’Yanuwa musulmi almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky(H) na yankin da’irar Katsina da kewaye sun shiga sahun masu tattaki na nuna juyayin cikar kwana arba’in da shahadar Imamu Husaini(AS), tattakin da aka soma daga garin Malumfashi har zuwa Husainiyyar Bakiyyatullahi dake birnin Zariya.
Jagoran tattakin malam Sani Lawal , ya bayyana manufar wannan tattaki da cewa, amsa kiran Sayyid ibarahim Zakzaky(H) ne da ya yi akan amsa ma Imam Husaini(AS) da ya ce, “halmin nasirun yansuruna”.Sannan ya bukaci wadanda za su gabatar da wannan tattaki cewa, akwai bukatar zamantowarsu masu bin tsare-tsaren da aka gabatar domin samun nasara tare da kauce ma afkuwar hadari.
Bayan kammala wannan tattaki, almizan ta bukaci jin yadda wannan tattaki ya gudana, sai Malam Sani Lawal ya yabbayan godiya ga Allah, sannan ya ya kara da cewa, babu shakka wannan tafiya ta samu gagarumar nasar daga dukkan bangarorin da suka gudanar da ita.ya kara da cewa, abin da ya shafi kulawa da hanya, akwai bangaren harisaawa da suka kula da wannan aiki, ta yadda sukan lura da mitoci masu nisa tsakanin ‘yanuwa da ababen hawa ta yadda kafin mai mota ya tunkaro ‘yanuwan daga nesa , su masu kulawar sun ankarar da shi, haka abin yake a bayan masu tattakin, abin da ya taimaka wajen gudanar da wannan tattaki ba tare da samun wata matsalaba. Ya kara bayyana cewa,. Bangarorin masu kula da lafiya(ISMA) suma sun bada gudun muwa ta hanyar lura da wadanda suka sami matsaloli, tare da bada shawarwarin da zasu taaimaka ma mutum yin wannan tattaki cikin nasara. Ya ce masu kula da haskaka masaukai suma sun bada tasu gudun muwar ganin duk inda aka yada zango domin kwana , ‘yanuwa sun kasance cikin haske ne, ya ce, wanna ma ya taimaka wajen samun nasarar wanna tafiya.
Da ya juya kan al’ummun garuruwa da aka bi ta cikinsu , Malam Sani ya bayyana jin dadin yadda al’ummun wadanna wurare suka rika nuna jin dadi gami da bayar da abinci da abin sha musamman zangunan da aka sauka, ko domin Salla ko kuma domin kwana kafin a ci gaba da tafiya.
A karshe malam Sani, ya bayyana farin cikin ganin yadda ‘yanuwa suka bi tsare-tsaren da aka yi domin samun nasarar wannan tattaki, inda ya yi fatan Allah ya nuna mana masu zuwa anan gaba.
Almizan ta lura da yadda ‘yanuwa daga yankuna daban-daban da aka ratso ta garuruwansu suke jiran ayarin masu tattakin ya riske su domin suma su sa sahu, abinda ya kara yawan masu gabatar da wannan tattaki daga wannan yanki.
Kididdiga ta nuna cewa, wadanda suka gabatar da wannan tattaki daga wannan yanki, sun tasar ma ‘yanuwa dubu biyar da doriya tsakanin maza da mata dama kanan yara.
Shi dai wananan tattaki, shi ne irin sa na farko daga wannan yanki, kuma ‘yanuwa da dama da basu sami damar shigar saba a bana, sun kuduri cewa, da yardar Allah da su za a gabatar da na shekara mai zuwa.
No comments:
Post a Comment