Daga: Abdulkwanarya
An bayyana manufar samara da makarantun Fudiyyah da cewa, domin kawo gyara ne a cikin al’ummarrmu. Malam Yakubu Yahaya wakilin ‘yanuwa almajiran Sayyid Zakzaky(H) na Katsina ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen bukin yaye dalibai karo na takwas da makarantar Fudiyyah ta Katsina ta gabatar a dakin taro na Multi-Porpuse dake Filin Samji Katsina, a ranar 6/8/1431.
Malam Yakubu ya bayyana cewa, iyaye sun dauka tura yaro a makaranta ,yaro ya je ne mu huta da matala, bamu dauka muna gina wata al’ummaa ba ne. Sai ya yi kira da cewa,”babban abinda zaka ba yaro shine ilmi komai tsadar sa.
Da yake jawo hankalin iyayen su fahinci irin yanayin da wannan kasa take ciki na halin yanayin tabarbarewar al’umma, gami da lalacewar da kasar ta yi inda ta zamo sahun gaba a duniya wajen tabarbarewar al’amurra abinda da malamin ya bayyana da creewa ‘yan boko ne suka haifar da shi.Sai ya bukaci iyayen da su kara dagewa wajen daukar nauyin karatun yaran.”yaranmu sune jarin mu, sune za su kawo sauyin da ake nema”Sai ya yi fatan samun albarka ga wadannan yara.
A wani sashe na jawabin Malam Yakubu ya bayyana cewa, da yardar Allah a wannan shekara za a himmatu wajen samar da babbar kuma fadadaddar makaranta domin magance matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu. Ya kirayi ‘yanuwa gaba daya da su zamo cikin shiri domin tunkarar wannan aiki duk lokacin da aka bukata..
A tun da farko ,da yake gabatar da jawabi,Shugaban Makarntar MAlam Kabir Sani, ya bayyana irin nasarorin da makarantar take samu, wanda ya hada da samun nasarar cin jarabawar da makarantu a fadin jihar suke ta kokarin ganin dalibansu sun samu cinyewa, ya kara da cewa a duk lokacin wannan jarabawa ta Science Allah yana taimaka ma yaranmu su samun nasara inda yace "ko a bana ma yaranmu talatin da uku suika sami nasarar cin wannan jarabawa", ya kuma yi kira ga Da’irar Katsina ta himmatu wajen samar da makarantar sakandare wadda zata taimaka wajen kara tarbiyyantar da yaranmu akan lamarin wannan harka. ya nuna takaicin yadda yaranmu kan samu cikas da zaran sun fita daga fudiyyah sun koma wata makaranta.
An dai gabatar da kyaututtuka ga dalibnai masu barin makaranta da yahada da bayar da shedar kamala karatu “testimonial” gami da nada sabbin masu unguwanni da zasu kula wajen tafiyar da al’amurran dalibai.
No comments:
Post a Comment