Thursday, January 24, 2013

MUZAHARAR MAULUDIN ANNABI(S) A YANKIN KATSINA



A yau Alhamis 12/ 3/ 1434 ne da misalin karfe tara na safiya, 'yanuwa musulmi almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) na yankin Da'irar Katsina, suka gabatar da muzaharar tunawa da zagayowar rana da watan da aka haifi Manzon Allah(S) a cikin su.


 A jawabin da ya gabatar bayan kammala muzaharar, Malam Yakubu ya ankarar da al’ummar musulmi da ta lura da yunkurin da ake yi na rabata da Manzon Allah ta  hanyar shigo da makirce-makirce na zagi da aibata Manzon a kowane lokaci daga kafirci da kafiran duniya.
Malam Yakubu ya ci gaba da bayyana cewa, makiya sun dauka sun raba musulmi da Manzon Allah, amma sun ga abin ba haka bane, domin kuwa ga al’umma tana farkawa kuma ta  fito tana nuna soyayyar ga Manzon.
A cikin jawabin da ya gabatar bayan kammala muzaharar, Malam Yakubu ya yi kira ga al’umma gaba daya da su dunkule domin tunkarar wannan hali na kaskanci da ake ciki, malam yakubu ya kara da cewa dole ne musulmi ya bi tsarin da  Manzon Allah ya zo da shi, don kuwa muddin mutum bai bi na Annabi ba, to dole ya bi tsarin  bature wanda kuma shi bamaguje ne da ya yaki addinin Kiristanci ya zo da tsarin ‘yan kasa, sannan ya ce, duk abinda ake bukata na shugabanci ,Manzon Allah ya zo da shi, kuma akwai shi a wannan addin, sai  ya ce, tsarin yankasanci ba shi ne abinda ya kamaci musulmi ba. Don haka  ya zama wajibi musulmi duk da bambancin fahintar su, su dunkulu zuwa ga haduwa akan manufa ta addini tunda kowane musulmi yana so ne ya zame wajen Manzon Allah, Ya kara da cewa, haduwa ba yana nufin kazo ka yi abinda muke yi ba, a’a, yana nufin ka fahinci cewa, abin da mutum yake yi ,yana da hujja, kai ma abinda kake yi akwai hujjar da ka dogara da ita, amma a hadu domin cigabantar da wannan sako na Manzon Allah(S).
A wani gefen ,Malam Yakubu ya yi tsokaci akan halin da matasa suke ciki na yanayin shaye-shaye, inda ya ce ba wani ne yake da alhakin kan hakan ba, sai azzaluman mahukunta da sune suka hana yanayin da matasan zasu sami ilimi, ya kara da cewa, da wadannan matasa sun sami yanayin Karatu ,to da wasunsu Waliyyai ne sai kuma manyan masana ,amma saboda amfani da ‘yan siyasa ke yi da su ta saka su wani mummunan yanayi na shaye-shaye don su rika satar akwatunan zabe, shi ne dalilin zamantuwar su ‘yan kwaya da kuma kauranci. Sai Malam Yakubun ya yi kira ga matasan da cewa, su zo su hada sahu su koma mutanen kwarai domin suna iya watsi da wannan shaye-shaye, kuma musulunci zaya gyarasu su zama na kirki a cikin al’umma kamar yadda ya gyara na baya.
Da ya juya kan abubuwan da suke faruwa a halin yanzu a Mali, Malam Yakubu ya ce, makirci ne da aka kulla domin yakar addini tare da samun damar afka ma al’ummun kasashen da suke na  Musulmi,  ya kuma bayyana wannan abu da yake faruwa a Mali din da cewa, shiri ne na  da yunkurin kawo matsala a wannan kasa  da harggitsa yanayin yankunan da musulmi suke rayuwa da sunan yaki da boko haram,sai ya yi fatan Allah ya yi maganin wannan makirci sannan ya  farkar da zukatan musulmin su fahinci wannan makirci .
Jama’a da dama da suka kasha kwalkwatar idanunsu, da suka hada da ‘yanKabilar Igbo da sauran mutane, sun bayyana jin dadinsu da ganin yadda wannan muzahara ta gudana cikin lumana da kwanciyar hankali.
 Bangarorin da suka kayata wannan muzahara sun hada  da, Dalibai daga Makaranrun Fudiyyoyin yankin Makarantun Islamiyyu, bangaren Dalibai watau Acadamic Forum , mawakan gwagwarmaya da sauran al’umma maza da mata.
Sannan kamar yadda aka saba, muzaharar ta bi dukkan manyan tituna na cikin garin Katsina domin isar da sakon wannan muzahara mai taken , Labbaika ya Rasulallahi.

No comments:

Post a Comment