A karo na uku, Mu’assasatus shuhada da bangaren ‘yanuwa na kwamitin ahl-duthour yankin da’irar Katsina, suka gabatar da taron tunawa da shahadar Alhaji Ibrahim hamdala Charanci dake jihar Katsina da yammacin ranar Assabat 14/6/1433.
A jawabin da ya gabatar, Malam Shehu Dalhatu Karkarku, ya bayyana Shahada da cewa falala ce da Allah (T) yake bayar da ita ga daidaikun bayinsa musamman a irin wannan lokaci da al’umma bata bisa tsarin Allah. Malam Shehu Dalhatu ya bayyana matakai da Shehu Usmanu Mujaddadi ya bayyana da suka wajaba musulmi su dauka a duk lokacin da suka sami kansu a wurin da ba a bin dokokin Allah, wadannan abubuwa kuwa sune, kauracewa daga wannan wuri da ya bijire ma tsarin Allah, ko kuma gwagwarmayar tabbatar da tsarin Allah din ko kuma mutum ya tafi daji ya sami wata itaciya ya ciza har sai ya mutu.
Ya yi tir da yadda ake ta yunkurin bata kiran komawa ga tsarin Allah da sukar kiran da sunan ana shi’a, wai kuma shi’ar ba addini ba ne. Yace, “amma kiran shi ne mafita ga al’umma daga wannan yanayi na zalunci da ake ciki” daga nan Malam Shehu ya gutsuro matsayin shahidi da bayyana kadan daga cikin matsayan da suka hada da , ceton mutane saba’in daga cikin danginsa, bayan rahama da yake cikinta tun kafin tashin kiyama. Ga makasan Alhaji Ibrahim kuwa, ya bayyana matsayinsu ne na dawwama cikin azabar wuta kamar yadda Allah(T) ya fada a cikin littafinsa mai tsarki.
A tun farko sai da aka gabatar da ziyarar Shahidin a makwancinsa, inda Malam Muhammad Awwal Iyal Zariya ya gabatar da takaitaccen jawabin da a cikinsa ya tunatar akan irin ta’addancin da aka yi ma Alhaji Ibrahim na kisan gilla ba domin komi ba sai dai saboda imaninsa. Ya kawo misalin halin da al’umma take ciki na zalunci da kashe-kashe da ake ta yi akan musulmi, inda ya bayyana mafita daga wannan yanayi sa cewa, ita ce, matsayar da Imamu Husaini(AS) ya dauka a lokacin da ya ga addinin Manzon Allah yana fuskantar rusawa, abinda ya kai ga shahadarsa .malam Awwal ya kara da cewa, gwagwarmaya a irin wannan lokaci ita ce kawai mafita, ya yi nuni da cewa, ko a kasashe irin su Iraki da Amerika ta kai mamaya tana kashe jama’ar kasar, g wagwarmaya suka yi har sai da Amurka din ta ga babu wurin zama sannan ta fara janye sojojinta daga kasar. Sai ya ce a wannan kasar ma gwagwarmaya karkashin jagorancin Sayyid Zakzaky(H) tare da tsayuwa akan tafarki ne kadai zaya kawo mafita ma wannan al’umma .
Idan za a iya tunawa, kimanin shekaru uku da suka gabata ne, wasu gungun ‘yan ta’adda suka kai ma shahid Alhaji Ibarahim Hamdala hari a gidansa bayan ya tashi daga shagonsa, inda suka sassare shi har suka shahadantar da shi.
‘Yanuwa daga garuruwa da dama ne suka sami halartar wannan tunawa da shahadar tasa.
No comments:
Post a Comment