umma ne” muna yi ne saboda ita al’ummar bata yi ba, amma shi wannan dauki na irin abinda muke yi , ya kamata ne ita al’ummar baki daya ta zo ta yi, domin wannan yajin aiki yana shafar mu ne duka” Sai ya yi kira ga sauran jama’a da su shigo a hada hannu a yi wannan aiki tare.”
Kodayake mun tarad da abokan aikinmu ‘yan Red Cross, ‘yan agaji na kungiyar Izala, Hizba, ‘Yan agaji na Jama’atu Nasril Islam da kungiyar dalibai da aka fi sani da (scout) suna ta kokari, saboda yanzu mun hada hannu ne tare da su muna gudanar da aikin” ya koka da rashin kayan aiki, amma duk da haka ya ce, suna gudanar da aikin.
Ya bayyana cewa bayan kulawa da marasa lafiya da suke yi, akwai kuma wani yunkuri da tuni suka fara na tsaftace Asibitin baki dayanta domin tsoron da suke da shi na barkewar cututuka saboda kazantar da yajin aikin ya haifar a Asibitin.
Ya yi bayanin yadda suka kasa aikin na su zuwa kashi uku , ta yadda wasu za su yi aikin safe wasu na rana wasu kuma na dare domin samun saukin gudanar da aikin .
Malam Abdul Karim Ya yi kira ga gwamnatin jihar ta Katsina da ta sasanta da ma’ikatan domin kulawa da lafiyar al’umma lallai gwamnati ce zata iya daukar nauyinsa. Ya jadda bukatar gwamnatin ta saurari wadannan ma’aikata tare da sasantawa da su domin mutane suna tagayyara sosai.
A karshe ya yi kira ga masu hali a fadin jihar da su kai dauki a wuraren da yajin aikin ya shafa domin samun sauki ga wadannan bayin Allah, tare da yin godiya ga Malam Zakzaky(H) wanda akan koyarwarsa ne har aka iya hada mutane masu masaniya a harkar lafiya daban –daban wuri daya suna gudanarda wannan agaji.
Wasu jama’a da da dama da da suka bayyana mana ra’ayinsu akan wannan yajin aiki, sun bayya muhimmancin sasantawa da ma’aikatan tare da bayyana takaicin ganin yadda gwamnati ta yi biris da al’amarin har aka shiga mako na biyu alhali majinyata suna cikin halin kaka ni kayi
Gabadayan Asibitin ta Katsina duk inda ka zagaya baka ji motsin jama’a sai dan abinda ba a rasa ba da suka yi saura, yayin da kasuwa ta bude ma Asibitin kudi ta gwamnatin tarayya da na masu zaman kansu saboda tururuwar da masu hali ke yi da majinyatansu, su kuwa marasa hali kodai sun koma gida ko sun hakura sun zauna a Asibitin jihar har zuwa wannan lokaci da Allah ya kawo wadannan masu bayar da agaji gare su.

No comments:

Post a Comment